BABI NA ASHIRIN DA SHIDDA

2K 171 16
                                    


🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
•Gureenjo6763 on Wattpad•

*'Yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

*026*

Nenne ce da kanta tazo ta tarbeta hannunta ta kama har part d'inta kanta a kasa so bata samu damar karewa masarautar kallo ba amma de ta tabbatar Allah yayisu da yawan kuyangu ko bayi don duk inda suka bi gaisuwa ce kawai ke tashi amma ba wadda ke amsawa wadda hakan ya sata jin ba daad'i bata san haka gidan sarauta yake ba.

Ke'bantaccen d'aki babba sossai nenne ta kai ta zarah de na binsu a baya Ummu da Abba kam tuni sunyi site d'insu yayinda hamna tayi wurin nenne petel don a chan sukayi zasu had'u da ummanta, Hafeez da Abdul kowa site d'inshi ya tafi, "Feel at Home Ohk?" Nenne ta furtawa Iman, gyad'a kai iman tayi tana murmushi, ko ba'a fad'a mata ba ta gane wannan itace nenne mahaifiyar Abba, tsohuwa me mutunci da sanin ya kamata.

Fita tayi wasu mata suka shigo d'auke da manyan trolleys har guda uku, zarah dake mata masifar ta bud'e kanta haka ta sha iska ta dakata tare da juyawa ta kallesu, a tare suka ce "barkanku da isowa, Hajiya Nenne ce ta turo mu don fara yiwa Amarya abinda ya kamata" murmushi zarah tayi kan ta gyad'a kai tana janye gyalen fuskan Iman "Toh madam se ki mike za'a fara miki gyara" kallon matan tayi kan tayi murmushi suma suka mayar mata.

Akwati d'ayar ta bud'e ta d'auko wani silk farin riga da iyakarshi be wuce gwiwar ta ba ta bata "ranki shi dad'e bismillah" kar'ba tayi ta kalli rigan ta kuma kallon rigan ita zata saka wannan a gaban mutanen nan? 'Bata fuska tayi zatayi musu zarah tace "wallahi if I hear pim Nenne zan kira" Sarai ta san halin zarah hakan yasa ta mike ta shiga toilet ta sako da kyar ta fito ya kuwa amshi jikinta se tattakurewa take gashi hannunshi irin na vest.

Zama tayi bakin gadon tana kallonsu dariya zarah ta kwashe dashi bata san sadda ta banka mata harara ba, d'ayar ce ta katsesu da cewa "ranki shi dad'e In ba matsala zan iya bud'e kanki?" Kai ta gyad'a matar ta matso ta bud'e kanta ba laifi gashinta na da tsawo sossai zuwa de wuyanta kuma ba datti amma dukda haka matar tace "ranki shi dad'e kan yana bukatar wanki zamu iya karasawa toilet?" Wani irin abu iman ke ji In manya mutane irinsu suna mata magana haka cike da girmamawa kuma se suyi maganan kaman neman izini suke.

Mikewa tayi ta bita suka shiga bayin tas ta wanke mata kai cikin natsuwa ba hayaniya zata iya rantsewa bata ji ko alamun zafi ba haka ruwa ko kad'an be hau kanta ba, suna fitowa taga d'ayar ta had'a wani karamin kujera gefen sockets bismillah tayi mata kan ta karasa ta zauna, wacce ta wanke mata kai d'ince ta fiddo hand dryer ta had'a ta fara busar mata da kai yayinda d'ayar ta d'auko lallen da bata san sadda aka kwa'ba ba ja da baki ta fara mata jan.

Yayinda d'ayar ta fiddo wasu abubuwa kaman kurkur da su madarar turaruka ta fara had'awa, mikewa zarah tayi tana yafa gyalenta tace "Bestie bari inje sashin baba yarima yanzu zan dawo" Kai iman ta gyad'a itafa yanzu bakin magana ma bata dashi, abinda ya kamata ace a gidansu kuma 'yan uwanta ne sun mata se gashi en uwan miji sun had'a gabad'aya sunayi, tsoronta ma kar hakan ya zama abin gori a gareta gashi gidan sarauta yadda take jin labarinsu kad'ai abin tsora ne bare kuma ta zama topic of discussion.

Cikin awannin da basu wuce uku ba an gama mata had'ad'en lalle ja da baki har an kankare, gashinta an zuba mata nyinyirin two step kaman ka lashe tsabar had'uwar kitson da kankantarshi, jikinta An mulkeshi da dilka, 'yan mata ne hud'u a d'akin bayan zarah, Nabeeha, Ameerah, teemah da zee yaran baba yariman ne kuma kusan sa'anni ne da zarah, musu suke akan wacce ta fi kyau tsakanin Hamna da Iman duk d'akin ya kaure da hayaniya Zee ce tace "wallahi Iman tafi kyau ku tsaya kuji hujjojina" Shiru sukayi suna sauraranta ta d'aura da.

NOOR IMANOù les histoires vivent. Découvrez maintenant