*MEENAL WA LAMEEN*
*Written 2013*
*Posted 2019*'''ZEE YABOUR'''
*Follow and vote me on wattpad @ZeeYabour*
'''IN DEDICATION TO'''
*Zakiya Musa Bala*
*Hafsat Salisu*_*Haske Writers Association*_
*30*
"Ki gaggauta fita rayuwar Al'ameen kafin na miki illa" Text d'in ta karanta ta sake karantawa, "Kowaccce wannan bata da hankali, tayi naci bai kula ta ba, shine zata mun barazana", Cewar Farda taja siririn tsaki, Ta kabbara sallah, Dama Sallah zata yi taji k'arar text ta tsaya dubawa.
" Yaran nan ya kamata, iyaye su zauna a saka lokacin bikin su, ba mu bar su suna ta soyayya ba" Bappa ya fad'a, Ummi tace "Hakane, nima naso na maka maganar", " Yau idan sun dawo duka kice ina neman su", "Toh", Suka shiga wata hira.
Meenal na kwance d'akin ta, Tana kallon favorite series d'inta Mehek, Wayarta tayi k'ara, Ganin sunan masoyinta tayi murmushi, Tayi receiving "Hello My baby", " Ba wani my baby ni nayi fushi", Ta fad'a tana turo baki kamar yana ganin ta, "Ohh Am sorry babyna, wlh Mum ta aikeni tun d'azu bank", " Toh na hak'ura tunda Mum ce", Yayi dariya yace "Ya kike?", " Lafiya lau", "Anjima zan zo na ganki", " Allah ya kawo mun kai lafiya", "Amin Babyna", Yayi hanging up, " I Love You Khalil", Ta furta a fili
Kashe kallon tayi, ta nufi kitchen, In less than one hour tayi Shawarma da Milkshake, D'akinta ta koma ta watsa ruwa, ta cancara kwalliya cikin material gown, Tayi kyau sosai, Ganin kiran shi tasan yazo, bata d'auka ba, Ta fito, Kafe ta yayi da ido dan ba k'aramin kyau ta mishi ba, "My baby you are so beautiful", " Kai Ya Khalil" Ta fad'a tana zama kujerar kusa dashi, "Ban tab'a ganin mai kyau irin ki ba", " Uhmm ka dai fad'a dan naji dad'i", "Allah kuwa, Allah ya nuna mun kin zama matata", " Ameen" Ta fad'a ta d'an rufe fuska, "My baby mai kunya", Tayi dariya,
6:00pmAl'ameen ya fito daga office, lokacin tashin shi yayi, PA d'in shi na biye dashi a baya, Rik'e da briefcase, Farda ta fito daga office d'in ta, Yayi tamkar bai san da ita ba, Wanda bai san gidan su d'aya ba, zai rantse bai tab'a sanin ta ba, Ta bishi da kallo a ranta tace " Haka zamu yi zaman aure", Ran ta taji ba dad'i,
Motar shi ya shiga, Driver yaja, Tun a cikin mota ya hango Meenal da Khalil, suna ta hira cikin raha, suna dariya, Take yaji ran sa ya b'aci, Zuciyar sa na gaya masa dashi kad'ai ya cancanta tayi hira da dariya,
A fusace ya fito motar, Driver da bodyguard na mamakin me ya b'atawa ogan nasu rai sun san lafiya suka baro consolio, "Yayana Sannu da zuwa", Wani banzan kallo ya watsa mata ya shige abun sa, Jikinta yayi sanyi kamar zata yi kuka ta kalli Khalil tace " Yayana ya canza mun, a da baya fushi dani, ko wani ya b'ata masa rai, ni baya nuna mun dan kada na shiga damuwa", "Yanzu ai kin girma Meenal dole abubuwa zasu sauya, kiyi hak'uri, kar kisa damuwa kinji, bana son damuwar ki", Tayi murmushin da bai kai zuciya ba tace " Toh, zan shiga gida sai munyi waya",
Bata jira amsar shi ba, Ta wuce ciki, Yabi bayan ta da kallo tare da jin zuciyar shi ta sosu, A fara fuskantar Al'ameen baya son soyayyar su da Meenal, "Idan hakane wallahi bai isa ba, babu Wanda ya isa ya rabani da Meenal sai Allah", Ya fad'a a fili, Rai a b'ace ya bar gidan.
Ba zai iya fassara yadda yake ji a ran sa ba, Zaune yake bakin gado ya rasa meke masa dad'i, tunda ya shigo d'akin ya kasa yin komai, Da sallama ta shigo, " Ya Lameen, Yayana", Ya mata shiru, K'wak'walwar sa na hasko mishi ita da Khalil, Ran sa na k'ara b'aci, Ganin ya mata banza, Ta fad'a jikin sa ta fashe da kuka, Rungumeta yayi yana jin kukan har cikin ran sa, "Kiyi shiru, you are hurting me", Ya fad'a a d'an tsawace, Rage sautin kukan tayi, Ya shiga bubbuga bayanta cikin sigar lallashi, A wani irin yanayi yake jin sa, da ba zai iya fassara shi ba,
YOU ARE READING
MEENAL WA LAMEEN
Romance"A da ina son ka ina k'aunarka ina ganin girman ka , k'imar ka mutuncin ka darajar ka, A yanzu na tsane ka tsana mafi muni, ba wanda na tsani gani kamar ka, ka aikata abunda ko kafiri yayi sai al'umma tayi Allah wadarai dashi, Wallahi Wallahi Wallah...