🥀NOOR IMAN🥀*Fatima Muhammad Gurin*
•Gureenjo6763 on Wattpad•*'yar mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)*02*
"Wow nice name, kiyi hakuri fah da abinda Dr. Abdurraheem ya miki haka yake da wulakanci ga dizgi wai shi In har ya shiga aji to ba me shiga a bayanshi, amma ke baki jima da fara zuwa ba ko? Gashi an ci rabin semester na san baki yi catching up wasu abubuwan ba, zan dinga koya miki karki damu daga yau mun zama friends".
Lord!! Wannan bade surutu ba mutum kaman aku, na raya a raina a fili kuwa murmushi na mata Ina son inyi karatu sossai inga na zama wata a duniyan nan yanzu ban son aure ban son wani magananshi karatu kawai hakan yasa nake son yin kokarin yaki da zuciyata In kuma kau da tasiri da maganan mutane ke min inyi karatu tukuru.
Dama asalina me surutu da kazar kazar ce rayuwa ne ya maida ni miskilar karfi da yaji, kallonta nayi nace "yanzu d'an wannan yaron ne doctor kina nufin ya kammala doctoring degree d'inshi?" Zarah ta ta'be baki kan tace "kwarai kuwa ke abunki da wadda be yi karatu a nigeria ba firrrrrr ya tafi ba wani delay balle strike duk degrees d'inshi a kasar waje yayi kuma daban daban"
Jinjina kai nayi don son kawar da magananshi na ce "Toh yaushe zaki fara koyamin karatun?" Tace "duk sadda muke da interval tsakanin lectures se mu dingayi ko In mun gama da wuri kuma bamu da wani se mu d'an yi kan mu tafi" wannan karon murmushin da na mata tun daga cikin zuciyata ya fito, wara brown eyes d'inta kad'an tayi kan itama ta saki murmushi tace "wow I like your dimple and your wushirya" na kuma yin murmushi nace "nice meeting yhu zarah".
Tace "same here" hira ta ci gaba damin ni kam se nodding da d'an murmushi tunda na shiga 18 zan iya rantsewa ban ta'ba mintuna biyu ba tare da damuwa ko tunani ba amma gashi yau samun mutum a kusa dani kuma me faran faran ya sani sakewa da ita sossai har na manta da damuwana na wani lokaci.
Eleven nayi muka shiga another lectures na chemistry sossai na maida hankali kuma ba laifi na fahimta don ni d'in ba laifi me d'an kwakwalwa ce.
Karfe d'aya muka fito muna fitowa zarah ta kalleni tace "har anzo d'aukana muje mu sauke ki a gida ko Ina Gandun albasa kike kikace?" Kai na gyad'a mata Ina d'an murmushi nace "nop ke kam yi wucewarki, se in mun had'u gobe" na san irin gulman mutane yanzu a fara rad'e rad'en na fara bin maza ana saukeni a manyan cars dama yanzu ma ban tsira ba.
Ba yadda zarah batayi ba amma naki haka ta tafi ni kuma na ci gaba da takawa a hankali sbd kafana da ya d'an suntuma zuwa lokacin, ban wani 'bata lokaci ba na tare napep na shige tare da fad'a mishi inda zani.
Bayan mun iso na sallameshi na fara takawa cikin taka tsantsan kaina a kasa kaman kullum daga gefe majilisan 'yan unguwa ne na samari gaba kad'an kan gidanmu na tsoffi.
Kullum In har zan bi ta wurin na wuce se na zub da kwalla dayake mutuwar aurena har biyu a unguwan na Gandun albasa ne, 'ka ganta nan ashawon, ta fito yawon karuwanci da sunan makaranta' runtse ido nayi Ina jin zafin sunan amma daga yanzu nayi alqawarin bazan kara yi musu kuka ba.
Ina jin wani daga ciki yace 'wai itace me aure auren?' Wani yace 'kwarai kuwa aurenta na farko sako ta akayi a daren farko sbd bata kai budurcinta ba' da sassarfa na karasa wucewa dukda zafin da kafana ke yi, haka zuciyata kaman an saka a tukuban tsire.
Ina isa wurin manyan mutanen na duka har kasa na gaidasu suka amsa ba yabo ba fallasa amma nayi musu farin sani na san ina bada baya za'a dasa maganata dukda ba koyaushe sukeyi yadda zanji ba amma sun hana 'ya'yansu kap huld'a dani wai zan 'bata su.
