page13

5.1K 472 2
                                    

*🍒🌺AJALIN SO🌺🍒*
      _XPLICIT ROMANCE_

*WHATPAD SURAYYAHMS*
Dedicated to umherny nersallah

_PAGE 13_

Wasa wasa sai gashi Har banafsha ta samu hutu..
Da shike yanzu hjy mahnoor tana nan sai bata cika damuwa ba ko ya zo yafi spending time dinsa da ammyn sa.

Itama yanzu takan yi waya da chats sosai da su maryam so bata damu ba...

After 1monthz chas aka soma shirin komawa schl nusaiba ce ta fara komawa sabida hutun ta sati 3 ne kacal kum akai banbancin tsari da nasu banafsha sosai

Bangaren mohan kuwa yanzu gaba daya hankalin sa nakan wata project daya sa gaba ya ke yi sabida ya samu yakai inda yake so arayuwan sa
so yake kafin ya cika 30years a duniya ya mallake taken special cadio surgeon bai damu ba ko da za'ace nawaa zai kashe in har zai dawo hakan

Babban Dream dinsa ne yaga yayi aiki a zuciyan mutum kuma ya tashi,..

Ance aikin sai mai tsananin nitsuwa da extra ordinary talents gani yake tunda he's perfect with medicine yanzu kamar tanan kadai ya rage masa ya baje baiwar da Allah ya basa.

Meetings akan meetings duk ya bada time dinsa kai yana neman aproval daga kasar russia ind ayake so yaje yayi karatun

Yanzu haka sunce zasu turo masa da supervisors
Don haka kullum bai samun time din zama yana nan yana komarim hada presantation din da zai baje musu asamu ayi aproving masa sai ya samu gurbi mai kyau daga tushen abun..

Bangaren nimrah kuwa,da shike komai na tafiya mata normal yanzu haka shiri take zata bi hjy mahnoor dubai zasu je wani babban fashion show business

Dan zuwan gidan datayi wata rana sai da ta hada makirci aka karbe waya gaba daya daga hannun banafsha..

Ita dai da siyasa ta zuga hjy mahnoor akan idan banafsha tana yawan rike waya wata rana zata ce zata karbe number saurayi gata da aure kuma ai karamar yarinya ne bazatayi wani wayo ba

Cewar ta ai ba mutuncin su bane haka besides yanzu dole asama banafsha ido sabida tasan darajan igiyan dake kanta

Babu wanda yasan nimrah ce ta hade wayannan maganganu da shike hjy mahnoor tana ganin kamar nimrah ta dauke ta uwa me shiyasa take fada mata hakan sai ta amince da zancen 100percent

Da kyar hjy mamah ta rararrashe banafshan ta da sharadin idan tayi behaving zata sa a bata wayar ta ta cigaba da using..
Sumfi karfin ta anan sabida itama banafshan tunda ta samu sabbin kawayen nan kullum tana jikin wayar tana chats ko calls..

Ba karamin dariya kuwa nusaiba tayi mata ba,ita kam ba ruwan ta sai yadda taga dama take yi ma da wayan ta..

Haka banafshan tayi hakuri ba don ta so ba,
Duk sai taji ta takura
Auren ga yadda akayi maya shi,makaranta ma haka wai ace wayar ta ma an kwace duk sabida abu daya .she was feeling sad tasan kawayen ta sun neme ta kwana biyu basu same ta..
Washe garin da su hjy mahnoor da nimrah suka tafii dubai ranar banafsha ta fara zuwa makaranta

In kagan su da su maryam kamar zasu hadiye kansu as expected dik su na tambaye ta rashin hawa online da amsa calls...tace kuyi hakuri hjy mamah ne ta karbe waya na amma tace zata bani..

Hakan ya sa fazila ya shiga quesing dalilin tace ko akaan saurayi? Tayi mirmushi tace noo way nima bansani ba maye akna karatu ne
Cewa tayi banyi kokri last term sosai ba sai ma dage wannan karon.

Maryam tace ahhhh a hakan u came 5th kar ko manta 2 weeks to exams fa kika zo shine bakiyi kokarin ba? ta dan tabe baki daya ke bata son acika magana akanta sai tace just forget it,..ina muka tsaya da maganan mu..
Nan hira ya fara zafi har suka mance da kansu sai dariya suke kamar basu da damuwa..

