*MEENAL WA LAMEEN*
*Written 2013*
*Posted 2019*'''ZEE YABOUR'''
*Follow and vote me on wattpad @ZeeYabour*'''IN DEDICATION TO'''
*Zakiya Musa Bala*
*Hafsat Salisu*_*Haske Writers Association*_
*35*
*Wannan page naku ne Ummu Meenal, Fufah, Fiddausi, Hussyluv, Oum sadeeq, Fari'a zaki, Rabi'at Adam , Zahra(Aishat A Muhd novels GRP)*
Ya Mubarak yace "Mami zamu tafi, sai da safe", " Toh Mubarak Allah ya bamu alkhairi", "Ameen",
Asibitin ya rage daga Ummi sai Mami, Mami na tare da Al'ameen, Ya farfad'o, Yana jin ina ma bai tashi ba, Ina ma ya mutu, Mami tace " Al'ameen ka tashi?", Kai ya d'aga mata , "Sannu koh, bari a had'a ma shayi nasan kana jin yunwa", " A'ah Mami, bana buk'atar komai", Ya fad'a yana jin wani abu ya tokare masa wuya, "Ya zaka ce haka, tunda kazo asibitin nan baka ci komai ba", " Nasha kunu d'azu da kina wurin su Ummi", "Toh Shikenan",
Mik'ewa yayi da k'yar ya shiga band'aki yayi alwala, Ya fito ya kabbara Sallah, Nafiloli yake yana rok'on Allah gafara, sassauci da samun sauk'i a rayuwar sa.
Sautin kukan Meenal ya tashi Ummi daga baccin da ta fara, " Meenal kin farka", "Ummi kinga abunda Ya Lameen yamun, Dan Allah kice mun mafarki ne", Kasa magana Ummi tayi sai kuka,
" Da gaske ne ko, ya lalata mun rayuwa, ya cire ni daga sahun yan'mata, shikenan ba zan yi aure ba, babu namijin da zai ganni da daraja, meyasa zaka mun haka", Ta dafe zuciyar ta da take ji kamar ana hura mata wuta a ciki, "Ki daina kuka, addu'a zaki yi kinji", Kamar Ummi tace ta k'ara kuka, Ta cigaba da kuka, Tana jan numfashi kamar zata shid'e, Ummi a rud'e ta rungumeta tana tofa mata addu'a, Ta fara sauke numfashi a hankali, hawaye na bin fuskar ta,
Al'ameen ya idar da Sallah, Ya samu natsuwa ba kamar da ba, yaji yana buk'atar ganin lafiyar Meenal, Tuni Mami tayi bacci,
Idon sa suka sauka kan Meenal da ta fita hayyacin ta, Tausayinta ya shige sa, yana k'ara jin haushin kansa, Cikin sanyin murya yace " K'anwata", Kamar an soke ta da dalmar wuta haka taji sunan, D'agowa tayi daga jikin Ummi ba tare da kalle sa ba Tace "Ka kirani da sunan da nafi tsana, Ashe kai mugu ne azzalumi, mara imani, bana fatan sake ganin ka a rayuwata AMINU", Ta fad'a cikin d'aga murya, Ya kid'ima da jin zancen ta, kansa ya wani sara, kamar zai fad'i yayi saurin ankara,
Durk'usa yayi yace " Nasan ni mai lai......", "Bana son jin muryar ka, please stay away from me", Ta fad'a cikin kuka tana toshe kunne, Har cikin ransa yake jin kukan ta, Hankalin sa na k'ara tashi, Babu yadda ya iya haka dole ya tashi, Ya koma d'akin sa, Duniyar ta masa zafi, Ya rasa ina zai sa kansa yaji dad'i.
Bayan tafiyar sa ta buk'aci yin Sallah, Ummi ta kama ta kai ta toilet, Tayi sallolin da ake bin ta, tare da nafila tana rok'on Allah sassauci,
Tana zaune kan sallaya, kanta na mugun ciwo kamar zai fashe, Ummi tace " Ga shayi na had'a miki kisha", Kanta ta girgiza, "A'ah ki daure kisha, dan kisha maganin ki", " Ummi ki daina wahalar da kanki a kaina, mutuwa kawai nake buk'ata, ita tafi mun huta", "Haba Meenal, ke fah Musulma ce, ya kamata ki yadda da k'addara mai kyau ko mara kyau", Murmushin takaici tayi, ita kad'ai tasan zafi da rad'ad'in da take ji,
Cikin lallashi Ummi ta zauna tana bata shayi, d'acin sa take ji a bakin ta, Sha take dan bata da yadda zata yi, Rabin Kofi tasha, Tace " Ummi na k'oshi", "Ai baki sha wani abu ba", " Amai zanyi idan na k'ara", "Toh shikenan, ga maganin ki", Ta b'allo ta bata tasha, Akwai nasa bacci a ciki, Few minutes bacci ya d'auke ta,
Washegari da safe, Bappa na zuwa aka sallame su, Meenal ta kafe ba zata shiga mota d'aya da Lameen ba, Bappa ya kira driver yazo ya d'auke sa ,
YOU ARE READING
MEENAL WA LAMEEN
Romance"A da ina son ka ina k'aunarka ina ganin girman ka , k'imar ka mutuncin ka darajar ka, A yanzu na tsane ka tsana mafi muni, ba wanda na tsani gani kamar ka, ka aikata abunda ko kafiri yayi sai al'umma tayi Allah wadarai dashi, Wallahi Wallahi Wallah...