*MEENAL WA LAMEEN*
*Written 2013*
*Posted 2019*'''ZEE YABOUR'''
*Follow and vote me on wattpad @ZeeYabour*
'''IN DEDICATION TO'''
*Zakiya Musa Bala*
*Hafsat Salisu*_*Haske Writers Association*_
*28*
Al'ameen mamaki yake "So Farda is his second cousin, jinin shi ce, no wonder yaji ta a ran sa, Su Ya Mubarak gidajen su suka wuce, Ya fad'awa Ummi tsakanin sa da Farda, Da zata rik'a aiki a CONSILIO d'in shi, Ummi taji dad'i sosai, Tace " Ta dawo gidan su da zama", Hakan ya ma Farda dad'i, zata zauna kusa da Al'ameen kuma cikin yan'uwanta, Ummi ta kira mahaifin ta ta sanar dashi, yaji dad'i hankalin sa ya kwanta, dama bai so zuwan ta aiki 9ja ba, Sai da akai ruwa tsaki ya barta ta taho, tare da gargad'in ta ta rik'e mutuncin ta.
D'aki d'aya aka ware mata anan zata rik'a zama, Meenal kam tana ta murna ta samu Sister a kusa da ita, Tunda ta tashi gidan su, babu macen da ta tab'a zuwa ta zauna, Sai fah matan Yayyen ta suzo yini, ba kwana ba.
Khalil ya shirya zuwa gaida Al'ameen da taya shi murna, A harabar gidan ya tsaya, ya kira Meenal yace gashi yazo, Fuskarta ta k'ara gyarawa, ta d'auki veil ta yafa, Ta fesa cool turare ba mai k'arfi ba, idan ba kazo daf da ita ba, bara kaji k'amshin shi ba, Ummi ce ta hanata fesa turare mai k'arfi idan zata fita ko zata wajen Khalil( Koyarwa Manzo SAW duk matan da saka turare ta fita namijin yaji k'amshin shi laifin ta kamar tayi zina ne MATA A KIYAYE)
"My beb kullum k'ara kyau kike", " Kai Ya Khalil", Ta fad'a tana rufe fuska cikin jin kunya, "Allah babyna", Ya fad'a tare da kafe ta da ido yana jin sonta na ratsa shi, Kan kujeru dake harabar gidan daga gefe, Suka zauna, Ta mik'e ta shiga kawo mishi abun motsa baki, Yabi bayanta da Kallo, Yana sauke ajiyar zuciya tare da addu'ar Allah ya nuna mishi ranar da zata zama mallakin shi,
Yana cikin tunanin, ta dawo rik'e da tray ta ajiye gaban sa, Ta zauna, " Ina Yayan mu, ni fah shi nazo gaisarwa ba wurin ki", Ya fad'a cikin sigar tsokana, Ta b'ata rai tace "Toh Bacci yake, sai ka koma", Yasa dariya yace " My baby Sarkin fushi, wasa nake ni wurin ki nazo", Tayi d'an murmushi, Ta d'auki cup tana zuba mishi lemo.
