02

1.4K 138 0
                                    

*MEENAL WA LAMEEN*

*Written 2013*
*Posted 2019*

   '''ZEE YABOUR'''
*Follow and vote me on wattpad @ZeeYabour*
   
          '''IN DEDICATION TO'''
*Zakiya Musa Bala*
*Hafsat Salisu*

  *02*

  ® _*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*_

     A kwana a tashi Ummee nata rainon cikin ta har ya shiga wata tara,  haihuwa yau ko gobe, Tashi da k'yar zama da k'yar, Cikin na bata wahala kasancewar na farko.

     "Ban san wane irin murna Kwaise zata yi idan ta ganni", Salma ta fad'a tana shirya kayanta cikin akwati, Daddy mijinta wanda k'anin Bappa ne yace " Nasan zata yi murna sosai kam, amma hankalina bai kwanta da tafiyar ki ba", Da mamaki ta juyo ta kalle shi tace "Saboda me?", " Dan lafiyar ki", "Ka kwantar da hankalin ka In shaa Allah Lafiya zanje na dawo", " Toh Allah ya tsare ya kai ki lafiya", "Ameen, bana so ka sanar dasu zuwa na surprise nake so nama Kwaiseh", Kafin ya bata amsa Habeeb ya shigo yaro d'an shekara 7.

    " Mummy zan bi ki" Ya fad'a, "A'ah Habeeb ka zauna tare da Daddy da Ya Hafeez zan maka tsaraba da yawa", Ya fita yana tura baki ba tare da yace mata komai ba.

     K'arfe goma na dare jirgin su Ya d'aga daga London zuwa Nigeria.

    Ummee sam bata jin dad'in jikinta, ta rasa inda zata sa kan ta taji dad'i, Ga gabanta da yake yawan fad'uwa, Addu'o'i take ta karantuwa, Wajen asuba ta tashi da matsanancin nak'uda, Da k'yar ta rarrafa falo ta k'wala wa d'aya daga cikin masu aikin ta kiran ta, Da sauri ta nufi sashen Mami, Aka d'auketa zuwa asibiti.

    Labour yazo mata da sauk'i, K'arfe 6 na safe ta haifu santalelen yaron ta Namiji, Su Mami da aka sanar dasu an samu namiji, basu yi wani murna ba, Amma sun godewa Allah da ya sauketa lafiya, Yaron kamar shi Sak da Bappa, Ummee godiya take yiwa Allah da ya nuna mata k'wan ta a duniya, Kallo d'aya zaka mata kasan tana cikin tsananin farin ciki, Sai dai gabanta bai fasa fad'uwa ta rasa dalili.

    An sallame su sun dawo gida, Anan suka tarar da mummunan labari, Allah yayi ma Salma rasuwa, Daga airport zuwa gida motar su tayi accident, Ummee suma tayi, Da k'yar ta farfad'o da sunan Salma a baki, Mutuwar ta ta matuk'ar girgiza family, Ummee tayi kuka kamar ranta zai fita, Sai da gab'a d'aya kamanin ta suka canza.

     Daddy ya taho tare dasu Hafeez, Kuka kawai yaran ke yi, Shima Daddy ya kasa daurewa yana ta zubar hawaye.

     Ummee bata cin abinchi, ruwa kad'ai take sha, bata samu ruwan nono ba, Jariri nata tsandala kuka, Sai dai aka bashi madara, Shi kad'ai take kallo taji sanyi a ranta, Dan mutuwar Salma ba k'aramin girgizata tayi ba.

      Ranar suna ba'ayi shagalin suna ba, An yanka rago yaro yaci suna Aminu Al-Ameen, 'Yan uwan Ummee daga Lebanon sun zo, Taji dad'in ganin su sosai, Kwana biyu suka yi suka koma.

     Daddy ya yanke shawarar barin su Hafeez a Nigeria, Bappa yace su zauna gidan shi,  Habeeb wurin Ummee, Hafeez wurin Mami, Yaran na samun kula sosai sam basa maraicin uwa, an sasu makarantar su Mubarak, Hafeez shine sa'an Mahad, Habeeb kuma Mujeeb.

             *7 years later*

   Al-ameen ya tashi yaro mai hazak'a da saurin fahimtar abu, Duk yafi yaran gidan kyau, Yana da zuciya sosai, Wani lokacin zuciyar shi har tsoro take ba Ummee, ta kan bashi ruwan la'asar, Bata sake ko b'atan wata ba, Kullum maganar shi "Ummi yaushe zaki haifa mun k'anwa", Ta kan ce kayi ta addu'a Al-ameen sai yace toh. Yana primary 2, sam baya wasa da karatu.

     Mahad da Hafeez sun kammala secondary, Bappa ya samar  musu admission Cyprus, Mubarak yanzu shekarar shi ta biyu kenan a India yana karantar medicine, Gidan sun rage saura Habeeb, Mujeeb, Sadeeq da Al-ameen.

      Al-ameen ya shigo yana ta huci, buttons na rigar shi duk sun b'abb'ale, " Yau kuma dawa kayi dambe?" Ummi ta fad'a tana hararar shi, Sadeeq ya shigo yace "Ummi wallahi Al-ameen baya ji, kusan kullum sai yayi dambe a school, ko yayi ta dukan yara", Ummi ta jawo shi ta murd'e mishi kunne tace " Ba ka ji ko , Me yasa kake dukan yara?", Cikin isa yana magana kamar baya so Yace "Bana son raini"

Dariya ya bata, Ta sake shi tana dariya tace "Yanzu har kasan raini, ohh Al-ameen girman ka da kallo", Ya wuce ciki yana huci, Ummi tabi bayan shi da kallo tana fad'in " Allah ya shirya"

   Tun da ya shiga d'aki bai fito ba, Yayi zuciya kenan, Da k'yar Ummi ta lallashe shi yaci abinchi, Ya nufi sashen Mami.

     Ummi ta cire ran sake haihuwa, Addu'ar ta Allah ya raya mata Al-ameen yasa ya zame mata tamkar yara dubu.



*Yawan Comments d'inku yawan typing*


*ZEELISH*💞

MEENAL WA LAMEENWhere stories live. Discover now