57

2.1K 124 23
                                    

*MEENAL WA LAMEEN*

*Written 2013*
*Posted 2019*

'''ZEE YABOUR'''
*Follow and vote me on wattpad @ZeeYabour*

'''IN DEDICATION TO'''
*Zakiya Musa Bala*
*Hafsat Salisu*

*_Haske Writers Association_*

*57*
*Unedited*

   Bayan ya dawo sallar magrib, a masallaci sosai yayi ma Farda addu'a, tare da addu'ar Allah ya mantar da Meenal komai, Yasa ta bashi had'in kai,

Ya lek'a d'akin ta, Ta matse gefe d'aya tana bacci, fuskar ta tayi jajir saboda kuka, Tausayin ta yaji na ratsa shi, K'arasawa yayi ciki, Ya gyara mata kwanciya, Ya kwanta gefen ta, tare da rungumo ta jikin shi, A haka bacci ya d'auke shi.

    Around 10:00pm ita ta fara farkawa,  Idonta ta sauke kan fuskar shi, Son shi da k'aunar shi taji na ratsa ta, Maimakon ta tashi, sai ta k'ara rungume shi, Tana shak'ar daddad'an turaren shi, A hankali ya fara alamun tashi, Bata sake shi ba, Idon shi ya bud'e cikin nata, Bata kawar da kan ta.

   K'aunar junan su ke fisgar su tana k'ara jefa su a wani yanayi, A hankali ta furta "Am sorry da abunda ya faru d'azu", " Ba komai My darling, banga laifin ki ba", Kiss yaji ta manna mishi a goshi, Shima ya manna mata, Yace "Tashi muyi sallah"

    Shi ya fara sauka kan gadon, Ya d'auke ta ya kai toilet, Tana dariya, A tare suka yi alwala suka fito, Shi yaja su sallah, Bayan sun idar suka yi addu'o'i, Suka yi shirin bacci.

     A daren Meenal ta murzu wurin Al'ameen, ta bashi had'in kai, amma kuma ta wahala, Dan bai mata da sauk'i ba, Sun nuna ma juna soyayya a daren.

     Da asuba, a tare suka yi wanka, Suka yi sallah, Suka koma bacci, Sabuwar soyayyar ta ke k'ara shigar ta, Zuciyar sa har zafi take saboda tsananin k'auna, Itama Meenal hakan ne dan tana jin bata tab'a son wata halitta kamar sa ba.

  Basu farka ba sai 11 saura na safe, Al'ameen ya fara shiga toilet, Yayi brush, Ya tara ruwa a bathtub, "My darling", Ya k'wala kiran ta, Tana shigowa, ya jawo ta ciki, tare da flinging da towel na jikin ta, A tare suka yi wankan bayan sun gama jagwalgwala juna da wasannin su.

    A babban towel d'aya suka rufo jikin su, babu yadda bata yi dashi ba ya bari ta d'aura nata daban yak'i, Shirin ma a tare suka yi, Shi ya mata cream, Itama ta shafa mishi.

    Suka yi shiga cikin English wears, Wando da riga ta saka, da suka kamata suka fito da shape d'in ta, Sun matuk'ar yi mata kyau, Yana ta kallon ta yana yaba kyan da tayi, A tare suka had'a breakfast, Suka ci, bayan sun gama, Suka dasa sabuwar soyayya.

    Meenal ta kafe sai ya goyata, Ya duk'a ta hau baya, Yai ta zagaye falon da ita, haka ya tuna musu yarintar su.

         *Bayan sati d'aya*
_Gidan yari_

  Hayaniya da ihu ke tashi daga wani d'aki a gefen maza, Securities ne suka zo ganin me ke faruwa, K'attin maza masu ji da k'arfi su biyu ne ke jibgar Mahfuz kamar sun samu jaki, Security ne suka shiga tsakanin su, Suna tambayar su me ya faru, Wani a d'akin ke fad'in d'ibar ruwa suka aike shi yak'i zuwa, Securities kansu tsoron shaid'anci suke na (Victor da Ola), ba k'aramin criminals bane, a gidan yari basu natsu ba, Kowa tsoron su yake, Mahfuz suka yi mari biyu, Suka ce kuma daga yau ya rik'a bin duk abunda suka ce, Ya amsa da "Toh", Dukan da suka mishi yasa masifar tsoron su yake ji, Ya rame yayi bak'i, kamar wanda yayi shekaru a gidan yarin ba sati d'aya ba, Yana cike da tsantsar nadama, ina ma da bai sakawa kanshi hassada da kwad'ayi ba, Da yanzu yana can cikin rufin asirin shi.

    Layla ta b'angaren ta, itama matan d'akin su na azabtar da ita, Ita ke musu wanki, idan ta karb'u abinci, su k'wace su bata d'an kad'an, Duk ta rame tayi bak'i, K'afarta kullum k'ara rub'ewa take, Ance yankewa za'a yi, Bata da aiki sai kuka, da nadamar abubuwan da ta aikata.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Oct 08, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MEENAL WA LAMEENWhere stories live. Discover now