Al'ameen bacci yake na huce gajiya, k'arar wayar sa ta tashe shi, Sam ya manta ya saka silent, Wani tsaki yaja ya jawo wayar yayi receiving tare da kangawa a kunne, "Hello Babyna", "Ku mata meyasa baku da aji ne, ke kuma dak'ik'iyar ina ce", Yana fad'ar haka bai jira amsar ta ba ya kashe tare da jan dogon tsaki, Kullum matan da ke kiran sa sun fi a k'irga, " Ina jin na kusa canza sim, mata basu da aji" Ya fad'a cike da takaici, (Ni zee nace ba duka ba)
Toilet ya shiga, yayi brush, Ya watsa ruwa, Ya saka kayan shan iska, Gashin kansa ya d'an taje ya kwanta luf a kansa, Waje ya fito dan shan iska,
Gabansa ne yayi wani mummunar fad'uwa, Numfashin sa ya d'auke Na wasu sakanni, Ganin K'anwar sa da wani suna hira cikin salon soyayya, Jikinsa har rawa yake, ya k'arasa wurin su, Lafiyayyan mari ya wanketa dashi, "Yaushe kika lalace Meenal, har kinyi girman da zaki tsaya da saurayi, maganata ta zama ta banza", Dafe kuncin ta tayi, hawaye na bin fuskarta, tamkar a mafarki haka take gani yau Yayanta ya mare ta, tun tana k'arama ko nuna ta da yatsa bai tab'a ba, Runtse ido yayi yana jin zafi da rad'ad'i a zuciyar sa, Khalil kam kasa cewa komai yayi, Ya tsaya kallon ikon Allah, " Tashi ka bar gidan nan, kafin nayi k'asa k'asa da kai", Ya fad'a cikin tsawa ba tare da ya bud'e idon sa ba, Khalil ya mik'e ba dan yaji tsoron Al'ameen ba, sai dan a zauna lafiya, Yasan bai san waye ba, bai san an san shi a gidan ba, shiyasa yayi re-acting this way,
Meenal a guje ta shiga gida tana kuka, Ta fad'a jikin Ummi, "Lafiya?, ki gaya mun me ya faru?", Kukan ta cigaba ta kasa magana, Al'ameen ya shigo yana huci, " Ummi yanzu ya dace ku bar Meenal ta fara soyayya?", "Idan bamu barta ta fara soyayya yanzu ba, yaushe zamu barta, Shekarar ta 18 fah, ba tasa ta gaba zamu yi muna kallo ba", Zuciyar shi yaji ta k'ara harzuk'a bai ce komai ba ya fice d'akin,
Ummi tabi bayan shi da kallo tana fad'in " Yau ni naga ikon Allah ", Ta dawo kan Meenal " Ke kuma kama mun bakin ki", Mik'ewa tayi ta fice d'akin tana kuka da shesshek'a, Kacib'us tayi da shi a bakin k'ofa, Rungumeta yayi jikin shi, a tare suka ji wata natsuwa ta saukar musu, "Zan iya jure komai a rayuwata ban da kukan ki, ki taimaka mun ki daina", Lamo tayi a jikin shi, Ita ba marin ya dameta ba fushin da yayi da ita, Ran shi ya b'aci, " Yayana kayi hak'uri Dan Allah", "Zan hak'ura amma sai kin daina kuka", Tayi saurin share hawaye, Ya raba jikin shi da nata, Yace " Gaya mun yaushe kika fara soyayya? ", Bata b'oye komai ba, ta zayyana mishi, Al'ameen hakanan yaji ran shi na mishi ba dad'i, Ya daure yace " Ki kula da kanki K'anwata, Allah ya tabbatar mana da alkhairi", "Ameen Yayana", Ta fad'a tana kwantar da kanta kan kafad'ar shi.
Ko da ta shiga d'aki ta duba wayarta, Missed calls na Khalil ta gani, Number shi tayi dialing, Ringing d'aya ya d'auka, " Hope lafiya My beb, hankalina ya kasa kwanciya", "Lafiya lau, komai normal ya fahimta", " Alhamdulillah, Yayanki akwai zafi", Dariya tayi sam bata son laifin Yayanta, nan suka shiga hirar soyayya.
Farda na ganin yadda Meenal ke yawan waya da Khalil akai akai suna shan soyayya, but ita da Al'ameen sam ba haka ba, bai damu ya kira ta ba, Ko kiran sa tayi basa wata doguwar hira bare kalaman soyayya, Sau da yawan ta kan ce da kanta "Anya yana sonta", Wata zuciya tace " Yana sonki, tsabar miskilanci ne", Sai taji hankalin ta ya d'an kwanta,
Wani film yake kallo tare da Meenal, Na soyayya ne, Yadda wasu masoya ke wahala akan son juna, Tsaki yaja yace "Shirmen banza, banda film yaushe mutum zai kamo da son wani har haka, hadda su ciwo", Meenal dake kusa dashi tace " A gaske ma yana faruwa Yayana, so masifa ne, musamman idan ya maka mugun kamu", "Ke har so kika sani", Tayi dariya dan gani take tasan so akan Khalil, " Wannan duk shirme, canza mana channel abeg", Bata ce komai ba, ta canza, tana mamakin Yayan nata, kenan ba wani so yake ma Ya Farda ba, har taji ta bata tausayi, yadda ta fuskanci tana tsananin son Ya Lameen.
