*MEENAL WA LAMEEN*
*Written 2013*
*Posted 2019*'''ZEE YABOUR'''
*Follow and vote me on wattpad @ZeeYabour*'''IN DEDICATION TO'''
*Zakiya Musa Bala*
*Hafsat Salisu*_*Haske Writers Association*_
*42*
_Khadija Sanda, Hauwa M Bello, Shoter wannan shafin naku ne Allah ya bar k'auna_💕
Farda ta shimfid'e yaron gefen ta, Ta tofe shi da addu'o'i, Taja bargo ta lullub'e su, Sam bashi da rigima sau d'aya ya farka, ta bashi madara, Yasha ya koma baccin sa.
Meenal ranar bata runtsa ba, Kuka take wanda ta rasa dalili yin sa, Sam bata jin natsuwa a ranta, Kwana tayi tunani da sak'e sak'e.
Kiran sallar asuba ya tashi Al'ameen, Ya mik'e da sunan Allah, Toilet ya shiga yayi alwala da brush, D'akin Farda ya nufa, Shigar sa yayi daidai da kukan yaron, Da sauri ya k'arasa bakin gado, Ya d'auke sa ya shiga jijjiga shi, Farda ta farka jin kukan yaron, Madarar sa ta shiga had'awa, ta mik'a mishi, Ya karb'a yana bashi, Yana gama sha bacci ya d'auke shi, Ya kalle shi yace "Bawan Allah",
Ya mik'a mata shi yace " Zan je masallaci", "A dawo lafiya", Shimfid'e sa tayi ta shiga toilet yin alwala.
K'arfe 7 na safe, Baaba ta shiga tashin Meenal wanka, idonta biyu, Tace " Baaba ina kwana?", "Lafiya lau, ya k'arfin jiki?", " Alhamdulillah", Baaba ta nisa tace "Aminatu me zai hana ki karb'i yaron ki, yana buk'atar ki, jariri ne shi da bai san komai ba", Murmushin takaici tayi tace " Muje Baaba ayi wankan",
Bayan ta shirya, aka kawo mata kunu mai zafi tasha, Ji tayi tana buk'atar wani da za tayi magana dashi, Aunty Nussy ta kira tace Dan Allah tazo tana son ganin ta.
Cikin awa 2 Aunty Nussy tazo, "Meenal yaushe kika sauka?", " Jiya da daddare", "Mashaa Allahu, Ina babyn?", Ta d'an yi shiru sannan ta fad'a ma Aunty komai, " Lallai Meenal kinyi babbar wauta, ina hankalin ki da tunanin ki yake, meyasa zaki yi wannan d'anyen aikin?", "Ta hanyar nan kad'ai zan cusawa Al'ameen kwatankwacin bak'in ciki da ya sani",
" Akwai hanyoyi da yawa da zaki cusa masa bak'in ciki amma bata hanyar jariri bawan Allah da bai san komai ba", "Aunty na fuskanci yana tsananin son babyn tun kafin yazo duniya, wannan itace hanya mafi girma da zan cusa masa bak'in ciki", " Shikenan Allah ya kyauta, amma sam bana goyon bayan haka"
Ta kawar da maganar ta hanyar cewa "Ina Ya Khalil?", " Yana nan, Mama na son had'a shi aure da yar' k'awar ta yana hanya hanya", Gabanta yayi mummunan fad'uwa, Ta had'iye yawu masu kama da ruwan zafi, tace "Allah ya zab'a mafi alkhairi", " Amin"
Ta nisa cikin tunanin zuciyarta na ce mata ya zama dole kiyi k'ok'ari Khalil ya zama naki, kada kiyi sakaci.
"Tunanin me kike?, ina ta magana kinyi shiru", Tayi saurin zabura tace " Ba komai", "Ki rage tunani dai kar ki janyo wa kanki wata Matsala", Tayi murmushi tace " Toh"
Ummi ta aika musu da tsohuwa da zata rik'a ma Babyn wanka da gasa cibiya, Al'ameen kaya ya siyowa yaron masu yawa kuma tsadaddu, An shirya shi cikin kayan yara, yana ta k'amshin turaren babies, Al'ameen na rungume dashi, Farda na zaune gefe,
Ya Mubarak, Ya Hafeez da Ya Mahad suka yi sallama suka shigo, Farda da sauri ta mik'e ta shiga d'aki ta sako mayafi, Cikin girmamawa ta gaishe su suka amsa, Hafeez ya fara karb'ar yaron, Yace "Soo Mashaa Allah", Ya Mubarak yace " Su Al'ameen an zama baba", Dariya yayi yace "Ya Mubarak baka rabuwa da tsokana", Suna ta yaba kyawun yaron, Farda ta kawo musu lemo da abun motsa baki, Sun d'an jima suna hira, Kowanne ya ajiye 50k, Al'ameen ya musu rakiya har mota yana godiya,
YOU ARE READING
MEENAL WA LAMEEN
Romance"A da ina son ka ina k'aunarka ina ganin girman ka , k'imar ka mutuncin ka darajar ka, A yanzu na tsane ka tsana mafi muni, ba wanda na tsani gani kamar ka, ka aikata abunda ko kafiri yayi sai al'umma tayi Allah wadarai dashi, Wallahi Wallahi Wallah...