BABI NA ARBA'IN

2.6K 173 8
                                        


                🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
          *Gureenjo6763 on Wattpad*

*'Yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

*this page is a dedication ga duk wata Nurse me karanta littafina I'm so sorry if yhu guys feel disappointed, or some kind of disrespect a page d'ina na jiya, ban sa don cin mutunci ko wani abu ba if yhu noticed and baka ji daad'i ba sorry!!!!!.

                        *040*

Banko kofan da akayi ne ya sanyata d'ago kai daga kallon jibgin akwatunan dake gabanta da take shirin fara jerasu cikin wardrobe, kallon Hamna takeyi cikin mamakin wannan isa haka, ta tashi da wuri sbd bata wani iya baccin safe ba amma taji daad'in d'an baccin sossai fiye da yadda zatayi na awanni jinta take garau kaman ba jiya aka sallamota ba hakan yasa ta watsa ruwa kawai ta zura wata cotton doguwar riga ba tare da ta nemi d'ankwali ba ta janyo akwatunanta da shirin shiryasu cikin wardrobes d'in.

Cikin ta'be baki take karewa d'akin kallo up and down side by side, daga karshe ta ja tsaki tana cewa "Eyyah abin kunya da Allah wade na gode Allah da nawa iyayen ne suka min komai na d'akina basu jira gidan miji ba" ta'be baki tayi tace "Au ashe fa talakawa ne likis ba sisi bare kobo na taburman kaba" Zatayi wani maganan Iman tayi saurin cewa "toooh Allah sa de lafiya baiwar Allah se kace ba musulma ba? Ki shigowa mutum wuri ba sallama sannan ki tsaya kina haushi kaman......" bata karasa ba ta wani kwa'ba fuska ta maidashi kan kayan.

Cikin 'bacin rai hamna tace "kutumarr ni kike kira karya??" Ko kallonta Iman batayi ba ta bud'e wardrobe ta fara shirya atamphopin da ta fidda daman, "ke da ke fa nake magana, don uwa....." "kulll" cewar Iman tana karawa da "Uhmmm uhmm uwata fah ba sa'an wasan wata uwar bane bare wata yarinya ta samu daman zaginta a kiyaye" cikin 'bacin rai Hamna tayi kanta tare da d'aga hannu da niyyar marinta, hannunta taji an rike a zuciye ta juya se suka had'a ido yanayin da taga fuskanshi kad'ai yasata sanyaya nata zuciyar kofa ya nuna mata juyowa tayi ga iman tayi mata wani kallo kan ta juya ta fice fuuu.

Kallo d'aya ta mishi ta dukar da kanta hankalinta na tashi me ya sameshi Ko kuma tace me ke damunshi, kallonta kawai yakeyi zuciyarshi na tsananta bugawa ga sake sake da waswasi da suka taru suna mishi zirga zirga a kahon zuciya, batayi aune ba kawai se ji tayi ya mata wani wawan runguma har seda ta d'an yi kara sassauta riqon da ya mata yayi yana me lumshe idanunshi, a sanyaye ta d'aga hannunta zuwa bayanshi tana shafawa ta lura yana cikin damuwa ba kad'an ba.

Ajiyar zuciya ya dinga saukewa a jere a jere cikin sanyin murya yace "hayateee bazan iya rayuwa ba tare da ke ba wallahi Ina sonki sossai, kallonki kawai da nayi naji rabin damuwana sun yaye" d'agowa tayi ta kalleshi kad'an wani irin sonshi na kara mamaye mata jiki da jini, hannunshi ta kama be musa ba ya bita har bakin gado suka zauna kwanciya yayi tare da d'aura kanshi kan cinyarta ita kuma ta sa hannu cikin sumar kanshi tana wasa da shi.

Cikin taushin murya tace "menene ya faru? Akan matsalata ne ko?" Hannunta d'ayan ya kama ya d'aura kan kirjinshi tare da d'aura nashi kai idanunshi lumshe yace "Abba ba lafiya" a rud'e tace "innalillahi wainna ilaihi rajiun me ke damunshi haka?? Yana Ina asibiti ko gida?" Bud'e lumsassun idanunshi yayi ya zuba mata yadda ta rud'e kawai yasa yaji jikinshi yayi sanyi har hawaye ta fara ko su iya rud'ewar da zasuyi kenan.

Me laifinta? Bata da ko d'aya abinda ya kamata ya tambaya shine me ke damun ummu ne a duniyar Allahn nan? 'Digar hawayenta kan fuskanshi ne yasashi sauke ajiyar zuciya yace "da sauki fah yana hospital" share mata fuska yyi da tafin hannunshi cikin damuwa tace "Eyyah Allah ya bashi lafiya bari In tashi in shirya ka kaini pls in dubashi". 'Daga kanshi yayi ta mike shi kuma ya janyo pillow ya kwanta da kyau, a maimakon tayi toilet se ta fita zuwa kitchen, da tunanin abinda zata girka musu har mijin nata da ta tabbatar be karya ba ta shiga.

NOOR IMANMga kuwentong kahuhumalingan mo. Tumuklas ngayon