🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
*Gureenjo6763 on Wattpad*
*'Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*041*
Murmushi yake sakewa akai akai yana sauraran sauban dake zuba mishi surutu akan Iman, tsaye yake ya d'an jingina bayanshi da gini tare da hard'e kafanshi "khaih Abokina ka rufta dayawa wallahi wai kaga yadda ka rud'e kuwa akan yarinyar nan? Allah ban ta'ba zaton zaka so wata mace haka ba duba da yanayinka akan mata" wani murmushin ya saki yace "Ni Allah ka rabu da ni In ba kana so ka neme ni ka rasa bane sbd In kana hiranta ji nake kaman inyi tsuntsu In sauka gareta".
Wani irin dariya Sauban ya saki yana cewa "sannu Romeo ko ince majnun kai yanzu ka zama fah mijin tace" harara ya sakar mishi yana kauda kai yace "Kai ta shafa d'an sa ido" dariya ya ci gaba dayi har seda Abdul ya buga desk d'in gabanshi yana cewa "Allah ko ka gayamin abinda ya sa ka juyo dani daga asibiti zuwa office d'inka ko In maka rashin M" tsagaita dariyar muguntan shin yayi yace "akan maganan mama ne matar fa tana wahala sossai gashi alamu sun nuna tana kumbura da kad'an da kad'an why not in da hali ka kaita wani kasan sbd su duba ta da kyau mu iya dubawanmu bamu gano komai ba dukda sauran results d'in se nan da sati biyu, amma ni a ganina wajen zasu fi mu kayan gwaje gwaje ingantattu" gyad'a kai yayi kan ya gyara tsayuwarshi yace "kana ganin wani kasa ya kamata a kai ta?" Sauban yace "I think Miami ko de Cairo" dafe kai yayi abubuwa na cha'be mishi gabad'aya.
Ga ciwon Abba ga shi an turashi wani aiki New York, ga shi yana so cikin santin nan su tafi Adamawa wurin baba fufore sbd matsalan hayateenshi da ummunshi, yana so yaga komai ya tafi smoothly amma be san...... katseshi sauban yayi da cewa "ya y lafiya kuwa mutumi na?" Ajiyar zuciya ya sauke kan ya fad'a mishi damuwanshi amma ya 'boye akan me Iman zataje ganin baba fufore, murmushi Sauban yayi yana cewa "Abu mai sauki ka bar mana Mama a nan zuwa sati biyu in de har zuwa wurin baba fuforen baze fi haka ba, and Ina ce office se next two weeks suka ce tafiyan? Fine se ka d'auke matarka ku tafi daga chan ku tafi yawon honeymoon" murmushi Abdul ya sake yana girgiza kai dama chan yana son zuwa london don duba Company d'inshi.
Ya rasa ya akayi be yi tunanin haka ba seda sauban ya fitar dashi ko Don abubuwan gabanshin na dayawa, "Allah gayen nan sa idonka yayi yawa se kace haka na sa maka ido da naka iyalan, mtseww by the way thank yhu" be jira amsan sauban ba ya fice abinshi yana ji sauban d'in na wasu maganganu cikin dariya girgiza kai kawai yayi ya karasa motan shi ya tayar ya nufi asibitin da Abba yake, cike ya samu d'akin da en gidansu gabad'aya kowa da kowa na nan wurin ummu ya nufa ya duka har kasa ya gaidata a d'age ta amsa.
Ya dawo kusa da Abba ya gaidashi cikin fara'a sossai ya amsa shi, Anty rahama ya gaisar daga nan itama ta amsa duk yanayinta ba daad'i sbd har lokacin abinda ummu tayiwa iman na ranta, Anty kalthum, Hafeez da zarah suka gaida shi, amsawa yayi yana d'an murmushi, sede tunaninshi na Ina Iman tayi be ganta a d'akin ba bayan yace ta jira shi a nan, be de yi magana ba se mikewa da yayi ya fita yana danna waya layinta ya ta kira bata d'aga ba.
Dawowa yayi ciki a lokacin umma da Hamna suka shigo cikin fara'a sossai ummu ta tarbesu yayinda sauran da kyar suka gaisheta duk harara ta zuba musu a fakaice ta gaida Abba ya amsa ba yabo ba fallasa, Abdul kam ma ko ta inda suke be kalla ba bare har ya wani gaisheta, Don rashin ta ido a tsayenta yadda take ta gaida Abban gaisuwan ma ba ladabi bare taushi a harshenta.
Dr. Ne ya shigo da murmushi ya bawa mazan hannu suka gaisa, yace "amm please kuyi hakuri ku je waje bari In duba shi" duk fita sukayi yayinda Abdul ya mike don fita kenan Abba ya kira sunanshi, dakatawa yayi, Dr yacewa Abba "hope ka sha magungunan da 'yar ka ta kawo?" Murmushi Abba yayi yace "na sha tuntuni, yanzu ni Ina ganin za'a iya sallama na Don bana jin komai jirin ya daina" Doctor yace "ciwon kan fah?" Abba yace "shima kad'an kawai nakeji" dr yace "masha Allah bari In duba jinin In har ya sauka sossai za'a iya baka sallama" aikinshi ya fara, Abba na kallon Abdul yace "mahaifiyarka ta koreta ta tafi" Da sauri ya d'ago zuciyarshi na bashi yanzu kuka take kenan.