Zaune yake a tantsamemen office d'inshi, tsayawa bayyana muku kyau da tsaruwar shi k'auyanci ne, kowacce ta ayyana a ranta, Designs yake dubawa a system, Door bell ce tayi k'ara, wata k'aramar computer ta nuna mishi mutumin dake tsaye waje bakin k'ofa, PA d'in shi ne, Wani d'an remote ya danna k'ofar ta bud'e, Ya shigo, Cikin rissinawa yace "Sir kayi bak'i", " Su waye?", "Daga Federal Government", " Kace su shigo", Ya fad'a ba tare da ya d'ago kansa daga kallon system ba, "OK Sir"
Dattawa ne su biyu cikin shigar kamala suka shigo, Al'ameen ya tarbe su cikin girmamawa, Bayan sun gaisa, Suka mishi bayanin contract da suka kawo mishi, wanda idan yayi yadda ya kamata zai mak'udan kud'i, Ya karb'a ba tare da fargabar samun wata matsala ba, Suma basa shakku akan aikin sa, sun san ya k'ware.
Anyi bikin Habeeb ba ayi shagalin biki ba, D'aurin aure kawai akayi da Yinin biki, Aka kai Amarya gidan ta, Habeeb har yanzu ya kasa cire Meenal a ransa, Amarya sam baya wani marmarin ta, sun gama tambad'ewa a waje, (Yan mata kuyi k'ok'arin rik'e mutuncin ku, da kai budurcin gidan miji, Wallahi Miji ba zai tab'a ganin ki da daraja ba, Musamman wanda kuka tambad'e a waje tare)
Yau asabar duka ilahirin gidan sun taro a gida, Duk asabar suna had'uwa duka, Ya Mubarak yaran sa biyu (Jawhara da Jawwad), Ya Hafeez ma nada biyu ( Sultan da Ajab), Mujeeb nada d'aya(Safeena), Mahad ma d'aya(Haidar) matar sa nada tsohon ciki, Haihuwa yau ko gobe,
Hira suke cike da nishad'i, Jikokin na wasa a harabar gidan, Motar Al'ameen ce ta shigo, Bodyguard yayi sauri ya fito ya bud'e mishi k'ofa, Cike da k'asaita ya fito, Murmushi yayi ganin yadda gidan ya cika da yara, "Yanzu nan duk jikokin Bappa ne, Allah ya raya", Ya furta a fili, Chocolate ya rabawa yara, suna da tsalle da murna,
Sallama yayi falon, Duka suka juya suka kalle shi tare da amsawa a tare, Sam baya son hayaniya, gashi ya taru gajiya, D'akin sa ya wuce, Rigar sama ya cire, Ya fad'a kan gado, Yana sauke ajiyar zuciya tare da fad'in " Ya Allah"
A can ya bar Farda bata gama aikin ta ba, Duk da wuri d'aya suke aiki, Kowa tafiyar sa daban, dawowar sa daban,
Meenal tayi sallama rik'e da tray na abinci a hannu, Ta ajiye gabansa, "Yayana sannu", " Yawwa Lil sis", Ya fad'a yana d'agowa, "Ga abincin ka na kawo maka, nasan ba zaka iya ci a falo ba", Yayi smiling yace " Thank you My one and only sis", Saukowa yayi k'asa, Tayi serving d'in shi Yace "D'auki Spoon muci tare", Ba musu ta d'auki spoon, suka fara ci.
Tunda ya dawo, Meenal ke dafa masa abinci, Baya cin abincin kowa sai nata.
*Follow*
*Vote*
*Like**ZEELISH*💕
YOU ARE READING
MEENAL WA LAMEEN
Romance"A da ina son ka ina k'aunarka ina ganin girman ka , k'imar ka mutuncin ka darajar ka, A yanzu na tsane ka tsana mafi muni, ba wanda na tsani gani kamar ka, ka aikata abunda ko kafiri yayi sai al'umma tayi Allah wadarai dashi, Wallahi Wallahi Wallah...