29

803 65 6
                                    

*MEENAL WA LAMEEN*

*Written 2013*
*Posted 2019*

   '''ZEE YABOUR'''
*Follow and vote me on wattpad @ZeeYabour*
   
          '''IN DEDICATION TO'''
*Zakiya Musa Bala*
*Hafsat Salisu*

       _*Haske Writers Association*_

*29*

   Tsaye yake gaban dressing mirror, Ya gama shiri yana saka cufflinks, Meenal ta shigo, Da murmushi ya kalle ta, Sanye take cikin rigar bacci iya gwiwa, Da alamu daga bacci ta tashi, Tace "Yayana har ka shirya, gashi yau na makara wurin had'a ma breakfast", " Ba komai Lil-sis but ya akayi baki tashi da wuri ba", "Jiya banyi bacci da wuri ba", " Kina me?, "Waya", Ta fad'a tare da saka hannu tana rufe fuska alamun jin kunya, Wani abu yaji ya soki zuciyar shi, Take far'ar dake kan fuskar shi ta d'auke, Briefcase d'inshi ya d'auka, Ya rab'a ta gefen ta zai wuce, " Yayana" ta kira shi cikin sanyin murya, Banza yayi da ita ya wuce abun sa, Bin sa tayi da kallo, "Na b'atawa Yayana rai", Ta fad'a a fili kamar zata yi kuka.

     A falo yaci karo da Farda, " Al'ameen please mu tafi tare, motar da ake kaini ta lalace", Kallo bata ishe sa ba, balle ya mata amsa, Yayi gaba abun sa, "Yau waya b'ata masa rai, ko kuwa yan miskilancin ne a kai", Bodyguard d'in sa na ganin shi, Ya fito da sauri ya bud'e mishi, Ya shiga, " Uban me kake jira", Ya daka ma driver tsawa da sai da ta gigita shi, Jiki na rawa yaja motar suka tafi, Farda ta fito kenan, ita driver ya gani ya tsaya, Al'ameen shima yasan ita ce, Bak'in ciki da haushi ya cika ta lokaci d'aya, Kamar tayi kuka, Ta fito ta nemi napep,

    Tun daga gate ma'aikata ke gaishe sa cikin girmamawa hadda tsofaffi (Nace kud'i masu gidan rana, Yaro da kud'i babba), Babu wanda ya amsawa, Ganin haka yasa suka san ran ogan nasu a b'ace yake, Suna ja da baya, Karo yaci da wani, Ya kwashe shi da lafiyayyan mari, Rik'e kunci yayi cikin al'ajabi da b'acin rai, Al'ameen ya wuce abun sa, Zama yayi kan kujerar office, tare da kwantar da ita, "Meke damun ka?", Meyasa kake jin zafi idan k'anwar ka ta kula wani ba kai ba?", Ya jefo ma kanshi tambayoyin da duk iya tunanin sa, bai gano amsar su ba.

  Tsaki yaja, tare da fusgar da iska ta baki, Ya jawo file na contract na FG , Yau ya kamata su tattauna da Farda, gashi baya son magana da kowa, but ya zama dole ko dan cigaban company, Wayar shi ya jawo ya kirata, Ringing biyu ta d'auka, " Where are you?, Kinsan bana son delay", "Ina inda ka barni", Wani wawan tsaki yaja ya kashe wayar, Tabi wayar da kallo tana murmushi, Dama so take ran shi ya b'aci, Tana office d'inta, Akan contract d'in take dubawa,

      Almost 1hour, Sannan ta mik'e ta nufi office d'in shi, Ran shi ya kai mak'ura wurin b'aci, Baya son b'ata lokaci, komai yana so ayi shi on time, Yana ganinta ta k'aramar system tana danna doorbell, Yak'i bud'ewa, Kusan minti 20 tana tsaye, Tsaki taja ta juya zata koma, Ya danna k'ofar ta bud'e, Duk da ran ta ya b'aci, Ta shigo da murmushi zaka rantse bata ji haushi ba, Ya k'ara jin haushi " Lallai Yarinyar nan", Ya fad'a a ransa, "Sannu da aiki", Ta fad'a tana jan kujera ta zauna, Tamkar bai San da zamanta ba, Ya cigaba da sabgogin sa, Ganin ba magana zai mata ba, Tace " Ga designs da nayi, ka duba ka gani ko sunyi",

