*MEENAL WA LAMEEN**Written 2013*
*Posted 2019*'''ZEE YABOUR'''
*Follow and vote me on wattpad @ZeeYabour*'''IN DEDICATION TO'''
*Zakiya Musa Bala*
*Hafsat Salisu**_Haske Writers Association_*
*53*
*Unedited*
*_Bansan da wane baki zan baku hak'uri na jina shiru ba, nasan da yawa kun fara manta yadda yake, ko karanta last page sai ku cigaba_*
Wayar ta ta d'auka, tayi dialing number Layla, bugu d'aya ta d'auka, "Meenal ina kika ajiye wayar ina ta kira bakya d'auka", " Afwan bana kusa ne", "OK kizo ki sameni gidan mu yanzu", " OK gani nan zuwa", Tayi hanging up tare da furta "K'arshen ku ya kusa zuwa",
Shiri tayi cikin sauri, Ta fito ta sanar da Farda, tace ta iya takun ta,
Da kanta tayi driving zuwa gidan, Layla na ganin ta, ta washe baki, Cike da far'a ta tarbe ta, tare da dabaibayeta da abun motsa baki, " Da baki wahalar da kan ki ba, a k'oshe nake", "Ba zaki zo wurina ba, ko ruwa ki kasa sha"
Ta tsiyaya ruwa a kofi tasha, "Yawwa ko kefa", Tayi murmushi, Wasu takardu ta jawo ta mik'a mata tace " Wannan nake so kiyi k'ok'ari ya saka hannu, da yasa tashi ta k'are", Da murmushi ta karb'a tace "Kar ki damu an gama", " Baki ci snacks d'in ba", "A'ah wlh a k'oshe nake, wucewa ma zanyi na bar aiki gida", Ta fad'a tana mik'ewa, " OK muje na raka ki", "Da kinyi zaman ki", " A'ah"
Ta mata rakiya har mota, ta dawo gida cike da murna, burin su ya kusa cika.
Shigowar motar ta yayi daidai da fitowar Al'ameen, Gabanta ya fad'i kada yayi wani zargin, Ta k'arasa tayi parking, Ta fito ba tare da ta kalli saitin da yake ba, a jikinta tana jin yana kallon ta, "Daga ina kike?", Ta jiyo muryar sa, Banza tayi kamar bata ji sa ba, tana cigaba da tafiya, Gabanta yayi saurin sha, " Baki ji ina magana bane",
Kanta ta sunkuyar k'asa tace "Please ka bani hanya na wuce", " Ki bani amsar tambayar da na miki", "Sak'o naje karb'uwa", " Idan ma wani shirin kuke k'ullawa ki sani ba zaku tab'a cin nasara ba"Murmushi tayi, tare da girgiza kai tayi gaba, D'akinta ta nufa, tasa key ta rufe tasan zai iya shigowa, ta fiddo takardun daga handbag d'inta, ta kalla, "Greediness nasu Layla yayi yawa, tayi kuskuren yarda dani, soon zan tarwatsa duk wani shiri naku, kuma ku tsinci kanku a gidan yari, Wata akwati ta jawo ta saka takardun can k'asa, ta saka mata lock.
Farda bata bar office ba sai da kowa ya watse, Ta shiga office na Layla ta ciro camera, ta saka a jaka, Ta mayar da office d'in ta rufe.
Zaune take a falo tana kallo, but hankalinta sam baya kan kallon ya tafi tunani, Knocking da taji ana yi, yasa ta tashi ta bud'e k'ofa, " Afra Yau kece?", "Nice fah", Ta fad'a tana shigowa ciki,
Bayan sun gaisa ta kawo mata abun motsa baki, Tace " Invitation na biki na kawo miki", Ta ajiye masu yawa a gabanta, "Gashi idan zaki gayyaci wasu", " Au har an bugu IV, ni angon ai fushi nake dashi, tunda bai tab'a zuwa mu gaisa ba, kullum sai dai yace a gaishe ni", Afra tayi dariya tace "Soon zai zo ku gaisa", " Toh Allah ya yarda", "Amin, bari na tashi sauri nake, mama na jirana zamu je wani wuri", " Toh ki gaisheta, ina nan zuwa In Shaa Allah", "Allah yasa, nasan halin ki", "Auren ki guda, ai dole nazo ayi shirye shirye dani", " Sai kin zo", Ta mata rakiya bakin k'ofa ta dawo ciki.
Al'ameen na zaune falon shi, yana operating system, Haidar na gefen shi na wasa, Farda ta shigo, ta gudun shi yaje ya rungumeta, Ta d'aga shi sama tana mishi wasa, Yana dariya, Zata ajiye shi ya mak'e yak'i sauka, Ta juya kan Al'ameen tace "Sannu da aiki", " Sai yanzu kika lura dani, ta yaron ki kawai kike", "Tuba nake", Ta fad'a tana murmushi, "Ba zan karb'i tuban ba, sai an mun kisses guda 3", Dariya tayi ta k'arasa wurin shi, ta manna mishi kiss guda 3, Ya kama hannun ta ya manna mata d'aya, " Bara naje na wasa ruwa dawowa ta kenan, nazo nan", "OK, ki kular mun da kanki", " I will", "Haidar sauka ko, naje nayi wanka", Ya k'ara mak'ale ta, " Toh muje na kai ka wurin Mummy Meenal",
YOU ARE READING
MEENAL WA LAMEEN
Romance"A da ina son ka ina k'aunarka ina ganin girman ka , k'imar ka mutuncin ka darajar ka, A yanzu na tsane ka tsana mafi muni, ba wanda na tsani gani kamar ka, ka aikata abunda ko kafiri yayi sai al'umma tayi Allah wadarai dashi, Wallahi Wallahi Wallah...