15

878 77 0
                                    

*MEENAL WA LAMEEN*

*Written 2013*
*Posted 2019*

   '''ZEE YABOUR'''
*Follow and vote me on wattpad @ZeeYabour*
   
          '''IN DEDICATION TO'''
*Zakiya Musa Bala*
*Hafsat Salisu*

       *_Haske Writers Association*_

    *Kuyi hak'uri na rashin ji na akai akai ina exams ne*

*15*

    Sunyi resuming school, New Session ne Al'ameen ya shiga Ss2 yayin da Meenal ta shiga Primary 4, A ranar sai da Layla ta tunkare sa, kamar kullum kallo bata ishe sa ba, Ya wuce ya bar ta tana hawaye, Nana ta dafa ta tace "Layla ya kamata kiyi wa kanki k'iyamul laili ki rabu da Al'ameen ya nuna baya sonki, kada ki sa ma kanki wata matsala fah", Ta juyo ido cike da k'walla ta kalli Nana tace " Wallahi bazan tab'a hak'ura dashi ba, ko ta halin yaya ne sai Al'ameen ya soni", "Toh shikenan, ni na tafi class", Ta wuce ta bar ta tana sak'a abubuwa da dama a ran ta.

     Dukkansu  suna zaune babban falon gidan, Hira suke cike da nishad'i, Bappa yace " Mubarak dai ya tsayar da Mata, Hafeez da Mahad na baku wata 3 ku fitar da mata a tare nake so a had'e bikin Ku", Mami tace "Ka k'osa dai ka fara ganin jikokin ka", Suka sa dariya, Meenal tace " Bappa nima amun aure da Ya Lameen", Duka falon suka sa dariya jin yarintar ta sab'anin Habeeb, Da yaji wani abu ya tokare zuciyar sa, Bappa yace "Aminatu ai Yaya baya auren k'anwar sa, Habeeb dai zamu aura miki", Tayi shiru jikinta yayi sanyi duk da bata san meye aure ba. Habeeb kuwa murmushi kawai yake, Al'ameen a ran shi yace " Dama shine k'udirin su shiyasa yake ta rawar k'afa a kanta, sam k'anwata bata dace dashi ba, she deserve a very rich, classy and decent guy", Meenal ce ta katse mishi tunani ta hanyar cewa "Yayana kana so na auri Ya Habeeb?", A kunne ya rad'a mata " Kada ki yarda ki aure shi", Tayi nodding kanta cike da yarda, Idon Habeeb na kansu, Yana jin wani haushi na kama shi, Ya rik'e hannun ta suka fice falon, Habeeb ya cika yayi fam.

    
  Habeeb na k'ok'arin janyo Meenal jikin shi, ita kuwa tana kaucewa maganar Yayanta tayi tasiri sosai akan ta, Hakan na ba k'aramin b'ata mishi rai yake ba, but wata zuciyar na dangata mishi hakan da yarinta ce zata daina, A kullum soyayyarta k'ara shigar sa take, Yarintar ta da komai nata burgeshi yake ba, Har ya kan ji anya zai iya jira har tsawon shekara 6 ba tare da an musu aure ba, Ba zai kuwa ce a musu aure tana js3 ba ta k'arasa a gidan sa, Da wannan tunanin yake kwana yake tashi, Gani yake kamar za'a k'wace masa ita.

      Al'ameen, Meenal da Ummi ne zaune suna hira, Ummi kan tsinci kanta cikin farin ciki mara misaltuwa idan tana tare da yaranta, tana tuna shekarun baya lokacin da bata haihuwa, Yanzu kuwa sai dai tayi godiya ga Allah. "Allah ya rayuwa mun ku yarana, yayi muku albarka ya kare ku da fitinar duniya da ta lahira", " Ameen Ummi", Suka fad'a a tare.

     " Ummi I want ice cream" Meenal ta fad'a, Al'ameen yace "Muje driver ya kaimu", " Kana da kud'i ne?" Ummi ta tambaya, "Eh Ummi", " A ina ka samu?", "Bappa ya bani", " OK sai kun dawo, ku kula", "Toh Ummi"

     Driver ya kai su, Suka sha ice cream suka ci shawarma, Suna cikin sha Meenal ta d'iba ta shafa mishi a fuska, Shima ya d'iba ya shafa mata, Haka suka dinga wasa suna dariya, Suka dawo gida duk sun b'ata jikin su, Kowanensu ya nufi wurin wanka.

      An zab'i mutum uku da suka fi kowa k'ok'arin a primary 4 zasu yi common entrance tare da Primary 5 students, Meenal tana ciki, Haka Ss2 an zab'a wanda zasu yi SSCE tare da Yan Ss3 Al'ameen na ciki, School ce zata yi sponsoring d'in su, Layla na ganin haka tasa rigima a gida itama sai tayi, Babanta naji da ita, Ba musu yazo school ya zuba musu kud'i, Suka sata cikin wad'anda zasu yi, Al'ameen yaji kamar yace ba zai yi ba, Baya sonta ko kad'an, ta zubar da girman ta a idon shi, baya son mace mara class.

    Ummi ba k'aramin farin ciki tayi ba, Ganin an zab'i yaranta cikin masu hazak'a, Tana addu'ar Allah ya k'ara musu baiwa da hazak'a.

    Ranar har da special girki ta musu, da suka ci ta d'auke su suka tafi yawo, Ta musu shopping, Sunyi murna sosai.

      Al'ameen ya k'ara mayar da hankali kan karatu, Yana so ya fito da excellent result, Meenal ma yana sata karatu.

       Habeeb ya dawo daga office, rik'e da leda cike da kayan k'walama, Sashen Ummi ya nufa, Meenal na zaune falo rik'e da littafi tana karatu, Al'ameen na d'akin shi, Ummi na kitchen, "Ya Habeeb Sannu da zuwa", " Yawwa My Meenal, ana ta karatu", Ta d'aga mishi kai, "Toh Allah ya bada sa'a", " Ameen", Ya mik'a mata leda, Ta karb'a tana godiya, Yace "Ina Ummi?", " Tana kitchen", Ya nufi kitchen.

    "Ummi sannu da aiki", " Yawwa Habeeb ka dawo", "Eh Ummi", " Bak'i zaki yi ne", "Au baka san yau su Daddy zasu zo ba", "Na manta fah, kinsan aiki yayi yawa Ummi, har sun taso ne", " Ai suna gab da isowa ma", "Toh Allah ya kawo su lafiya", " Amin", "Zan je na huta", " Abincin ka na nan kan Dinning table", "Toh Ummi", Yana son Ummi yadda ta rik'e shi tamkar ita ta haife shi, Ko Mamansu na raye kulawar da zata basu kenan.

*Follow*
*Vote*
*Comments*

*ZEELISH*💕

MEENAL WA LAMEENWhere stories live. Discover now