🥀NOOR IMAN🥀*Fatima Muhammad Gurin*
*Gureenjo6763 on Wattpad**'Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)*038*
"Ba yanzu ba Mama bazaki tafi ki barni ba Mama kece gatana plz karki tafi" abinda take ta furtawa kenan tun farkawanta daga suman shock d'in abinda doctor ya fad'a, d'agota yayi ya rungume yana shafa bayanta a kunnenta ya dinga rad'a mata adu'o'in da zatayi Don samun saukin tashin hankalin da take ciki sbd mutuwar Mama, ta kuwa kar'ba tayi ta maimaitawa har seda taji ta samu natsuwa kan ta d'ago da sauri "karfe nawa hamma?" Yace "hud'u saura" Da sauri ta nufi sauka ya riketa "Ina zaki?" Tace "Hamma baza'a kai Mama bamuyi sallama ba dan Allah ka kaini In ganta" tayi maganan hawaye na ci gaba da gangara daga idanunta.
Taimaka mata yayi ta sauka sossai tausayinta da sonta suka kara narkewa cikin zuciyarshi ita kam haka Allah ya so ya ganta, Allah ya bata daman haye waennan kaddarorin rayuwar, jikinshi ya manna ta har suka isa motanshi ya bud'e mata ta shiga tana ci gaba da hawaye, shima zagayawa yayi ya shiga se ga Anty rahama itama ta shige baya suka fice.
Karatun qur'ani yayi playing suratul A'araf sheikh Abdulrahman sudais ke rero karatun, saurara take tana jin tension d'inta na sanyaya amma fah hawayen be dakata da zuba ba sede ba magana ko uhm bata iya cewa har suka isa hawaye take, shima gabad'aya yayi kalan tausayi zafin hawayen yakeji har ranshi amma ya ya iya? Dole tayi kukan wannan rashi da ze iya da ya tayata.
Mutanen da ta gani jibgi a kofan gidansu yasa kukanta fara fita da shesheka, fita yayi ya zagaya ya bud'e mata tare da rusunawa kad'an yace "kukan nan be isa haka ba saudah? Kin san fa ba lafiyace ta isheki ba kema, kiyi hakuri ki kar'bi wannan jarabawar hannu bibbiyu ko kin manta Allahn da ya bamu ya fi mu sonta? Lokacinta ne yayi Muma In tamu tazo ko munki ko mun so se mun je gareshi so why not kiyi ta mata adu'ar dacewa da rahamar ubangiji akan wannan kukan? Ko kin manta kuka karin zunubi da nauyi ne ga mamaci?".
Tafin hannunta ta sa ta share fuskanta tana gyad'a mishi kai, mikewa yayi ya kama hannunta Anty rahama da itama hawayen tausayin Iman d'in ya zubo mata ta bi bayansu, da sannu da sannu suka shige cikin gidan, mata ne ko ta ina hakan ya sa shi had'a hannunta da Anty rahama shi kuma ya ja baya, en uwa ne ko ta Ina kowa hawaye da kukan wannan rashi yake Mama mutum ce wacce ta chanchanci ayi kukan rashinta.
Ana ganin Iman kuwa aka fara Allah sarki Allah sarki wadda hakan ya kara sa Iman kuka, d'akin baba aka nuna mata alamu chan gawan maman yake, da sassarfa ta karasa d'akin tare da zubewa gaban gawan da aka mishi komai saura sallah da kaiwa makwanci, kawai se ta rungumeta ta kuma fashewa da sabon kuka "Mama dan Allah ki tashi na san baza ki mutu ki barni ni d'aya a duniyar nan ba, mama kin manta kince In Shaa Allahu se kinga jikokina kan mutuwanki, kin manta kinci burin yi min wankan jego da alkawarin ko Ina So ko bana so se naci tuwon dawa da kunun tsamiya? Mama dan Allah ki tashi bazan iya ci gaba da rayuwa ba ke ba In wani abin ya kara faruwa da ni fah? Mama kina so in mutu nima? Na san bakya so ki tashi dan Allah mamaaaa.....".
Wani irin kuka me ban tausayi take, Baba dake gefe se share hawaye yake yayinda Umma tayi saurin ficewa tana ci gaba da kuka, kaman ance saurara taji zuciyar Maman na bugawa kasa kasa, kunnenta ta kara mannawa Ai ko de ba hasashe bane da gaske ne.
Chak kukanta ya tsaya ta d'ago ta kalli baba tace "baba Mama bata mutu ba wallahi tana numfashi" girgiza kai baba yayi yace "kiyi hakuri Mamana, ke aka wa rashi dole hankalinki yafi na kowa d'agawa, na sa...." katseshi tayi tace "baba ba fa wai rud'ewa bane ko wani abu wallahi naji tana numfashi zo ka sa kunnenka kirjinta kaji yana bugawa" dukawa Anty rahama tayi ta dafa kafad'anta tana cewa "haba Iman kiyi tawakkali mana ko kin ta'ba ji Ance wadda ya mutu ya dawo ne?".
![](https://img.wattpad.com/cover/243459919-288-k522923.jpg)