47

1.1K 76 6
                                    

*MEENAL WA LAMEEN*

*Written 2013*
*Posted 2019*

'''ZEE YABOUR'''
*Follow and vote me on wattpad @ZeeYabour*

'''IN DEDICATION TO'''
*Zakiya Musa Bala*
*Hafsat Salisu*

_*Haske Writers Association*_

*47*

   A hankali ta mik'e ta nufi sashen ta, Kanta ya mata nauyi, Duniyar ta mata zafi, Ta rasa ina zata sa kanta taji dad'i, Wayarta ta lalubo, ta kira Afra ko zata rage damuwa, Bugu d'aya Afra ta d'auka, Suka shiga hirar duniya, Rabin hirar Afra ce mai bada labari.

    Haidar tuni yayi bacci kan gadon Al'ameen, Da wuya yayi kuka bai yi bacci ba, Kwanciya yayi gefen sa ya rungumo sa cikin sa, Ya shiga tunani, Bai san sai yaushe damuwa zata bar shi ba,

   Farda shiru bata ga Al'ameen ya maido Haidar ba, Tana son zuwa sashen, tana tunanin suna tare da Meenal bata so taga laifin ta, Kiran sa tayi, Ya d'aga, "Dama naga ne baka maido Haidar ba", Ta fad'a a sanyaye, komai na Farda cikin natsuwa take yin sa, " Yayi bacci, ki bar shi a nan ya kwana", Tace "To, sai da safe",

     A zuciyar ta tana jin ba dad'i, tun ranar da aka haife sa take kwana dashi, Tana addu'a Allah yasa ba rabata dashi zai yi ba, Ya koma hannun Meenal, Idan hakan ta kasance ba zata ji dad'i ba, Gashi har yau ko b'atan wata bata tab'a yi ba, Da tunani iri-iri a ranta bacci ya d'auke ta.

     Farda tana hanyar zuwa office d'in Al'ameen, Layla ta fito tana sauri, Suka yi kaura, takardun dake hannun ta suka zube, Farda ta duk'a zata d'auko mata, Tayi saurin hanawa ta hanyar d'auka da kanta, Ta shiga had'a su wuri d'aya,  alamun mara gaskiya ya bayyana akan fuskarta, Farda ta bita da kallon mamaki da tuhuma, Ta dake tace " Ya dai Matar Al'ameen, kika kafeni da ido", Murmushi Farda tayi tace "Ba komai", Ta wuce, Tabi bayanta da kallo, Zuciyar ta cike da zargin ta.

   Office d'in sa ta k'arasa daidai lokacin ya fito daga toilet, " Kece nake jin motsin ki?", "A'ah yanzu na shigo, Layla ce", " Layla kuma, shine bata jira ni ba", Ya d'age kafad'a alamar rashin damuwa, Kujera ya zauna, Tace "Dama wata friend d'ita ce ke so a mata designing gida", " OK, yanzu ina wani aiki we will talk later", "Okay", Ta fad'a tana mik'ewa.

    A office nazarin yanayin Layla ta shiga yi, ta shigo ta fita ba tare da ya sani ba, Reactions d'in ta ya nuna rashin gaskiya, Dole zata sama mata ido to clear doubt.

    A gajiye sosai ya dawo gida, Duk yau bai saka Meenal a ido ba, Zuciyar sa na tursasa shi akan yaje ya ganta, Yana son hana kanshi,  duk lokacin da ya ganta zuciyarsa kan shiga yanayi, wanda hakan ke haifar masa da matsala.

     Zaune take a falo tana kallo, Gefenta plate ne na apple tana ci, Tunanin Haidar da Baban sa ne ya cika zuciyar ta, Kewar yaron ta da son jin shi a kusa da ita take, Mahaifinsa kuwa haushin sa take ji na rashin nunawa damuwa a kanta, Sai a wuni a kwana bata sa shi a ido ba.

     Alamar motsi da taji a bayanta yasa ta juyo, Idonta ne suka sark'e cikin nashi, Tayi saurin kawar da kai, saboda fad'uwar gaban da taji, Shima hakan yaji, Zuciyar sa na harbawa da sauri,

   Juyawa tayi ta cigaba da kallo, duk da hankalinta baya kan kallon, Ta rasa dalilin da yasa zuciyarta ke bugawa da sauri, tana jin rashin natsuwa da tsayuwar sa a kan ta,

   " Baki iya gaisuwa bane?", Taji muryar sa, Kamar ba zata yi magana ba, Tace "Na iya, ra'ayin ne bani da",

   Danne Zuciyar sa yayi, dake tunzura shi ya falla mata mari, Juyawa yayi ya fice tare da buga k'ofar falon da k'arfi,

    Siririn tsaki taja, Kallon gaba d'aya ya fita ranta, Ta kashe TV, Ta shiga d'aki ta kwanta, Tana jin ranta baya mata dad'i, Tun ranar da ya mata fyad'e tayi bankwana da farin ciki da walwala, Shine mutumin da ya zama silar rugujewar farin cikin ta, Har kullum shi ke k'ara jefata cikin damuwa, Ganin sa ba abunda yake haifar mata sai matsala, Me yasa ma zata rik'a damuwa akan rashin nuna kulawar sa gare ta, bayan babu wanda ya kai shi rashin sonta, Ganin tunanin zai iya haifar mata da matsala, Ta d'auko Qur'ani ta fara karantawa, A hankali taji natsuwa na saukar mata.

MEENAL WA LAMEENWhere stories live. Discover now