*MEENAL WA LAMEEN*
*Written 2013*
*Posted 2019*'''ZEE YABOUR'''
*Follow and vote me on wattpad @ZeeYabour*'''IN DEDICATION TO'''
*Zakiya Musa Bala*
*Hafsat Salisu*_*Haske Writers Association*_
*33*
Al'ameen baya iya k'in d'aukar wayar Layla, Ko sau nawa zata kira zai d'auka ya saurare ta, Shi kansa bai san meyasa yanzu sam baya jin haushin ta ba, Layla kam sai murna da rawar kai burin ta d'aya ya rage ya aure ta.
Khalil baya zuwa gidan idan Al'ameen na nan, Ko yazo da yaga lokacin dawowar sa ya kusa, yake tafiya, Baya son rigima, Meenal itama duk abunda zai sa Al'ameen yaga laifin sa bata yi.
Al'ameen ya samu peace of mind ganin yadda Meenal ke basa kulawa ta musamman.
Zaune yake a d'akin sa, yana waya da Layla cikin natsuwa, "Masoyina ina son ganin ka yau", Kamar wanda ake wa dole yace " Ki bari mu had'u office gobe", "Uhmm amma naso ganin ka yau", Ta fad'a cikin kisisina, Jin yayi shiru tace " Amma Allah ya kaimu goben", "Ameen"
Shigowar Meenal yasa shi kashe wayar, Da murmushi yace "K'anwata", kafin ta amsa wayar sa tayi ringing, Idonta ya kai kan sunan Layla da ya fito kan screen, A ranta tace " Dama tana nan", Ta kawar da zancen tace "Ummi ce ke neman ka", " OK Ki ce mata ina zuwa",
Text yama Layla, Zai kirata back, Ummi ke kiran sa, Riga ya saka dan daga shi sai singlet ne, Ya sami Ummi a falo, Kusa da ita ya zauna, Yace "Ummi na", " Na'am", "Sannu da hutawa", " Yawwa", Ta numfasa tace "Maganar had'a lefe ga biki na gabatowa, ban ji kana magana ba", Gaban sa ne ya fad'i, kwana biyu yama manta da zancen auren Farda, Yace " Ban manta ba Ummi, ina jiran naji daga gare ki ne", Tayi murmushi tace "A Dubai nake son had'a lefen, daga can zamu siyo kayan d'akin Meenal", " Toh Ummi", "Ka kawo abunda zaka bayar, Bappa ya d'auki nauyin yin saura", Ya d'aga kai tare da godiya da yi ma Bappa addu'a.
Karon farko da yaji baya son auren, A da sam bai damu ba, Wunin ranar yayi shine sukuku, Duk da yana k'ok'arin kawar ma kansa da damuwa.
Yana zaune office d'in sa, Yana duba wasu files, Layla ta shigo cikin shigar da bata dace da musulma ba, Kallo d'aya ya mata ya kawar da kansa saboda yadda tsigar jikin sa ta tashi, Tayi shigar ne dama dan ta jawo hankalin sa, " Sannu da hutawa Masoyina", "Yawwa" Ya amsa ba tare da ya kalle ta, "Naga kamar baka farin ciki da zuwana", " Ko kad'an, ina d'an wani aiki ne", Ta saki wani malalacin murmushi, tana k'ok'arin kamo hannun sa, Ya fisge, Tare da d'ago kai cikin b'acin rai, Suna had'a ido ya kasa ce mata komai, sai jikin sa da yayi sanyi.
Hira take jan sa, Yana amsawa, Farda ta turo k'ofa ta shigo dan ya cire security, Ganin shi tare da Layla suna hira, Gabanta yayi mummunan fad'uwa, Take wani kishi ya lullub'e ta, Ta juya zata koma, "Dawo, ina zaki?", Taji ya fad'a, Layla ta juyo tana bin ta da kallo mai cike da kishi da tsana, Amma saboda mak'ira ce Tayi faking smile on her face tace " Sannu Farda", Ta tattaro natsuwa cike dakewa tace "Yawwa", K'arasa yayi gaban table d'in sa, Ta ajiye wasu takardu tace " Ka duba new designs daga Mexico", Tana fad'ar haka ta fice daga office d'in, Zuciyar ta na cigaba da bugawa.
Gaba d'aya ta kasa sukuni, Zuciyar ta zugi take na tsananin kishi, Layla da Al'ameen suna hira, Shi da baya hira da kowa sai k'aunar sa, Ko ya kamu da son Layla, Kan ta ya sara tana addu'ar Allah yasa ba haka bane, dan tsab zuciyar ta zata buga.
Al'ameen sam yak'i ba Farda fuskar da zata tambaye sa, Meye tsakanin sa da Layla, abun na cin ta a zuciya, Sau da yawa ta kan ga Layla tazo consolio d'in, Bata zarcewa ko'ina sai office d'in sa, Taci alwashin yau zata tambaye sa cikin siyasa.
YOU ARE READING
MEENAL WA LAMEEN
Romance"A da ina son ka ina k'aunarka ina ganin girman ka , k'imar ka mutuncin ka darajar ka, A yanzu na tsane ka tsana mafi muni, ba wanda na tsani gani kamar ka, ka aikata abunda ko kafiri yayi sai al'umma tayi Allah wadarai dashi, Wallahi Wallahi Wallah...