Ina shiga gida hawayen da nake rikewa ya fara gangara umma ta na tsaye jikin igiya tana shanya baba zaune a kan taburma kasan bishiyar umbrella (almond) yana shan iska don ya dena fita majalisa sbd habaice habaice da bakar maganganun da ake ya'ba mishi gashi ya ci alwashin baze ta'ba chanza wani unguwan ba sbd ni, rijiyar lemo da Gadon kaya sun isa.
"Umma barka da gida" da "yauwa" kawai ta amsa ni ba tare da ta ko kalle ni ba, girgiza kai nayi inajin hawayena na karuwa na rasa dalilin kasa sabawa da wannan hali na ummana a shekaruna na 23 a duniya.
Har kasa na duka gefen taburman baba nace "sannu baba Ina yini?" Kau da kaina nayi daga kallon banzan da yake watsa min Ina jin yadda ya ja dogon tsaki, gwiwa a sage na mike na karasa kofan mama nayi sallama daga ciki ta amsa ni tana cewa "lale lale 'yar albarka barka da dawowa" murmushin yake nayi na karasa parlorn na zauna.
Ikhram da ikhlas dake zaune saman kujera suka ce "sannu da dawowa yaya iman" nace "yauwa" mama ce ta fito tana kallona tace "naga kaman duk kin gaji tashi kije kiyi wanka ki zo ga abinci nan kizo kici" wani yaken nayi Ina mikewa nace "Toh mama na gode" taku d'aya biyu nayi naji ta saki salati tsayawa nayi na san sbd kafana ne itace kad'ai!!
Itace kad'ai a duniyata da zata ganni da damuwa ta magance min, ita ce kad'ai me sona nan duniya haka nima Ina sonta har raina sbd son da take min ban damu da kasancewarta kishiyar uwata ba "na shiga uku Iman me ya samu kafankin?" Na juyo Ina murmushi nace "mama bugewa nayi" tace "ashsha zo muga" wurinta na koma tana gani ta waro ido "maza juya mu fice gidan malam iro ya gyara miki daga gani gurd'ewa ce ko tsagewar kashi".
Baki na turo Ina shirin mata musu har ta shige d'aki tana fitowa ta sani a gaba muka fice zuwa tsakar gida ta kalli baba tace "malam yarinyarnan Noor Iman ta samu matsala a kafanta bari muje gidan malam iro ya duba mata" bata jira cewar shi ba muka wuce don ta tabbatar ba amsa ze bata ba inde akan maganan da ya shafeni ne kaman yadda nima na san da hakan.
Muna isa ya tabbatar da gocewar kashi ne a rike ni ya gyara da kuka da komai aka gyara mama se mita take wai na cika ragwanci, biyanshi tayi muka fito muka dawo gida ina share hawaye, wanka nayi na shirya cikin riga marar nauyi duk a d'akin mama komai na yake don ban ci darajar a bani d'aki na ni kad'ai kaman sauran 'yan matan gidan da yanzu suke gidan mazajensu ba.
Ido na a lumshe nake taryo rayuwarmu na baya, Malam Musa Muhammad d'an asalin kauyen wudil ne na nan jahar kano yana da mata d'aya da yara takwas ya jima yana sana'an driver kuma har Allah ya kar'bi rayuwanshi sana'anshi kenan, da Sana'an ya sayi gida anan hayin rigasa suka dawo nan da zama anan cikin kano gabad'aya yaranshi sukayi karatu kasancewarshi me son boko, dukda shi be yi ba, baba shine na hud'u a cikin 'ya'yanshi yana da kanne hud'u.
Goggo Kamila, goggo saratu, goggo hindatu, se bappa Audu.
Yayyunshi uku duk maza ne bappa Yushe'u, se bappa Mu'azu se bappa sama'ila kan baba, duk mazan sunyi karatu daidai gwargwado iyawar mahaifinsu kan rasuwarshi inda babana yayi diploma d'inshi a fannin mass com, ya auri ummana (Aisha) ne a chan garin malumfashi na nan katsina inda ta kasance 'ya d'aya tilo a wurin iyayenta batayi wani karatun kirki ba iyayenta suka cireta suka aurar da ita.
A lokacin ya fara aiki a matsayin karamin ma'aikaci a gidan rediyon freedom, suna son junansu don zaman amana da soyayya sukeyi wadda jigonshi ya kasance hakuri, har ummana ta shekara hud'u bata ta'ba koda 'Batan wata ba, hakan yasa su goggonina da inna mahaifiyar baba suka matsa ya karo aure yaki sam amma se suka fi karfinshi inda ya auri kanwar matar bappa yushe'u.
🖤Gureenjo🖤