brainwashed

9.7K 702 48
                                        

*🌺🍒AJALIN SO🌺🍒*

WATTPAD SURAYYAHMS

47
_Brainwashed_

Mohan sai da ya gama dariyar sa sannan ya dago ya kalle ta"sharrin shedan ko? Hmm ai sai kije ki fada mata..Sai ya Kuma Ya hade rai

Durkushewa gaban sa tayi A hankali ta ke share hawayen tsoron dake tahowa dakan su a fuskan ta"

Cikin ranta tana tunani ya xatayi ta bada Nimrah hakuri'

Ganin ya mike ya bude kofar zai fita ta taso itama ta biyo bayan sa

Dakin nimrah ya nifa ya turo kofar ya Tsaya kallon ta,

zaune take akan gado ta cika fam tana karkada kafa,yace wai fushi kikayi?Wani wawan hararar ta juyo ta balla masa

...Tabe baki yayi dariyar ta nacin Sa arai Amma sai ya make

,Nan ya juyo ya kalle banafsha dake boye abayan sa yace ohh baxaki bata hakurin ba?

Banafsha kamar wacce xata yi kuka ta fito tace"anty dan Allah kiyi hakuri nifa bada ke nake dariyar ba"

Wani shiru wajen ya dauka dama ita nimrah bata san da shigowar ta ba.
Ganin sun hada ido
juya kansa yayi gefe don kuwa
Dariyar su yake ji har ransa, irin ok ba ma ita kike dariyar ba ma aljanun abinci ne ko?

A firgit nimrah ta mike tsaye cikin fusata tace,ohh biyo ni ki kayi don Kin isa?

Da Sauri Banafsha ta girgixa kai sai xurr hawaye suka sako kai shikuwa mohan ganin yadda Banafshan tayi lumui kamar kamilan kyanwa ta marairace Fuska gwanin tausayi
Dariyar daya ke kintsewar ya sake yayi musu Sosai

...cikin dariyar Yace haba anty nimrah tafa baki hakuri,.
Hararar sa tayi ta sa masa Kuka tace ni nagaji da wannan wulakancin naka mohan, ni nagaji,
Dariyar sa yake,..yace itafa ba abincin da kika ci ya dame ta ba,wannan aljanun naki ne yasa ta dariya

Ko bahaka ba? ya juyo ya kalle Banafsha...a hankali tace ehhh

Aiko jin haka wani sabon rusa kukan nimrah ta fara ta shako fuska kamar xata kashe Banafsha,
Cikin zafin rai tace Kikace ehhh?.

Banafsha da sauri ta toshe baki"Anty Bansan nafada ba wallhy sharrin shaidan ne....
haba mana
mohan daya kafa dariya awajen shi bai san sanda yayi zaune gefen gadon ba.

Shiru Banafsha tayi tana sadda kai kasa dan itama abun ya bata dariya sosai musamman yadda taga nimrah na kuka kamar wacce aka dake ta

Sam nimrah batajin dadi,..She's actually ashame,
sosai taji kunyar abun da ya faru
don bayan bata mata plan din ta na jan aji da yayi,gashi taji kunya sosai agaban mohan
Datake cika masa baki.

Sai da yayi  mai isar sa,sannan ya hadiye dariyar ya juyo yana kallon nimra me kukan kamar taji sakon mutuwa"
Dagota yayi ya aje ta kan gado

sai ya juyo yana kallon Banafsha...
Yace sake bata hakurin"
A hankali Banafsha tace kiyi hakuri anty.

Wani mugun kallon da nimrah ta dago ta mata da jajayen idanu yasa ta hadiye  yawu....kallon Banafshan yayi yace mata get out,
A sadade ta juya kamar munafuka tayi waje,

Bakin gadon shima ya xauna ya jawo nimrah jikin shi ya shiga bubbuga mata baya cikin rarrashi "yace hey girl,tace fa badake take ba besides meye na xuwa dukan aljanu bayan ta riga taganki kinacin abincin ai ce mata xakiyi ta xubo miki tunda kema gidan naki ne
.tare da murmishi ya karasa maganan ,rinannun idanun ta ta dago tana hararar sa a fusace tace toh kai dariyar da kake yimin ta mene ne?...maimakon ka mata fadan abunda tayi min shine xaka biye mata kuna min dariya tsaban wulakanci ko?

AJALIN SODonde viven las historias. Descúbrelo ahora