*MEENAL WA LAMEEN*
*Written 2013*
*Posted 2019*'''ZEE YABOUR'''
*Follow and vote me on wattpad @ZeeYabour*'''IN DEDICATION TO'''
*Zakiya Musa Bala*
*Hafsat Salisu*_*Haske Writers Association*_
*51*
Meenal sai dare ta koma gida, Jiki a sanyaye, Zuciyarta cike da so, k'auna, da kewar Al'ameen, A falo ta tarar da Ummi,
"Daga ina kike?, Ina ta neman ki", Ummi ta tambaya tana tsare ta da ido, dan ta hango damuwa tattare da yar'ta ta, " Naje gida ne d'auko wasu kayana", Ta d'auko kaya kala biyu dan tasan Ummi zata tambaye ta, "Shikenan, amma ki rage damuwa, ki dage da addu'a", Ta d'aga kai sama, tare da yin hanyar d'aki,
A bakin stairs tayi karo da Farda, Ta tambayeta " Ya jikin Haidar?", "Jiki da sauk'i, ya ware yana ta wasan shi", " Mashaa Allah, Allah ya K'ara lafiya", "Amin",
Ruwa ta watsa tabi lafiyar gado, dan kanta ke sarawa, Cikin ikon Allah bacci ya d'auke ta.
Al'ameen kwana yayi sak'e sak'en yadda zai bar wurin nan, da tunanin wacece tasa a kawo shi nan?, " Farda?" Ya tambayi kansa, Yayi saurin cewa "No Farda will never to this", " Meenal?", "Despite she hates me nasan bara ta tab'a haka ba, conspiracy ne dan a b'atar mun da tunani, yanzu haka namiji ne, Let me get out of here, ko waye will pay for it"
Bayan sallar asuba, gari bai fara wayewa, Al'ameen ya tashi a hankali, Cikin sand'a ya b'alla k'ofar d'akin, Mutumin dake bakin k'ofar ya murd'ewa kai, Ya barshi kwance, Har ya kawo bakin main gate na gidan babu wanda ya gansa, Hodar gusar ma mutum da hankali, Da Dantse ya yar a d'akin ya d'auka, Ya fiddo daga aljihu, Ya watsa wa mutum uku dake bakin gate ba tare da sun ankara ba, sai fad'i suka yi a wurin, Ya bud'e gate ya fara gudu, Yayi gudun kusan minti 30 amma bai hango alamar bil'adama ko d'aya ba, balle gida, daji ne gaba da baya, Ya gaji da gudu ya koma tafiya.Farda ta karb'i mukullin office na Layla wurin mai shara, ta bincike ko'ina, bata ga wata alama da ta nuna Layla nada sa hannu a d'auke Al'ameen ba, ko takardu na filin shi, Still bata gamsu ba, dan zata iya b'oye su wani wuri, Tana rok'on Allah ya tona asirin ko su waye.
K'arfe 9 na safe Al'ameen ya shigo gari, Ya galabaita sosai, Ko gani baya yi sosai, Mai napep ya tara ya mishi kwatancen gidan su Bappa, Yasan suna can cikin tashin hankali.
Dantse da murna ya tashi yau Al'ameen zai saka hannu, Ba sallah ba salati ya mik'e ya nufi d'akin da yake, Yaron sa da ya gani kwance baya numfashi ya firgita, Ya lek'a d'akin babu Al'ameen, Wajen ya fito hankali tashe, yaga masu gadin shi kwance babu mai motsi,
Ihu ya saki yace "Ya Gudu, am dead", Wayarsa ya lalubo ya shiga kiran Layla, bugu d'aya ta d'auka, " Ya gudu, aiki ya lalace", Ihu ta kurma ta wayar cikin d'aga murya tace "Shikenan, garin yaya ka bari ya gudu", " Ranki ya d'ade....", "Shut up! Useless", Ta katse wayar, Ranshi ya b'aci matuk'a da ta kira shi Useless, Ga haushin rasa kud'in da ta mishi alk'awari, Yaran sa biyu dake wani gida a cikin dajin ya kira, Yace su bazama neman sa.
