19

893 63 4
                                    

*MEENAL WA LAMEEN*

*Written 2013*
*Posted 2019*

   '''ZEE YABOUR'''
*Follow and vote me on wattpad @ZeeYabour*
   
          '''IN DEDICATION TO'''
*Zakiya Musa Bala*
*Hafsat Salisu*

       _*Haske Writers Association*_

*19*

   Daga ranar, idan zasu yi karatu, Fahad na kiran Farda, Al'ameen ya koya musu tare, Sosai take fahimta kasancewar wanda take tsananin k'auna ke koya mata, Al'ameen bai tab'a mata magana ba, Karatu kawai yake koya musu ya tashi abun sa, Idan tace Sannu, Yace Yawwa baya k'arawa da wani abu, Wataran ma kai kawai yake d'agawa, Yau ma yana gama koya musu ya tashi, Farda tabi bayan shi da kallo har ya b'ace ma ganin ta.

     Fuska d'auke da damuwa tace "Fahad kana ganin Al'ameen kuwa zai so ni", " In shaa Allah zai so ki, ki cigaba da bin abun a hankali, kina addu'a", "Toh", Ta fad'a tare da sauke ajiyar zuciya.

    Layla a kullum cikin tunkarar Al'ameen take, bayan text messages da  take mishi, tana k'ara zubar ma kanta girma a wurin shi, ba tare da ta sani ba, Text mai yawa mai d'auke da zafafan kalaman soyayya ta tsara ta tura mishi, Ganin sunan Disturber yayi appearing kan screen na wayar yasan itace, haka ya mata saving, Tsaki yayi, Texts d'in ta sunfi 50 bai bud'e ba.

     Meenal ta fara sakin jiki da Habeeb, Yau ma ya d'auke ta sun tafi wurin shak'atawa, Abu d'aya ne bata so game dashi, yawan son tab'a ta da yake, Sau da yawa ya kan kama hannun ta, ta k'wace, Sai yayi murmushi.

     Siyayya ya mata sosai na kayan k'walama suka dawo gida, Ummi tace " Meenal yar' gata, Al'ameen ya tafi ga Habeeb zai maye miki gurbin shi", Ta tab'e baki tace "Tabb Yayana is irreplaceable", Maganar ta soki Habeeb, ya rasa dalilin da yasa yake kishi da Al'ameen, Ummi tayi dariya, A falo ta baje, tana shan ice cream da chocolate.

     Meenal a Js1 tayi k'awa Afra (New comer ce),  komai tare suke, Har gidajen juna suke ziyara, Ummi tasan Maman Afra a dalilin k'awancen su, Kullum labarin Ya Lameen take bata, ta kan ce tana so taga Ya Lameen d'in nan.

    Meenal nata faman zuba ma Lameen surutu a waya, Afra na zaune gefe tana kallonta, " Ya Lameen ga friend d'ita zaku gaisa", Kamar yace ta bar shi, sam baya son abunda zai had'a shi da mace, Da rawar jiki Afra ta karb'a, " Ina wuni?" Ta fad'a cike da ladabi, "Lafiya lau", " Ya School?", ta tambaye shi, "Lafiya" bai jira me zata k'ara cewa ba ya kashe, Afra tabi wayar da kallo tana mamakin shi, Tace "Haka Yayan naki yake dama, gaskiya bashi da kirki", " Kada ki k'ara cema Yayana haka", Taja bakinta tayi shiru, tana mamakin wannan isa tashi, yana amsa waya da k'yar, zata so ganin sa a fili.

    Haka rayuwa ta cigaba, Al'ameen na jin dad'in zaman sa London, Daddy yaja sa jiki sosai, Haka Saratu, Idan ba fad'a maka akayi ba, zaka d'auka su suka haife shi.

     Mubarak ya kai Meenal wurin Nusayba, Da dare zai dawo ya d'auke ta, Suna zaune d'akin Nusaiba, Meenal na bata labarin Ya Lameen, Khalil yayi sallama ya shigo, Matashin saurayi mai ji da kyau da naira, Meenal ido tabi shi dashi Shine Wanda ya tureta a asibiti, "Aunty Nussy dama kin San shi?", " He is my brother ", " Amma bashi da kirki ba kamar ke ba", Dariya Nussy tayi tace "Me ka mata ne Khalil?", " Shareta Sis, bata san me take ba", Ran Meenal ya b'aci matuk'a, A hasale tace "Kai ne baka san me kake ba" Taja dogon tsaki, D'aga hannu yayi zai mareta, Nusaiba ta rik'e mishi hannu, "Are u out of ur sense?, kasan me kake shirin yi kuwa?", " Yarinyar nan bata da kunya, ki bari na koya mata hankali", "Fitar mun a d'aki", Ta nuna mishi hanyar fita, Ya fice rai a b'ace.

   Meenal ta rik'e fuska, ta k'udundune gefe d'aya, Nussy ta d'agota tace " Sorry my dear, me ya had'aki dashi ne?", Ta fad'a mata abunda ya faru a asibiti, "Ai Khalil bashi da kirki, ki daina kula shi", Meenal tace " Toh"

     Tana komawa gida, ta karb'i wayar Ummi ta kira Al'ameen ta bashi labari, "Da ya tab'a mun k'anwata da na biyo flight gobe nazo nayi dealing with him", " Yayana idan ka dawo zamu je ka mishi warning kada ya k'ara attempting mari na", "Toh Lil-sis", Nan ta shiga bashi labarin School almost 2hours suna waya.

