34

804 60 4
                                    

*MEENAL WA LAMEEN*

*Written 2013*
*Posted 2019*

'''ZEE YABOUR'''
*Follow and vote me on wattpad @ZeeYabour*

'''IN DEDICATION TO'''
*Zakiya Musa Bala*
*Hafsat Salisu*

_*Haske Writers Association*_

*34*
 

     Ummi farkawa tayi da mummunan fad'uwar gaba, Salati tayi ta sanar da Ubangiji, Ta mik'e, Ta kunna fitila, Lafiyar yaran ta taji tana son ganin.

     D'aukewar numfashin ta yayi daidai da dawowar Al'ameen hayyacin sa, Ganin abunda ya aikata gata kwance cikin jini bata numfashi, K'ara ya saki tare da fad'in "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" , Kansa ya hau juyawa, Anan ya fad'i baya motsi.

    
    Ummi na bud'e k'ofar idon ta ya sauka kan Meenal, Jikinta ne ya hau kyarma, tashin hankali ya lullub'e ta "Waya ma ya'ta wannan aikin, wane azzalumi ne", Hawaye ya wanke fuskarta, A wurin ta durk'ushe, Al'ameen ta hango kwance gefe, Kana ganin yanayin shi zaka san tabbas shi yayi wannan aikin,

      " Al'ameen yama Meenal fya.....", Bata k'arasa ba numfashin ta ya d'auke, Ta fad'i sumammiya.

Dukkan su a gadon asibiti suka tsinci kan su,

   Ummi ta fara farkawa da sunan Allah a baki, Tuno abunda ya faru yasa hawaye masu zafi suka wanke fuskar ta, "Hak'uri zaki yi mu d'auki hakan bisa k'addara", Bappa ya fad'a, Idon sa sun kad'a sunyi jajir, yana jin rad'ad'i a zuciyar sa.

     " Ya Allah wane laifi nayi, na fuskanci wannan mummunan k'addara, Ya Allah ka d'auki raina na huta da ganin wannan bak'ar rana", "Ki tauna kalaman ki Kwaise, kada kiyi sab'o", Cewar Bappa, Kuka ta cigaba da yi kamar ranta zai fita.

     A hankali ya bud'e idonsa, Yana jin kansa ya masa nauyi tamkar an d'aura mishi dutsen dala, Abunda ya faru ke dawo masa cikin kai, Ya runtse ido, zuciyarsa na zafi da bugawa kamar zata fasa k'irjin sa, " Me na aikata, I raped my blood sister", Wata k'ara ya saki yana kakkafewa, A guje likitocin suka shigo, Ganin yanayin sa ya tsorata su, A rud'e suka shiga basa taimakon gaggawa.

    Meenal bata farka ba, Ba k'aramar ta'asa Al'ameen ya mata ba, Sai da aka mata stitches, Amintacciyar Nurse wacce suka saba da Ummi, Daga haihuwar Meenal har Lameen ita ta karb'a, ta duba Meenal, suna son sirri, Ummi ta kalli yar'ta cike da tausayawa, idonta sun kumbura daga gani tasha kuka, Hawaye suka biyo kuncin ta, "Wannan wata jarabawa ce Allah ya kawo musu, addu'a kad'ai zata magance musu",

    Daga Bappa har Ummi babu wanda yabi ta lafiyar Al'ameen, suna tsananin fushi dashi, Mami ce a tare dashi, Sauran Yayyen su duk sun hallara asibitin, basu san meke faruwa ba an kawai ce musu Meenal da Lameen ba lafiya,

Farda taci kuka idonta sunyi luhu-luhu duk da bata san meke faruwa ba, Kukan rashin lafiyar masoyinta take, Ganin yadda ta damu yasa Bappa yace ta koma gida, Baya son ta gano, jinya ta koma kanta.

  Khalil hankalin sa ya kasa kwanciya yayi ta kiran Meenal bata d'auka, Ya shirya zuwa gidan yaga lafiya, Tun a bakin gate Maigadi ya sanar masa suna asibiti, Gabansa ya fad'i yadda bai tab'a ji ba, Motar sa ya shiga yaja sai asibiti, A passage yaci karo dasu Ya Mubarak duk sunyi cirko cirko, " Ya Condition d'in ta?", Ya tambayi Sadeeq, "Har yanzu bata farfad'o ba", Ya bashi amsa cike da damuwa.

