55

1.2K 88 5
                                    

*MEENAL WA LAMEEN*

*Written 2013*
*Posted 2019*

'''ZEE YABOUR'''
*Follow and vote me on wattpad @ZeeYabour*

'''IN DEDICATION TO'''
*Zakiya Musa Bala*
*Hafsat Salisu*

*_Haske Writers Association_*

*55*

     _*This page is for you Ayshafareeda and Aysha Kanya(Pherty Novels*__

    Meenal taso yi musu girki ya hanata, Ya fita ya siyo musu shawarma dama akwai lemo a gida, Suka kora dashi, A tare suka kwanta manne da juna, Bacci ya kasa d'aukar kowannen su, duk da cewa idon su a rufe yake, Tunanin Farda da kyawawan halin ta yake, yana jin muguwar tsanar su Layla na shigar sa, Ba zai tausaya musu ko kad'an ba.

     Meenal ma tunanin Farda take, yayin da take mata addu'o'i, Ko ba komai rik'e Haidar da tayi tamkar dan' ta haifa, ba zata tab'a mantawa da ita ba, "Farda mutuniyar kirki", Ta fad'a a ranta.

     Kiran sallar asuba yasa kowannen su mik'ewa, Da mamaki yadda lokaci yayi sauri,

    Al'ameen ya shiga toilet na d'akin, Meenal fita tayi ta koma d'ayan d'akin ta kwanta, Bacci ne mai nauyi ya d'auke ta.

    Ya lek'o yaga tana bacci, Ya koma d'akin sa, Yana shirin yadda za'a kama su Layla.

      Hasken rana da ya dallo d'akin ya haske ta, Yasa ta farka, Ta karanta addu'ar tashi daga bacci, Toilet ta shiga tayi wanka, Bata yi wani shiri ba, doguwar riga ta saka, Mutuwar Farda har yanzu bata sake ta ba.

   Kitchen ta shiga, Akwai bread, tayi sandwich ta had'a kayan tea, Ta nufi sashen Al'ameen, Ta jera kan dining table,

    A bakin k'ofar d'akin shi suka yi kaura, Taja baya tace " Ina kwana?", "Lafiya lau, kin tashi lafiya?", " Lafiya lau", "Ke zan je tadawa nace ki shirya mu tafi", Tayi murmushi tace " Na tashi, ga breakfast d'in ka can", Yace "Toh", Dan kar taji ba dad'i, but sam baya jin cin komai.

     Tea yasha, sai sandwich da yaci rabi, bata tilasta mishi k'ara ci ba, Tasan tension da yake ciki, Bashi da natsuwa sai yaga an kama su Layla, da rad'ad'in mutuwar Farda da yake ciki.

    Hijab ta saka wanda ya saukar mata zuwa gwiwa, Al'ameen ke driving tana gefe, Hanyar gidan su Layla taga ya nufa, ba tace komai ba, Har suka kawo bakin gidan, Ya kalleta yace " Ki shiga ciki, kice takardu kika kawo mata, sai ki duba kamar zaki d'auko, kice kin manta su a gida, tazo kuje ku karb'a", Ta amsa da "Toh"

    Layla da murna ta tarbi Meenal, tasan takardu ta kawo mata, Yau suka yanke suna karb'a, su aika a kashe Al'ameen, su gudu su bar k'asar,

     "Yau na cika alk'awari", Meenal ta fad'a, Tana k'ok'arin bud'e jaka, " Laaah! Na manta su gida kan gado, ashe da na d'auko ban sa a jaka ba", Take far'ar kan fuskar Layla ta d'auke, Tace "Sai ki koma ki d'auka", " A'ah wahalar zata mun yawa kuma Al'ameen zai iya ganewa, kizo muje dai ki karb'a", Cike da gamsuwa tace "Toh", Ta jawo mayafin dake gefenta, ta yafa tace " Mu tafi"

    Ta cikin mota yake hango su, Yana cije baki, Layla bata ga wanda ke ciki ba, Kasancewar glass d'in tented ne.

   "Tare da Yayana nake, ki shiga baya koh", Ba musu ta shiga, Meenal ta shiga gaba, Tana shiga yasa lock, " Sannu ko" , Kai ya d'aga mata, Ya fara driving, Sam bata gane shi ba, dan bai juyo ba, "K'arshen Al'ameen ya kusa zuwa, har na k'osa naga idon shege ya waiga yaga komai da ya mallaka ya zama ba na shi ba", Meenal dariya tayi tace " Ke dai bari"

   Bai zarce ko'ina ba sai police station, "Me ya kawo mu......", Harshen ta ne ya sark'e, cikinta ya murd'a ganin Al'ameen na jefan ta da wani matsiyacin kallo,

MEENAL WA LAMEENWhere stories live. Discover now