    Al'ameen tsaye gaban dressing mirror yana d'aura agogon shi na kamfanin rador, Turaruka designer ya shiga fesawa sunfi biyar, Smiling yayi tuna da 9ja ne, Meenal zata kalle shi tace " Ya Lameen kayi kyau" , Yace "Thank you My lil sis"

    A falo ya tarar da Aunty, Ta kalleshi tace "Wannan d'aukar wanka Al'ameen, ko ka samu mana suruka", Smiling yayi yace " Ni da nake jira ki haifi mace, ta girma na aura", Dariya Aunty tayi, tace "Ai ka mata tsufa" , "A'ah Aunty ki bari tayi deciding da kanta", " Toh shikenan", "Na tafi School", " Allah ya bada Sa'a ya tsare", "Ameen"

     Al'ameen na fitowa daga mota, Idon Farda ya sauka kansa, ta sauke ajiyar zuciya tana lumshe ido, "Ya salam Allah yayi halitta anan" Shine abunda ta furta, Daga gefenta taji wasu mata na cewa "Anya kuwa Al'ameen d'an Nigeria ne", (Ni zee nace ruwa biyu ne, Ummi yar' Lebanon ce), Wata tace " Ni kaina ina doubting, Kyan sa da had'uwar sa ya wuce tunani", Farda wani kishi ya taso mata ta watsa musu wani shegen kallo ba tare da sun san tana yi ba, Ta mik'e ta bar wurin,

   Gab da zai shiga class Layla tasha gaban sa, Yau ta kai shi mak'ura, A fusace yace "Get out of my way", K'in matsawa tayi sai ma ido da ta kafe shi dashi, " Bakya cikin jerin mata masu aji, wacce irin zuciya ce dake, meyasa bakya fahimtar bakya gabana Layla, I beg u let me be", Tuni k'walla suka cika mata ido, "Kace mun duk abunda zaka ce Al'ameen, son ka ne bazan fasa ba kuma sai na aure ka", Tsaki yaja yace " Out of my way ", Ta matsa gefe tana sharar k'walla, Farda na kallon su, Layla ta bata tausayi dan tasan rad'ad'in so, sai dai tana addu'ar Allah yasa kar ya wulak'antata itama idan ya fuskanci tana son shi, Wata zuciyar tace " Ai ke ba zaki bayyana masa ba, ba zaki kai kanki gare sa ba", Ta sauke numfashi tana fad'in "Allah yasa na zamo mata a wurin Al'ameen"

   
  Ranar Layla wuni tayi kuka, Friends d'in ta na lallashin ta, Wanda basa ganin laifinta akan son da take ma Al'ameen dan ya kai a so shi.

   Cikin Aunty ya tsufa dan kuwa haihuwa yau ko gobe, taso zuwa 9ja Daddy ya hana ta, Gani yake idan ta tafi ita kad'ai zata rasu kamar yadda Salma ta rasu, Al'ameen idan yana gida yana taya ta da wasu ayyuka, Allah ya zuba mishi tausayi, musamman mace mai ciki.

    Da daddare ne suna kitchen, yana taya ta soya doya, Nak'uda ta taso mata, A rud'e ya kira Daddy, suka d'auketa zuwa asibiti, Cikin awa d'aya ta haihu twins yara maza, Farin ciki wurin Daddy da Al'ameen ba'a magana, Nan da Daddy ya kira waya ya sanar da yan' uwa, Kowa nata murnar samun yan' biyu.

   Ba b'ata lokaci aka sallame su, suka dawo gida, Layla da taga yasa twins d'in a IG, ta shirya zuwa barka, Da k'atuwar ledarta ta barka, Suna zaune falo sai jin sallamarta suka yi, Al'ameen ji yayi kamar ya tashi ya mammare ta, Ta gaishe da Aunty da neighbors d'in ta Turawa da suka shigo, Suka amsa da sakin fuska, "Sai dai ban gane ki ba", Fad'ar Aunty, " Budurwar Al'ameen ce", Mutuwar zaune yayi, mamaki da tsoron Allah suka cika shi lokaci d'aya, Duk da Aunty taga rashin kunyar ta, ta basar tace "Sannu ko", Bari a kawo miki ruwa, Ta kira mai aikin ta, da aka kawo mata tace " Ta kawo mata ruwa", Sakin jiki tayi tasha lemo taxi snacks ba kunya, Bata dad'e sosai ba, ta mik'a kayan barka hadda kud'i ta tafi.

    Al'ameen ya mik'e yabi bayanta, Gyalenta ya fisgo da k'arfi ta juyo, Saukar mari taji, Tayi saurin dafe kuncin ta, "Ke dabbar ina ce, mannerless, a gidan uban wa kika zama budurwata, this should be the last time u will try this non sense, bana sonki Layla, I will never love you", " Ni ka mara Al'ameen, dan kawai na nuna ina son ka", "Bana son soyayyar taki, stay away from me", " Sai kayi dana sanin mari na" Ta fice a fusace.

   

*Follow*
*Vote*
*Like*

*ZEELISH*💕
  
    

MEENAL WA LAMEENWhere stories live. Discover now