   Jikinsa yayi sanyi ya nemi wuri ya zauna, tare da yin tagumi yana mata addu'ar samun sauk'i.

             *After 7hours*

   Khalil da wasu yayyen su Bappa yace su koma gida, Ba da son rai ba Khalil ya tafi cike da tunanin sahibar sa,

    Al'ameen ya bud'e idonsa, Yana jin ina ma ace mafarki yake ba da gaske bane, haushin kansa yake ji, baisan ya akayi ya aikata haka ba,  Da wane ido zai kalli Ummi, Bappa, uba uwa Meenal bai san me zata d'auke sa ba, " Ya Allah ka d'auki raina na huta da abun kunya", Ya dafe zuciyar sa dake rad'adin zafi da ciwo, Damuwar sa wane hali k'anwar sa ke ciki, A hankali ya sauko daga kan gado, Yana bin bango yana takawa a hankali saboda jiri da yake gani,

Kansa na sarawa, Ya bud'e d'akin ya shiga kansa a k'asa, Ummi da Bappa sai Ya Mubarak da Ya hafeez ne a d'akin, A tare Ummi da Bappa suka kawar da kai, Duk'awa yayi gabansu, kansa a sunkuye k'asa ba zai iya had'a ido dasu ba, "Bappa Ummi ina rok'on ku da Allah Ku gafarta mun", A fusace Ummi ta taso ta mare sa, sai da ya kai k'asa, Kafin ya d'ago Bappa ya k'ara masa yace " Allah ya wadarai da halin ka, kayi abunda ko kare ba zai yi ba", Ummi ta k'ara da "Nayi bak'in cikin kasancewar ka d'ana Al'ameen", Cikin d'aga murya Bappa yace " Kaje ka nemi wasu iyaye bamu ba",

A razane ya d'ago murya na rawa yace "Kuji tausayina Bappa ko yanke mun kowane hukunci banda yafe ni", " Ka fita a d'akin nan ko na d'aga maka nono", Cewar Ummi, Ya mik'e jikinsa na kyarma, yana kaiwa bakin k'ofa ya fad'i, Ummi ta fashe da wani irin kuka tana kawar da kanta daga kallon sa, Ya Mubarak suka yi kansa, Mami cike da damuwa tace "Dan Allah Ku fitar dani duhu, meke faruwa?", Bappa girgiza kai yayi, Ya fice daga d'akin

    Al'ameen oxygen aka saka masa dan jawo numfashin sa, Doctor nata fad'a a daina k'ara masa damuwa, Hakan zai sa zuciyar sa ta buga, Ummi da Bappa  sun tsorata da jin bayanin likita, Ummi duk iya tunanin ta ta kasa gane dalilin da yasa Al'ameen yama Meenal fyad'e, Ta bar hakan akan tsananin shak'uwar su ta saka haka, Tayi dana sanin barin su shak'u, Yaranta da su kad'ai ta mallaka a duniya, Hakan ta faru dasu.

   Farda na zaune kan sallaya ta d'aga hannu sama tana addu'a " Ya Allah ka tashi kafad'un Al'ameen, Ya Allah ka bashi lafiya, Ya Allah ka ba Meenal lafiya", Ta k'arasa da hawaye, Tana jin rad'ad'in sosai a zuciyar ta, wanda bana ciwon shi kad'ai bane, ta rasa na meye?

      Layla tayi ta kiran wayar Al'ameen, Switched off, Har office taje aka ce bai zo ba, Ta kasa natsuwa sai faman zirga zirga take tana addu'ar Allah yasa lafiya, Dan jikin ta na bata ba lafiya.
     

    A hankali Meenal ta bud'e ido ta sauke su kan Ummi da ke rik'e da hannun ta, Gani Ummi tayi tamkar Al'ameen, A firgice ta mik'e tana fad'in "Kaji tausayina Ya Al'ameen kada ke keta mun haddi", Ummi ta rungumeta tana fad'in " Nice Ummi Meenal", Wata ajiyar zuciya ta saki, sai kuma d'ib bacci ya sake d'auke ta,

     Kallo-kallo Mami dasu Ya Mubarak kema juna da jin kalaman Meenal, Mami a ranta tace "Zafin ciwo ne bata san me take fad'a ba"

     Kuyi managing wannan

*Follow*
*Vote*
*Like*

*ZEELISH*💕

MEENAL WA LAMEENWhere stories live. Discover now