🥀NOOR IMAN🥀*Fatima Muhammad Gurin*
*Gureenjo6763 on Wattpad**'Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*this page is dedicated to yhu Maman Ameer (Amina Ibrahim) ina me tayaki murnan gama littafinki na zaytoonah wadda be karanta ba yaje ya nema ya karanta kar a barshi baya, In Ana sallah toh fa ba'a magana littafin zaytoonah me kankat ne ya ta'bo abubuwa dayawa marar lissafuwa manya manyan kuwa sune Fad'akarwa, nishad'antarwa, soyayya, ladabi, iya magana da gujewa 'bata daga tafarkin ubangijinmu, Masha Allah, Masha Allah, mun karu da abubuwa dayawa cikinshi, Allah ya baki lada. Sannan Ina me tayaki farin cikin fara sabon littafinki "A barwa rai" Allah ya shigemiki gaba Ina yinki irin over d'innan mutuniyata🥰😘*035*
Zaune suke a parlorn sama sun kunna waka sun kure kaman gidan rawa, jawahir da Hamna ke takawa yayinda umma ke zaune tana karasa taune sauran kazan Amarcin Iman da kukun Hamna ya d'umama musu suka gama breakfast dashi, (ummu Ameer da ummu haneef😝😝😝😝😜 gashi mutanenku sun cinye basu ragemuku ba🤣🤣🤣) tun shidda jawahir tazo gidan Don lokacin da akayi bukinsu Iman bata kasar amma tana samun Information daga wurin ita hamnan.
Tun daga kasa yakejin kid'in ranshi ne yaji ya 'baci ainun ga kanshi dake sarawa ga damuwan ciwon Iman a hankali ya dinga haurawa har ya isa tsakiyar parlorn ba tare da ko ya kallesu ba yaje ya kashe kid'an ya nufi hanyar d'akinshi, umma ce ta dakatar dashi da kiran sunanshi tsayawa yayi ba tare da ya juya ba tace "ya zaka kashe muna chacewar tayaka murnar Karin aure?" Kuji iskanci🙄 taune lip d'inshi na kasa yayi na seconds kan ya sake wani munafukin murmushi yace.
"Ai zakuyi hakuri in angwance tukuna, yanzu Ina ango ne, In na angwance I will let you guys know se kuyi rawar da tushe" Hamna tace "yanzu hamna umma kake gayawa magana irin wannan? Ko ba kanwar mahaifiyarka bace ba ai ta girme maka har haifanka zata iya yi, sannan Ina ruwan mu da wani angwancewanka da b.........." hannu ya d'aga mata "duk babban da be ji kunyar yarda girmanshi ba yaro bazeyi shayin hawa ya taka ba" yana kaiwa nan ya shige d'akinshi.
Jagwab hamna ta zube kan kujera yanzu take jin tana son mijinta se yanzu takejin bazata iya rayuwa ba shi ba, ji take ko me yace ta dena baza ta sakeyi ba har abada, amma yanzu taya zata juyo hankalinshi kanta? Jawahir ce ta dafa ta tace "ke ki dena d'aga hankalinki plz akan wannan gayen na sha fad'a miki In kina so ki mallakeshi se kin bi ta masu duniyar wato bokaye(waiyazubillah) sannan ki sake nairori amma kinki yarda dani" umma tace "Ai yanzu ta yarda tunda munje har sau biyu, ke wani babban boka kika sani me kankat wadda daga munyi shikenan?" Jawahir tace "yanzu mu shiga daga ciki muyi magana kar ya ji mu, huuuuuu kawata kice kin shigo gari wallahi kukanki ya yanke inde wannan mijin naki ne kad'ai matsalarki" murmushi tayi suka shige ciki suna ta hure mata kunne akan boka shine maganin komai. (Allah ya shiryemu ya tsare mana imaninmu).
********
A hankali ta fara bud'e idanunta kanta na tsananin sara mata da fankan d'akin dake juyawa a hankali ta fara cin karo, "Sannu Iman kin tashi?" Taji An fad'a daga gefenta juyawa tayi a hankali tana d'aga hannunta da taji alamun ba komai a jiki tana dafe goshinta, Anty rahama ta gani gefenta Anty kalthum da zarah se Hamma hafeez, murmushi tayi musu tana amsawa da "yauwa" zarah tace "bari In kira ya sauban.
Fita tayi chan anjima suka dawo da sauban da kuma dr Amira, yana dariya yace "Anty kuka tura zarah kirana kuna so mutumin yayi kuli kulin kubura da ni ne yau?" Anty kalthum tace "me yasa ze yi kuli kulin kubura da kai?" Tayi maganan tana dariya tun kan taji me dalilin. Labarin abinda ya faru jiya ya basu dariya duk suka dingayi suna mamaki har Doctor Ameera dariya take yayinda kunya ya rufe Iman, Anty rahama tace "eyeeee malabon ne ya rud'e kan mace aaa Lallai Iman kin taki sa'a".