medicine

11K 718 96
                                    

*🍒🌺AJALIN SO🍒🌺*

_WATTPAD SURAYYAHMS_

Brilliant writers association

_50 medicine_

Tun daga fitar ta ta kira layin maryam tace mata tana nan A hanyar zuwa maryam Tace Toh Kizo gidan ummah Kawai ina wajen

Nan Din ta wuce  driver ya aje ta,
Bakowa harabar gidan Sai ta shigo Falo da sallamar ta,Maryam din ne a zaune Ganin ta yasa ta mike da fara'a tana cewa maraba Da xuwa, ta bata wajen zama
..gidan shiru kamar ba kowa sai su biyun...aje maysam Banafsha tayi gefe tana sauke boyayyen ajiyan zuciya Don har wani iska na daban ta ke ji naratsa ta

Maryam tace kaga amaryan doc hjy Banafsha...,sai wani pale pale kike kinyi haske, Banafsha anya ba wani katon kwallon kika chabe ba?

Murmurshi kawai tayi tace wannan ai sai ku yaushe zan iya mantawa da azaban danaci a nakuda?

,. . yah Yaya ameer ango na Fatan kuna lpya?

maryam Tayi Murmushi tace lpya Lau fatan dai zaki zo min, dan nan dai ba gida na bane.....sukayi dariya Banafsha tace Ke kadai ce?naga bakowa Inche Lpy?

..tace eh fa daga shiga kitchen nafito sai banga ummah ba,bari dai na duba mana abincin sai naxo..

Sai Ta gyada mata kai,bby maysam ke Neman fara kuka sai ta dago ta ta aje ta kan cinya tana bata nono

,...yadda yarinyar tayi shiru ta nitsu tana tsotsar ta sai ya sa takafe ta da ido tana ganin kamannin mijin ta,.ranar ma tanaji hajy na fada cewa mohan bai wani sha nonon uwa ba sabida hjy mahnoor ba ita ta raine shi ba
...tace hjy mahnoor ta samu cikin shi ne a lokacin da take kokarin fara kafa career ta na fashion and desing a duniya kuma tana so yayi karfi sai kawai ta fi bada muhimmanci achan fiye da shi.

Sometimes idan hjy na bada labarin yarantar sa har abun dariya yake bata,yanzun ma wani abun ta tuno zatayi dariyan amma saiga hawaye sun sako mata

...wani mugun mugun son mijin ta da kewar sa ke neman mata illah,'dan kadan tahade goshin ta dana maysam tana kallon kamannin sa anan tana kukan zuci.

Maryam Tray din hannun ta ta aje Ra karaso kusa kanta tace Banafsha?...
Bata ma ji ma ta kuma cewa
nafsha... adan firgit ta dago cikin sauri Ta kuma sadda kai tana goge hawayen ta

..maryam da shiKe ta dade tsaye kusa da bayan ta tana kallon abunda take tuntini tuni ta karbe baby ta ajiye gefe ta Dawo ta tsuguno gaban ta

tace Banafsha lpya kuwa,meya sameki kike kuka? Bata  Amsa ba Tayi shiru...ko maysam ne bata da lpya Kin  fada ma doc?what's going on....

Da maryam ke tambayar ta A haka sai taji She cudnt hold it anymore,wani matsanancin kuka ta fashe da shi tana cewa babu komai kawai wani abu nake tunawa..sai kuma tayi shiru Ta cigaba
..hankalin maryam Kuwa tuni ya tashi,but she's very tactfull dan haka ta nitsu ta riko hannun Banafshan gently Tace kawata"..kar kice min iyayen ki kike tunawa...ko su hjy sun bata miki rai ne?...Tayi saurin girgiza kai

tace ah'a Maryam...tun daga nan bata Sake cewa komai sai kuka...

Gefe da ita maryam ta Dawo zauna ta jawo ta jikin ta Tafara rarrashin ta,Maryam duk wani kalma na hakuri ta fada mata da kyar ta dago Ta hadiye kukan tace Mata maryam Im not happy....my marriage,... ni bansan ya zanyi Da shi ba,It s alwys hurting Me..what shud i do pls..?

sosai maryam ta shiga halin tausayin ta Data ganta a hakan ayanda suke rike da amincin junan su itama tuni ruwan hawaye ya taro a idanun ta,tace Banafsha dama yaya mohan ne?Kar kice mun fada kikayi da shi,Pls talk to me Nasan ki da boye damuwa Aranki,Kuma ba yadda xaki rike abu aranki ki samu saukin shi...pls whats wrong?meya faru ne nafsha kefa ta Yaya Mohan ne shi kadai, shima naki ne ke kadai.

AJALIN SOTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang