43

958 74 2
                                    

*MEENAL WA LAMEEN*

*Written 2013*
*Posted 2019*

'''ZEE YABOUR'''
*Follow and vote me on wattpad @ZeeYabour*

'''IN DEDICATION TO'''
*Zakiya Musa Bala*
*Hafsat Salisu*

_*Haske Writers Association*_

*43*

  *@Oum Rukayyat⁩ @⁨Hurril'ai⁩ @⁨Oum Sadeeq⁩@⁨Fatima Auwal Mannir⁩ @⁨Nabeela Y Jalo⁩ @⁨Beentu Abdallah🥰⁩ @⁨Hussylurv⁩ @⁨💞hafsat aminu💞⁩ @⁨jidda h garba⁩  @⁨khadijasulymanhalliru⁩@⁨Ummu Zarah🧕🏼⁩ @⁨Xainab Ibrahim Ameen⁩ @Ummu Nabeel⁩ @Mom Sayyeed&Noor⁩ @⁨Fatima Auwal Mannir⁩  Da duka sauran Yan KUNDIN HASKE NOVELS wannan shafin naku ne💕💕💕💕*

   Ummi bata bar d'akin Meenal ba sai da ta tabbatar tayi bacci, Ta koma d'akin ta cike da tausayin yar' ta, Babu wanda ya dace da ita sai Al'ameen, damuwar da zata tsinci kanta shine matsala,

    Bata waiwayi Bappa ba, ranar kwanan Mami ne, Sai faman juyi yake a gado, Tunani fal a ransa, Mami ta tambaye shi, meke damun shi, Yace ba komai, Tayi shiru ne ba dan ta yarda ba, but tana mishi addu'a, Allah ya yaye mishi damuwar shi.

      Duk bayan kwana biyu, Al'ameen sai ya kira Daddy da Aunty ya gaishe su, Suyi ta sa mishi albarka, Twins sunyi girma sosai, Suna kiran shi video call, su sha hira, Yana k'aunar su.

    Yau kwana biyu, Ummi bata samu sararin magana da Bappa ba, Ba kwanakin ta bane kuma bai zauna gida ba,

    Meenal kullum k'ara narkewa take bata da lafiya, Afra tazo duba ta, Ta kalle ta tace "Anya k'awata wannan ciwon nasan fah halin ki", Ta tuntsire da dariya tace " Ke wallahi ba wani ciwon zuciya, na had'a baki da Dr ne, dan a fasa aurena da Al'ameen, na auri Ya Khalil", "Lallai K'anwata, amma kina ganin hakan zaki yi nasara?", " Sosai kuwa, dan naga tashin hankali a tattare dasu Ummi"

    Ummi tazo bata magani, taji suna wannan maganar, Mamaki ne ya cikata, Ranta ya masifar b'aci, K'ofar d'akin ta tura ta shiga, Kallon da taga Ummi na mata yasa ta tsorata,

    Cikin d'aga murya Ummi tace "Wato abunda kika shirya kenan ko, meyasa baki da tawakkali, Toh wallahi ki sani auren ki da Al'ameen babu fashi", Jikinta ne ya hau kyarma, Zata yi magana, Ummi ta daka mata tsawa ta hanyar cewa " Kada na sake naji wata magana daga gare ki", Ta fice rai a b'ace,

   Hannu ta d'aura a kai tace "Na Shiva uku na", Ta saki kuka mai cike da k'unar zuciya, " Kiyi hak'uri Meenal, ki manta da komai",  Bata saurari Afra ba ta cigaba da kuka.

    A daren Ummi ta sanar da Bappa shirin Meenal, Ran sa ya matuk'ar b'aci, Yace "Aminatu tazo mana da rainin wayo, Amma Alhamdulillah tunda mun gane gaskiya, auren su na nan akan lokacin da na d'iba", " Allah ya nuna mana", "Amin"

     Ya kira Dr Yusuf, ya mishi tass, yana ta bada hak'uri da cewa tausayin ta yaji.

    Meenal ta sawa kanta damuwa duk ta rame, Ummi tayi lallashin ta da mata nasiha, ta gaji tasa mata ido, Tana ta shirye shiryen biki, though ba shagali za'a yi ba, D'aurin aure ne sai yinin biki.

      Al'ameen da kansa ya had'a lefe, Kayan duka daga Dubai yayo order su, Farda kad'ai sai driver yasa suka kai lefen, Su Ummi sunyi mamakin ganin lefe basu d'auka zai yi ba, Akwati 12 kaya tsadaddu ne, babu na banza.

    Meenal kayan ko kallo basu ishe ta ba, A ranta tace wato shi shirin aure ne ma yake hadda yin lefe, Wallahi sai ya gwammace mutuwar sa akan aure na.

     Bincike take masa a office tana neman wasu takardu, Idon ta ya kai kan invitation card, Sunan da ta gani a jiki, Ya sanya ta cikin rud'u, Al'ameen zai auri Meenal, "How is that possible, k'anwar sa Uwa d'aya uba d'aya, Noo bata gani daidai ba", Ta k'ara kallon IV taga sunayen su, Jin fitowar sa daga band'aki, Tayi saurin gyarawa,

MEENAL WA LAMEENWhere stories live. Discover now