*MEENAL WA LAMEEN*
*Written 2013*
*Posted 2019*'''ZEE YABOUR'''
*Follow and vote me on wattpad @ZeeYabour*'''IN DEDICATION TO'''
*Zakiya Musa Bala*
*Hafsat Salisu*_*Haske Writers Association*_
*46**Not Edited*
_A kullum masoyan littafin nan k'aruwa kuke, Ina godiya da soyayyarku_
Wunin ranar Meenal hira suke da Ummi, sam bata kawo zancen Al'ameen ba, tana jin kamar kar su rabu, dan sosai ta d'ebe mata kewa, tare da rage damuwa, "Ummi mai awarar unguwar nan tana nan kuwa", " Tana nan ", " Bari na aika a siyo mun", Ta kira mai aikin su ta bata,
Awarar take ci, suna hira, Al'ameen yayi sallama ya shigo, K'amshin turaren sa ne ya game falon, A zuciyarta tace "Ba dai son turare ba, kullum da kalar k'amshin da zaka ji yana yi",
Ummi tace " Al'ameen ka dawo", "Eh Ummi", " Ai sai ta tashi ko tafi", Ta shagwab'e fuska tace "Kai Ummi korata kike", " A'ah ba korar ki nake ba, naga dare yayi ne", "K'yaleta Ummi, ina ga so take ta kwana nan",
Ta tsuke fuska, tana hararar sa, Bai lura ba haka Ummi ma, " Sai da safe", Yacewa Ummi, "Toh Allah ya bamu alkhairi", " Amin", Ya juya kan Meenal "Ki sameni waje and Don't waste my time", Yayi maganar a hankali yadda ita kad'ai taji, Baki ta murgud'a mishi, Ya fice a zuciyar sa yana cewa " Yarinyar nan ta raina ni"
Mik'ewa tayi tace "Bari nayi fitsari Ummi", " Amma Meenal da abu kike, baki san da fitsari ba sai yanzu",
Toilet ta shiga ta kunna famfo, tana watsa ruwa a fuskar ta, Ba fitsari zata yi ba, kawai dan ta b'ata masa lokaci,
Al'ameen ya cika yayi fam, yasan ba Ummi ce ta tsayar da ita ba, Gudun kar Ummi taga gajen hak'urin sa yasa bai tafiyar sa ba, Ta cikin mota ya hango ta tana tafiya kamar bata son taka k'asa, Ji yake kamar ya fita ya shak'o ta, Ta bud'e murfin gaban mota ta shiga, Bai ce da ita komai ba, Ya figi mota a 360 (Hmm ran maza ya b'aci),
Meenal sai da hantar cikinta ta kad'a saboda tsoron gudun da yake, Sai da yayi nisa da gida yayi parking mota gefen titi, Ya juyo yana kallonta cike b'acin rai yace "Me yasa kika raina ni da yawa, Dan ina nuna damuwata a kanki?", Da mamaki take kallon sa, a ranta ta nanata " Damuwa, har damuwa yayi dani", Bakinta taji ya kama, ya murd'e da k'arfi, Yace "Duk ranar da kika k'ara murgad'a mun baki, sai na zubar miki da hak'ora", K'ara ta saki saboda azaba, Ya saki bakin, Tasa hannu biyu ta kama, Hawayen azaba ya shiga zarya kan kumatun ta,
Ganin hawayen kan fuskar ta yaji zuciyarsa ta raunana, Juyawa yayi, Yaja motar suka nufi gida, Fita tayi daga motar tana cigaba da hawaye, Yabi bayanta, " Meenal" Ya kira sunan ta, Cak ta tsaya, Handkerchief ya zaro daga aljihu, ya mik'a mata yace "Ki share hawayen ki", Tsintar kanta tayi da karb'a, Ya rab'a ta gefen ta ya wuce,
D'akin sa ya nufa, ya fad'a akan gado tare da furta " Ya Allah",
Bata share hawayen ta ba, Sai da ta kai d'aki, Tasa hanky tana share hawaye, K'amshin sa duk ya dabaibaye mata hanci, Tsintar kanta tayi da lumshe ido, Toilet ta shiga tayi alwala, ta gabatar da sallar isha'i, bata yi ba, Ta shagala suna hira da Ummi.
Damuwar da ta lullub'e zuciya da ruhin jikinsa, ke son haddasa mishi ciwon kai, Mik'ewa yayi ya nufi sashen Farda, Ganin Haidar zai rage masa damuwa,
Farda bacci ya fara d'aukar ta, Jin motsin Al'ameen ta bud'e ido, "Am sorry na tashe ki bacci", " Ba komai, dama baccin bai yi nisa ba",
Haidar dake bacci, Ya sumbata a goshi, Yace "Allah ya raya ka yayi maka albarka", Ya tofa masa addu'o'i, Ya juya kan Farda, Yace " Sai da safe", "Allah ya bamu alkhairi", " Amin"
YOU ARE READING
MEENAL WA LAMEEN
Romance"A da ina son ka ina k'aunarka ina ganin girman ka , k'imar ka mutuncin ka darajar ka, A yanzu na tsane ka tsana mafi muni, ba wanda na tsani gani kamar ka, ka aikata abunda ko kafiri yayi sai al'umma tayi Allah wadarai dashi, Wallahi Wallahi Wallah...