31

894 58 5
                                    

*MEENAL WA LAMEEN*

*Written 2013*
*Posted 2019*

'''ZEE YABOUR'''
*Follow and vote me on wattpad @ZeeYabour*

'''IN DEDICATION TO'''
*Zakiya Musa Bala*
*Hafsat Salisu*

_*Haske Writers Association*_

*SAKO DAGA KUNGIYAR HASKE WRITERS* *ASSOCIATION💡*

*ZUWAGA DUMBIN MASOYAN MU MUKE SHAIDA MUKU WANI BAKON AL'AMARI DAGA MAHASSADA*, *AKWAI WANI SABON  LITTAFI DA SUKA KIRKIRA ZAKUGA   A SAMANSA AN AMBACI ...BILLY* *GALADANCI (MAGAJIYAR KARUWAI)....TO BA WRITE UP DINMU BANE BA RUBUTUNTA BANE ANYI HAKA NE DOMIN A BA'TA SUNAN TA, SHIYASA MUKA YANKE HUKUNCIN SANAR DAKU DA WURI KAFIN LITTAFIN YA FARA YAWO....*

*31*

   Kiran ta da taji Ummi nayi, Yasa tayi saurin share hawaye ta fita, "Kuka kika yi?" Ummi ta tambaya, Tayi faking smile tace "A'ah fah Ummi, abu ne ya fad'a mun a ido", " OK Sannu, Dama Nusaiba ce ke neman ki", "Tana ina?", " Ta wuce sashen Mami", "OK bari naje na same ta"

    Afra yadda taga rana haka taga dare, Son Al'ameen ya mata kamu, Alla-alla take safiya tayi taje ta tambayi Meenal waye shi, dan maganar bata waya bace.

   "Matar mu" Cewar Nusaiba, Tana dariya tace "Kai Aunty Nussy", " Ai jiya yake sanar dani ance ya turo", Tayi dariya, Mami tace "Allah ya nuna mana lokaci da rai da lafiya", Nusaiba tace " Ameen"

     Goma na safe a gidan su Meenal tama Afra, Ta koma bacci kenan bayan ta had'a ma Al'ameen breakfast ya wuce office, Ta janye bargon data lullub'e dashi tana fad'in "Tashi sarkin bacci", " Ohh my God, wallahi Afra baki yi ba", Ta fad'a tana k'ara jan bargo, "Ki tashi tunda kika ga nazo da safiyar nan ba lafiya ba", Jin haka ta mik'e tana cewa " Me ya faru?"

  "Wani na gani jiya a gidan nan da ya hargitsa mun tunani", Meenal ta kwashe da dariya tace " Allah ya kama ki, anan gidan kuma", "Eh wani dogo, fari kyakkyawa sosai", " Laa Ya Lameen", Afra ta zaro ido tace "Shine Ya Lameen, yaushe ya dawo?", " Ya kwana biyu", "Meenal ki taimake ni wallahi ya tafi da zuciyata, gaba d'aya na kasa sukuni", " Tabb aikuwa kin makaro, yana da mata", Gaban Afra ya fad'i a d'an rud'e tace "Kina nufin yayi aure?", " A'ah ya dai kusa",

Ta sauke ajiyar zuciya tace "Da sauk'i, In shaa Allah dani za'a yi", " Lallai aikuwa da kin cire sa a ran ki tun kafin yayi nisa", "Meenal ban tab'a jin ina son wata halitta kamar shi ba, tsakanin jiya da yau na kasa gane kaina" Ta fad'a fuska d'auke da damuwa, "Babbar magana, ki rok'i Allah ya cire miki son shi kawai", " Toh Meenal, Allah ya yaye mun", "Ameen"

      Iyayen Khalil sun zo dasu goro, sweets, chewing gum da kud'i, An tarbe su cikin mutunci da girmamawa , abinci kala-kala aka musu, Ranar bakin Meenal har kunne.

    "My baby finally we are engaged, can't wait mu zama ma'aurata", Khalil ya fad'a, Tayi murmushi kamar yana ganin ta, Tace " Am so happy dear, bakina ba zai iya furta farin cikin da nake ciki ba Yau, Allah ya nuna mana mun zama ma'aurata", "Amin Babyna", Haka suka cigaba da bayyanawa juna jin dad'in su.

    Farda dake gefe tana jin su, jikinta yayi sanyi, tana ji ina ma haka suke da Al'ameen, Tana addu'ar Allah ya nuna mata ranar da zai nuna kulawa da soyayya a gare ta.

    Tunanin ta ya katse jin k'amshin turaren sa, Ta d'aga kai tana kallon sa, bai lura da ita ba, Hankalin sa na kan Meenal, Zuciyar ta ke harbawa saboda tsananin son sa, Meenal tace " Yayana", Ta katse kiran, Khalil tsaki yaja yasan Yayanta ne yazo shine ta kashe wayar, wani haushi yaji ya kama shi, Yadda take fifita Yayanta akan shi,

   "Dawa kike waya?" Shine tambayar da ya jefo mata, "Ya Khalil", Yaji ran sa ya sosu, ya basar ta hanyar cewa " Muje ki raka ni", "Toh", Yayi gaba ta biyo bayan sa,

MEENAL WA LAMEENWhere stories live. Discover now