04

1.1K 108 2
                                    

*MEENAL WA LAMEEN*

*Written 2013*
*Posted 2019*

'''ZEE YABOUR'''
*Follow and vote me on wattpad @ZeeYabour*

'''IN DEDICATION TO'''
*Zakiya Musa Bala*
*Hafsat Salisu*



® _*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*_

*04*

Ummi na rainon Meenal, wacce Al'ameen ya d'auki son duniya ya d'aura a kanta, Da yaji kukan ta zaka ga hankalin shi ya tashi, Ya b'ata fuska kamar zai yi kuka, Idan yana gida toh tana hannun shi har goya ta yake.

Habeeb Allah ya d'aura mishi son Meenal, Addu'ar shi Allah yasa idan ta girma ta k'auna ce shi, Sau da yawa ya kan so d'aukar ta Al'ameen ya hana, Sai yayi murmushi ya k'yale shi, a ran shi yace Watarana zata zama mallakina, ya zama ni kad'ai ke da iko da ita.

Su Mubarak tunda suka tafi school basu dawo gida ba, Bappa ne ya hana musu dawowa yace sai sun kammala, a ganin shi dawowar su hutu zai kawo cikas a karatun su, Ya kan ziyarci su akai-akai, Kuma basu rasa komai na buk'ata ba dan duk wata yana tura musu kud'i.

Meenal ta fara wayo, A ko da yaushe tana hannun Al'ameen, bata yarda da kowa sai shi, sai fah Ummi shima idan yana school, Da ta ganshi zata fara zillo alamar ya d'auke ta, Ga family na tsananin sonta kasancewar ta mace tilo, Bappa ma ya d'auki son duniya ya d'aura a kan ta, A lokacin da ita isa 'yaye tana shekara d'aya da watanni, Yana primary 5, Ya kafe akan shi zai yaye ta.

Ummi tace "Al'ameen ban da abun ka, ina kai ina yaye", Ya had'e rai yace " Ummi kina maida ni yaro, Am a big boy", Ta fashe da dariya tace "Al'ameen ba dai son girma ba, wurin Dada zan kai ta", Duk'awa yayi gabanta ya kama k'afar ta " Ummi please please please", "Tashi zan bar maka ita", Tsalle yayi ya rungume ta tare da manna mata kiss.

Meenal ta koma kwana d'akin Al'ameen, A k'irjin shi yake sata, bata minti biyu take bacci, Abinci a baki yake bata, kulawa ta musamman yake ba Meenal, wanda hakan ya k'ara so da shak'uwa tsakanin su,

Ya shirya cikin uniform zai tafi school, Ya d'auko ta a kafad'a tana bacci ya kai ta d'akin Ummi, Yana ajiyeta ta bud'e ido, Ta mik'o hannu alamar ya d'auketa, D'aukar ta yayi ya kai ta falon wurin Ummi, Har ya kai bakin k'ofa yaji ta tsandala ihu, Ya dawo a guje ya d'auke ta,

Ya shiga share mata hawaye yace " Am sorry my little sis, bana son kukan ki", Aikam tayi shiru tare da kwantar da kan ta jikin shi, Yana shafa bayan ta, Ummi ta kalli Habeeb dake zaune kan Dining table yana breakfast, WAEC suke bashi da paper so ba za shi school ba tace "Karb'e ta hannun shi, ya wuce school"

Yana tab'a ta, ta shafe da kuka, Al'ameen kamar mai shirin kuka yace "Ummi ba zan je school ba", Cikin fad'a tace " Mik'a mishi ita ka wuce, kafin ran ka ya b'aci", Haka ya mik'a mishi ita tana kuka, Shima ya fita yana hawaye, Zuciyar shi na tafarfasa, Ya buga k'ofar falon da k'arfi.

Ummi da Habeeb ba irin lallashin da basu mata ba tak'i shiru, Ummi taji dama ta bar shi ya zauna, Dabara ta fad'uwa Habeeb, Yayi searching hoton Al'ameen a wayar shi, Ya nuna mata, Ta fisgi wayar tana nuna shi, Sai dariya, Ummi mamaki ya cika ta, ta tsaya kallon ta.

Habeeb yace "Ummi ya kamata ki rage kusancin Al'ameen da Meenal saboda gaba", Ummi tayi murmushi tace " Kana tsoro ne nan gaba tak'i zama gidan ka tace sai da Al'ameen, ka kwantar da hankalin ka yanzu hadda yarin ta" Yayi murmushi yace "Toh Ummi", Yaji natsuwa dan fargabar shi kenan.

A school ba wanda ya ma magana, Kan shi ya d'aura kan desk yana hucin zuciya, Duk teacher da ya mishi magana, baya d'aga kai ya kalle shi.

Last period, Mathematics teacher ya shigo, he is very strict,

" Aminu Get up", Teacher ya fad'a a tsawace, Al'ameen ko gezau bai yi ba, A fusace teacher ya k'ara cewa "Are you deaf? I said get up", Ya sake yin banza, Ya k'arasa seat d'in shi, Ruler dake hannun shi ya shiga buga mishi a baya, har ta karye a bai motsa ba,

Teacher ya tsorata da al'amarin Al'ameen, Ya k'yale shi ya cigaba da teaching.

Shatin bulala ne gaba d'aya a bayan shi, Yana mishi rad'adi sosai, A gida bai sanar da kowa ba, Meenal kawai ya d'auka yayi d'akin shi da ita, Ya zaunar da ita kan gado, Ya canza kaya ya fesa turare, Al'ameen gashi yaro amma sai son gayu da turare, Abubuwa yake tamkar babba.

A tare suka ci abinchi yana bata a baki, in dai ba Al'ameen ya bata ba toh bata ci, Suna gama ci, Ta fara nuna mishi baya alamun ya goya ta, Ba musu ya d'auke ta ya goya, Duk da rad'adin zafi da yake ji bai sauke ta ba sai da tayi bacci, A k'irjin shi ya sata, Ya sumbace ta, Shima a haka bacci ya d'auke shi, Ummi ta lek'o ta gan su, Tayi murmushi tace "Allah ya raya mun ku yarana"



*Vote*
*Comments*
*Follow*




*ZEELISH*💞

MEENAL WA LAMEENWhere stories live. Discover now