54

1.1K 84 9
                                    

*MEENAL WA LAMEEN*

*Written 2013*
*Posted 2019*

'''ZEE YABOUR'''
*Follow and vote me on wattpad @ZeeYabour*

'''IN DEDICATION TO'''
*Zakiya Musa Bala*
*Hafsat Salisu*

*_Haske Writers Association_*

*54*

    *This page is for you Maria gogori and Fatima Ashemi*

     Meenal a kan gadon d'akin Ummi ta tsinci kanta, Tana addu'ar Allah yasa mafarki take, A hankali ta sauko daga gadon ta fito ta nufi babban falon gidan, Cike yake da mutane, Koke-koke na tashi "Allah ya jik'an Farda ya gafarta mata, yarinyar kirki", Ta jiyo muryar wata mata, Ko shakka babu Farda ta riga mu gidan gaskiya.

    Kanta ya sara, jiri ya d'ibe ta tana shirin fad'uwa, Ji tayi an rik'e ta ta baya, Aunty binta ce tace " Ki bi a hankali Meenal, ki sawa zuciyar ki tawakkali", Zama tayi ta rusa kuka, wanda ya jawo hankalin mutanen wurin gareta, aka shiga lallashin ta, "Ba kuka take buk'ata ba, addu'ar ki take buk'ata", Cewar wata k'anwar Ummi, Dan tuni mutanen Lebanon suka iso, kowa ya bud'e baki yabon Farda yake( Shiyasa ake so mutum ya zama nagari, ko ya samu kyakkyawar shaida), Da addu'ar Allah ya wulak'anta wanda suka kashe ta.

    Ummi idonta sunyi luhu-luhu, fuskarta tayi jajir saboda kuka, iyayen Farda mutuwar ba k'aramin girgiza su tayi ba, Mahaifiyar ta duk ta fita hayyacin ta.

    Al'ameen tunda aka dawo kai ta, Ya rufe kansa a d'aki ba irin bugun da ba'a yi ba, Yak'i bud'ewa, ya kashe wayoyin sa,

Moments d'insu da ita yake tunawa, " Zan iya sadaukar da raina a kan ka", Furucin ta dake mishi yawo a kai, "Meyasa kika zab'i ki sadaukar da ran ki a kaina, a daidai lokacin da zuciyata ta kamu da sonki, kika tafi kika bar ni, Allah ya jik'an ki Farda, Allah ya gafarta miki, nayi rashin mace mai hak'uri da kawaici, wanda ya kashe ki, da wanda ke da sa hannu a kashe ki, wallahi ba zai tafi a banza ba,

   Mutuwar ta ta matuk'ar girgiza shi, kuma ta tab'a shi.

   Layla ke ta faman zirga-zirga a d'akin hotel, na bak'in cikin rashin kashe Al'ameen, " Meyasa abubuwa ke faruwa haka?", "Ina mamakin wane irin so take mishi, da yasa ta sadaukar da ran ta a kan shi", Cewar Mahfuz, Tsaki taja tace " ana maganar abun yi, kana maganar so, meye mafita?", "Ki kwantar da hankalin ki, yanzu muje gaisuwa, kada su zargi wani abu, idan mun dawo sai a san abun yi", " Dole kawai zata sani zuwa, babu wanda na tsani gani sama dashi, burina naga ya bar duniya", "Kar ki damu, burin ki ya kusa cika"

    Da kukan munafunci Layla taje gidan gaisuwa, Meenal na ganin ta, ta ji kamar ta shak'eta sai taji k'amshin lahira, Ta tambaya ina Al'ameen, aka ce yana d'aki, taji dad'in haka dama bata son ganin shi,

   Taso su keb'e da Meenal ta tambayeta zancen takardu, tak'i bata dama, tashi tayi ta shige d'akin Ummi, Haka ta k'araci zamanta ta tashi ta tafi.

    Meenal tsakanin ta da mutane ido, bata magana ko gaisuwa aka mata sai dai ta amsa da kai.

   Har aka yi sadakar uku, bata saka Al'ameen a ido ba, tana cikin damuwa na rashin ganin sa, tasan yana cikin matsanancin damuwa da buk'atar taimako, Haidar ma sau d'aya ta ganshi, yana wajen Mami.

     "Kayi hak'uri da tawakkali Al'ameen, Mumini da tawakkali aka san shi kar ka manta mutuwa na kan kowa, Dan Allah kada ka sawa kanka damuwa da zata janyo maka matsala, Farda addu'ar ka take buk'ata", Ummi ke mishi nasiha, Murya a dashe tsabar kuka yace " Toh Ummi", "Yawwa, yanzu zan aiko Meenal ta kawo maka abinci ka tabbata kaci, kayi wanka ka shirya kazo ka gaisa dasu Daddyn ka, D'azu suka iso", Tana fad'ar haka ta fita.

    Ruwan shayi take sha, bread dake gefen ta ko tab'a shi bata yi ba, " Ruwan shayi ne zai k'osar dake Meenal, kina nan da rashin cin abinci ko?", "A'ah Ummi, bana jin dad'in bakina ne", " Allah ya sawwak'e", "Amin", " Muje na bakin abincin Al'ameen ki kai mishi, ki tabbatar yaci, ya shirya ya fito", Kiran sunan shi da aka yi gaban ta ya fad'i, Ta amsa da "Toh", Jiki a sanyaye tabi bayan Ummi,

MEENAL WA LAMEENWhere stories live. Discover now