Tafiyar su  nimrah da sati biyu hjy mamah ta soma shiga damuwa,
Babu attention din kowa yanzu a kusa da ita

Ga wani dan banzan habits din banafsha ta soma bata dawowa on time wani bin sai sun kai past 2 haka driver zaiyi ta jiran su suna shagalin su a schl park..
Anan maryam ke musu labarin kaya kala kala na mata tana nuna musu awayr ta suna hirar akai.

Sosai banafsha take son ta gwada siyan turarukan humrah da sauran su sabida yadda taga maryam na maganan i gancin su it will be worth it ita damadaga niger ake kawo musu irin wannan idan hajy mamah ta aika an taho da shi daga wajen hjyn birni...

To sai takejin ta gaji da qamshin su tana so ta sauya tsari makanta sai dai tana tsoron binsu su tafi gidan tare.

Tasan idan sukaje zasu dade hjy mamah yanzu ita kadai ne nusaiba ba saukowa take ba ga mohan is very busy..

Duk abun duniya ya dame ta kadaici da kewar mutanen gidan sai yafara nunawa a fuskan ta tin ba aje ko ina ba.

Yau jumu'ah ne don haka jumfa ya sakayawa wa jikin sa light brown,he looks so fresh hakan ya dada bayyana stress din dayake dauke da jikin sa..
Yana saukowa daga masallci Hanyar asibiti ya dosa tare dA ciro Wayar sa a aljihu..

Tana daukawa tace alhmdullh..
Ya dan yi ajiyam zuviuan jin muryan nata yace hjy mamah ina fata lpya ko?
Naga kirar ki ina msallaci ne..

Da har zatayi masa yar yadda suka saba na masifa amma sai ta fasa ta sauke kai cikin sanyin murya tace ka damu dani ne kake tambya ta ai zuwa kake kawai kayi baccin ka ka fice agidan tamkat bani da gurbi arayin ka..

Yayi murmushi kamar wanda yake magana ma budurwan sa yace meye kawo wannan maganan kuma...

Tace ai gaskiya na fadi,rabon ka da kazo na zauna naganka ai sai dai din kazo zaman auren dole da ya rataya awuyan naka
Nasan da babi shi bazan taba ganin ka...yace wait wai gani na kike so kiyi ne..yayi dan dariya ..yace toh fada min time din Da kike so na zo zan zo ma zauna miiko hjy mamaj na...

Kamar ya tsoma ta. Aljanna haka taji sanyi aranta tace yau nake so ai kazo min yammacin jumma'ah ko,
Batare da bata lokaci ba yace done...nan ya katse wayar sa shikadai yana murmushin sa sabida yasan aduniya tana daya daga cikin mutane mafi daraja a zuciyar sa...

Da ya kanyi tunanin mahaifiyar sa...hjy mamah da ayshan shi
Amma yanzu kwata kwata sai gashi ya dena kawo aisha sabida yana lumshe idanu ba abunda take dawo masa da shi sai fuskan banafsha...

Ko dan yanayin jikin su iri daya yake confusing kansa ya kasa ganewa
Shiyasa ma kawai ya dena kawo tunanin ta aransa kwata kwata ..

Da shike yau din yana mugun jin saukin aikin sa sai ya dawo gidan da wuri
Jin muryan sa a falou da hjy mama yasa daga banafshan har nusaiba babu wacce ta leko

Anan itama tayi kokari ya cinye sa da baki har ya amince zai dawo zama sa su
Damuwar ta wayake kuka da shi tunda nimrah tabi sawun mahaifiyar sa acewar ta ai gwara ma yana zaman sa nan din kawai tana ganin sa tana jin dadi maran ta..

Bai so ba amma ganim yadda hjy mamah yau ta sauke kai tana lalaba sa da kalaman kewa da son taji shi akusa sa itan yasa ya amince zai sawo nan da zama na dan lokavi kafin nimrah  da ammyn sa ta dawo.

Haka suma zauna suna hira kadan kadan ta lura sam baiso akawo amsa magana banafsha shi
cewa ma yayi tana raini sa.
Ita kam hjy mamah tasan mai iya masa sai Allah sai bata dauko maganan nasa serious ba...har aka kira magrib ya tashi ya fita masallaci bai dawo na sai da aka cimma ishai
Follow surayyahms and vote

AJALIN SOWhere stories live. Discover now