38

928 69 2
                                    


*MEENAL WA LAMEEN*

*Written 2013*
*Posted 2019*

'''ZEE YABOUR'''
*Follow and vote me on wattpad @ZeeYabour*

'''IN DEDICATION TO'''
*Zakiya Musa Bala*
*Hafsat Salisu*

_*Haske Writers Association*_

*38*

    D'aya bayan d'aya kowa ke ficewa daga falon, Farda tazo fita, Al'ameen yasha gabanta, Idon sa cikin nata, Tayi saurin runtse ido saboda yanayin da ta tsinci kanta, "Meyasa kika ce ba zaki aure ni ba?", Tayi shiru, " Tambayarki nake kinyi shiru", "Dan Allah ka bani hanya na wuce idan ba so kake zuciyata ta tarwatse ba", " Bazan tilasta miki ki aure ni ba Farda, amma ki sani ina buk'atar ki a rayuwata", Zuciyarta ta karaya da kalaman sa, Jiki a sanyaye ta fice falon, Ya koma ya zauna cike da damuwa, K'wak'walwar sa cunkushe da tunani.

      Ya Mubarak da ya koma gida, Ya tarar da Aunty nussy da Khalil suna tattauna yadda auren sa da Meenal zai kasance, Khalil ya gaishe sa, Ya amsa a ransa yana tausayawa Khalil,

      Farda kuka take kamar ranta zai fita, Ummi ta shigo, Ta dafa ta tace "Hak'uri zaki yi Farda, nasan da ciwo, Amma Dan Allah kada ki fasa auren Al'ameen", Tana jin nauyin Ummi sosai ba zata iya cewa a'ah ba, Tace " Ummi kin wuce komai a wurina, Na amince da auren Al'ameen ", Ta rungumeta tace " Allah yayi miki albarka, Allah ya saka miki da gidan Aljanna" 

    Meenal kwana tayi sak'e sak'en yadda zata zubar da ciki, Khalil ya kira ta sun sha waya bata nuna mishi komai ba.

    Da safe Farda ta had'a mishi breakfast kamar yadda ta saba, Ta kai mishi d'aki, Yayi mamaki sosai, Ta juya zata fita, Ya kira sunan ta,  "Farda", " Na'am, Ta amsa, "Zaki aure ni?", Cikin jin kunya ta d'aga masa kai, Murmushi ne ya sub'uce masa yace " Thank you", Bata sake cewa komai ba, Ta fice zuciyarta fal da farin ciki, Al'ameen na sonta ya damu da ita.

    Meenal ke ta zuba soyayya da Khalil a waya, Ummi ta shigo d'akin, Ta fisge wayar ta kashe, Tace "Ki maida hankalin ki Meenal, kinsan ba zaki tab'a auren yaron nan ba, Goben nan za'a mayar masa da kayan sa, Yau Bappa zai sanar dashi komai", Hawaye ne suka fara zarya kan kumatun ta tace " Shikenan nayi bankwana da farin ciki", "Baki yi ba, In shaa Allahu zaki samu farin cikin da baki tab'a samu a rayuwar ki ba", Hawaye ta cigaba da yi, Ummi ta fice, ba zata iya jure ganin kukan yar'ta ba.

   Khalil jikinsa ke kyarma, Hawaye nabin kuncin sa, Da jin zancen Bappa, " Kayi hak'uri Ibrahim, wallahi da ina da wata ya' mace da na baka, na yaba da hankalin ka da natsuwar ka, Allah ubangiji ya maka zab'i nagari", Yana sharar k'walla yace "Ba komai Bappa nagode, zan wuce", " Toh ka gaida Mutanen gida", "Zasu ji"

      Kansa ya kifa kan sitiyari yana kuka kamar ran shi zai fita, Yana tsananin son Meenal amma ya zama dole ya hak'ura da ita, Kiran ta ya shigo wayarsa, Ganin sunan ta yayi rejecting, Ya tura mata text, Yana ganin yayi delivering, Ya goge number ta, Da duk wani abu da ya shafeta a wayar, ya cire sim ya karya, Hannun sa ya buga kan sitiyari, Yana cigaba da kuka.

    Jikina na rawa ta bud'e text d'in sa, "*Mu hak'ura da juna, ki manta dani a rayuwar ki, nima zan manta dake, Ina miki fatan alkhairi*", Jikinta ya hau rawa, Tayi dialing number sa a kashe, Ta kira yafi sau goma a kashe, Ta jefar da wayar, Ta saki kuka, " Ka cuceni Al'ameen, Ka ruguza mun farin ciki, Allah ya isa tsakanina da kai",

   Al'ameen na tare da Farda office, Suna aiki suna tab'a hira, Farda na taimakawa wajen rage masa damuwa.

    Meenal ta saka d'aya daga cikin masu aiki ta d'ebo mata darbejiya, Ta daka ta tace ruwan, Ruwan darbejiya ne rik'e a hannun ta, Tace " Yau zan zubar da cikin nan, na tsane sa na tsani mahaifin shi, bana burin na haifo sa duniya", Ta d'aga kai zata sha, Taji an bige kofin, An wanketa da mari, Ummi ce rai a b'ace tace "Idan kika kuskura kika zubar da cikin nan, Allah ya isa ban yafe miki ba", Kuka ta saki mai cin rai, " Har yaushe zaki yarda da k'addara kamar ba musulma ba, Na gaji da lamarin ki Meenal", Tana fad'ar haka ta fice daga d'akin, Meenal kuka ta cigaba tana jin dama ta mutu ta huta, A wurin ta gara mutuwar ta, da wannan rayuwar.

MEENAL WA LAMEENUnde poveștirile trăiesc. Descoperă acum