D'agowa yayi yana dubawa cikin system, Da kai ya mata alamar sun yi, A ranta tace "Ban da Allah ya jarabceni da son ka, wallahi I will not take this", " Ohhh really", Taji ya fad'a, a razane ta d'ago tana kallon sa, da yayi tamkar ba da ita yake ba, Bata d'auka maganar ta fito fili ba, Bayani ya shiga yi mata da hannu, Sai abunda ya zama dole ya fad'a, yake magana,
        
  "Ba'a tab'a humiliating d'ina irin yau ba", Mahfuz ya fad'a, " Hmm kasan halin Oga da zuciya", "Me na mishi da nayi deceiving mari a gaban mutane, ko shi ubana ne, Wallahi he will regret raising his fingers on me", Ya fad'a yana huci, " Yana tak'ama da kud'i ko, sai nayi ruining life d'in shi",

      Meenal rai ba dad'i haka ta wuni, Tayi ta kiran Lameen yak'i d'auka, Lunch ta had'a masa, Ta kira driver tace ya kai mishi, Chatting da suka yi da Khalil ya rage mata damuwa, A kullum k'ara son Khalil take, tana jin tayi sa'a saboda k'aunar da yake nuna mata.

   Tare suka dawo da Farda, Meenal na zaune a falo, Yayi tamkar bai gan ta ba, "Ya Farda sannu da zuwa", " Yawwa Sister , ke kika b'atawa Yayan naki rai ne yau?", "Eh", "Laifin ki ya shafemu kenan", "Ya Farda kawai fah dan jiya banyi bacci da wuri ba", " A'ah Meenal kin masa wani laifi, rashin bacci bazan sa yayi wannan fushi ba", "Allah Ya Farda shine kawai", " Toh shikenan, kunfi kusa", Ta fad'a ba dan ta yarda ba, Ita kam Meenal har ga Allah ta d'auka hakan.

    A d'aki ta same sa, Daga shi sai singlet da boxer, bata ji komai ba ko tayi tunanin komawa a ganin ta Yayanta ne( Kuskuren da yawa muke yi, ko da yayanki bai kamata ki gansa a haka ba)

   Zubewa tayi gabanshi tare da kama hannun sa tace "Please Yayana am sorry, bazan k'ara ba", Wani yarr yaji, ya janye hannun sa daga rik'on da ta mishi, Yace " It's okay", "Thank You Yayana", Ta fad'a cike da murna, Toilet ya shiga ya watsa ruwa, ta fito falo.

    " Al'ameen sai na aure ka, Son ka yanzu na fara, soyayyar da nake maka ba zata tashi a banza ba", Layla ta fad'a, Tana kallon hoton sa a wayar ta, "Tsawon shekaru na nisanta kaina daga gare ka, Yanzu zan dawo rayuwar ka, duk macen da tace ta rab'e ka Wallahi sai na tarwatsa ta", 

   " Ke dawa kike ta magana", Maman ta tambaya tana shigowa d'akin, "Ba kowa Mummy", " Toh ki fito Daddyn ki na kira", K'aton hijab ta saka, a gaban iyayenta zaka rantse baiwar Allah ce,

     Durk'ushe take gaban Baban ta, "Layla kin gama makaranta, kin fara aiki, abu na gaba shine aure, ya kamata ki fito da miji", " Toh Daddy In shaa Allah ", " Yawwa shine na kira na gaya miki", " Toh",  Ta mik'e ta koma d'aki, A ranta tana ayyana ba da dad'ewa ba zata kawo Al'ameen a matsayin wanda ta tsayar, tasan iyayenta zasu yi murna, suyi alfahari da ita, Kowa a garin yasan waye Al'ameen, Ga iyayen nata da son abun duniya duk da tarin duniya da Allah ya basu.

  Layla ba da good result ta gama makaranta ba, Hanya iyayenta suka mata suka samar mata aiki a wani company.

_Kuyi hak'uri da wannan, sai a slow_

*Follow*
*Vote*
*Like*

*ZEELISH*💕

MEENAL WA LAMEENWhere stories live. Discover now