*🍒🌺AJALIN SO🌺🍒*
_XPLICIT ROMANCE_*WHATPAD SURAYYAHMS*
Dedicated to umherny nersallah_PAGE24_
A lokacin ana neman karfe 12 na rana don haka ko ina ya dauka da shiru musamman ma da mohan ya fice wajen aikin sa.
Nan Nimrah ta shigo a raunane ta kare ma gidan kallo ko ina tsaf alaman mayyar yarinyar har ta fito ta kimtsa inda suka bata
Tabe baki tayi tana yatsine ita damuwar kishin ne tukurum a gaban ta bata ma tunanin wani abu na rayuwan ta a yanzu
A hakan ta haura sama,da sake sake aranta wani bin sai tace ko tabi shawaran mum din ta ne kawai ta bi abun a hankali..
Amma noo ta sa abun sosai a brain din ta gani take har uwartan ma bata san zafin kishi bane. Ko ace akawo maka karamar yarinya kishiya ba shiyasa take fadan haka..
Tsaf ta gama shirya mugun tar ta taso tayi wanda zai sa banafshan ta rikice ta dena samun karrfin gwiwar magana kwata kwata agidan daga yau Sai dai kashh wani muhimmin meeting
Ya daga ta dan dole ta hakura ta fice.Ita kuwa banafshan tana nan kwance tana latsa wayar ta,sama sama take chats inda su mufidah suke mata albishir din dawowan su akan zasu zo mata washe gari
Zuwan sun ma ya dada hana qudirin nimrah wanzuwa..
Ta tsani taga banafshan tana cikin annashuwa da kwanciyar hankali..A duk dama jiyan mohan bai wani zauna ba amma sosai ranta ya harzuka ya dada baci musamman da taga sun ware ta sun dauki junan su kamar yan uwan jini na asali.
Babu irin labarin da basu bata ba,musamman mufidan dake kokarin bata shawarn yadda zata rage zaman kadaici kafin su bar gidan haujar nimrah saura kadan ya kunce don kuwa kulle kanta tayi a daki tana maganganu..
Don ranta ace kowa a duniya ya tsani mohan baya da relationshp da kuwa sai ita kadai amma abubuwa sai dada lalacewa suke.
Ba wanda kuma take bada laifin hakan akai sai banafsha..
Da wasa da wasa har banafsha tayi sati biyu tana neman na uku,
Akallah yau sunyi waya sau biyu da anty rawiyah
Itake sake tunatar mata da nauyin aure dake kanta sometimes ko da abu ya faru idan ta tuno da maganan ta sai taji karfin giwa ya rufe ta.Don yanzu kwata kwata ta hana ta fitowa inda nimrah take bare su hadu..
Gashi mohan ya tafi kasar hawaiii medical assist awani babban asibitin kasar,yau satin sa guda amma bata taba bari sun goga da nimrah ba.Itama ta nemi hanya har ta gaji,ko tazo da masifan dakin ta kullum a kulle take ji gam...gashi tana tsoron ta bunka mata wuta ta kona ta ko zata mutu ace ma gobara ne kamar yadda tasha kokarin yi amma ta kasa aikatawa..
Ita kuwa banafshan bata ma takan ta,tunda ya tafii sau biyu ya neme ta yanzun haushi ma take ji da ya kira ta na musamman don ya sata girkin tarban sa gobe da yake shirin dawowa
Wani bin idan yana magana kamar ba shi ba,yaushe ya saba cin abincin ta da zai sata aikin yi masa wannan karon..
Abun ya kan bata mamaki amma wa washe garin haka ta mike sai daf yana shirin dawowa ta fara hada masa simple african dish
Vegies da crispy cocunt rice wanda yaji bushahen kifi tayi ta hade da fresh pineaple and cocunut juice
Da shike ma akwai garin daka na mata mai kyau da aka hada mata take sha sai bata damu tayi tasting baDama yace mata da misalin bayan la'asar zai iso Nimrah bata nan dan haka tana gamaawa ta wuce dakin ta ta dan watsa ruwa ta fito tana shiryawa.
Colourles chappette mai qamshin beries ta goga ma lips din ta sakaya
Flair gown Violet Bowel tsadadde wanda yaji adon zaren hannu da wuya yau kam bata fetsa turare ba kayan humrahn nata kawai ta gwamusa masu sanyin qamshi da dadi tayi ras akan kujeran dakin ta tana chats...