A bakin gate mai napep ya tsaya, Ya fito yace mai gadi ya sallame sa, Audu sai washe baki yake yana faman yi mishi sannu da zuwa, Hannu kad'ai ya d'aga masa ya shiga ciki,
Tun daga bakin k'ofar falo yake jiyo ana waya wanda hands free yake, " Yaron nan ya gudu fah", Kansa ya sara yana son yaji shin da gaske ne kunnen sa ya jiye masa haka ko kuwa, Kafin ya dawo tunanin da ya tafi, Ya juyo muryar Meenal nacewa "Garin yaya kuka barsa ya gudu, kuna aikin me har ya gudu", "Kiyi hak'uri ranki ya d'ade", " Kar Ku bari ya koma gida, ku bi bayansa ku kamo shi", "Toh Ranki ya d'ade"
Ta kashe wayar, D'agowar da zata yi taga Al'ameen tsaye a kanta, Cike da farin ciki ta mik'e tsaye tare da fad'in "Ya Lameen",
D'aure fuska yayi kamar bai tab'a dariya ba, Yace " Kin sa an kamani sai kuma gashi na dawo gida, ki sani ba zaku k'ara nasara ba",
Cike da tsananin mamakin take kallon sa tabbas yaji wayar da take, "Ya Al'......", Hannu ya d'aga mata " Bana buk'atar jin komai daga gare ki", Kafin tace wani abu, Da gudu Farda ta rungume sa, tare da sakin kukan farin ciki,
Ya k'ank'ame ta yace "Meye na kukan tunda gani na dawo, duk da ba haka wasu suka so ba", " I miss you my dear", "I miss u more", Ya fad'a da manna mata kiss,
Meenal wani abu taji ya daki k'irjinta, dishi-dishi ta fara gani, k'afafun ta bara su d'auke ta ba, tuni ta kai zauna, Tana ji wasu hawaye masu zafi na zarya kan kumatun ta.
Jin motsin su Ummi, ya saki Farda, " Al'ameen kai ne " Ummi ta fad'a tana rungume shi,
Kan ace haka gida ya cika da murnar dawowar sa, Kowa ka gani farin ciki ne akan fuskar ka sab'anin Meenal, Mami ta kalleta tace "Meenal meye na kukan, ai murna zaki yi ya dawo", Tayi murmushin yak'e tace " Murnar dawowar sa ce ta saka ni kuka", "Toh ya isa haka", Tasa hannu tana share hawayen, zuciyarta na k'una, Dole ta fahimtar da Al'ameen abunda yake tunani bashi bane.
Bayan ya huta yake sanar dasu abunda ya faru gare shi, Kowa ya jinjina lamarin, tare da addu'ar Allah ya tsare gaba, Bappa yace " Za'a sa ayi bincike a gano su waye", Al'ameen yace "A'ah abar komai hannu sa", Bappa yace " Shikenan", Haidar ya manne mishi, Ummi tace " Uhmm Haidar ya gane baban sa", A kayi dariya",
Bappa yace su kwana anan sai gobe su wuce,
Yana zauna d'akin sa yana ma Haidar wasa, Meenal jiki a sanyaye ta shigo, Take far'ar dake kan fuskar sa ta d'auke,
"Ya Al'ameen Dan Allah ka saurareni abunda kake tunani bashi bane", " Me zan saurara daga gare ki, bayan naji komai da kunne na ba labari aka bani ba", "Let me explain to you", " Bana son jin duk wani da zai fito daga bakin ki",
"Kada ka manta wacece ni a wurin ka, ka sani bazan tab'a cutar da kai ba", Juyowa yayi ya kalleta yace " Ke kika manta wanene ni a wurin ki, kika manta bazan tab'a cutar dake ba, Dan haka nima duka na manta su, bana miki kallon k'anwata mai k'aunata, kin nuna mun k'iyayya k'arara",
Kuka ta saki na tsantsar nadama, da rashin fahimtar ta da Al'ameen ya kasa, Ashe shima haka yaji lokacin da yake k'ok'arin wanke kan shi gareta,
D'aukar Haidar yayi ya fice daga d'akin.
Ku k'ara yawan comments da votes na k'ara yawan typing
*Follow*
*Vote*
*Like**ZEELISH*💕
YOU ARE READING
MEENAL WA LAMEEN
Romance"A da ina son ka ina k'aunarka ina ganin girman ka , k'imar ka mutuncin ka darajar ka, A yanzu na tsane ka tsana mafi muni, ba wanda na tsani gani kamar ka, ka aikata abunda ko kafiri yayi sai al'umma tayi Allah wadarai dashi, Wallahi Wallahi Wallah...