BABI NA HAMSIN

2.6K 168 35
                                    


                  🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
           *Gureenjo6763 on wattpad*

*'Yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

*hakika bani da abinda zan ce muku sisters se Allah ya saka da mafificin alkahiri ya bar kauna, duk naga adu'o'inku gareni na gode kwarai Allah ya amsa ya biya mana dukkanin bukatunmu na alkhairi ba shaaka wannan page d'in naku ne sadaukarwa ne ga dukkan waenda suka iya 'bata lokacinsu da data d'insu wajen min adu'a na gode kwarai na muku wannan page d'inne sbd jin daad'in adu'arku, ranan litini In Allah ya kaimu zan fara jarabawar na gama tests. Allah ya bamu sa'a gabad'aya a duk abinda muke.

                           *050*

Cikin farin ciki da jin daad'in ganinta Anty rahama, Anty kalthum, zahra suka rungumeta murmushi kawai take musu tana jin daad'in yadda suke kaunarta har kasa ta duka ta gaida ummu dake "ga daughter, ga daughter" a kunyace ta gaidata ta amsa da fara'a ta gaida Anty rahama da Anty kalthum duk suka amsa suna mata barka nan fa hira ya 'barke akan ire iren abubuwa haka da suke faruwa.

Sun jima zaune parlorn ana hira kan Abba, Hafeez da Abdul suka shigo a tare kasa ta zame ta gaida Abba ya amsa fuska a sake cike da farin cikin ganinta barka ya mata na shiryawa da ummanta ya sa musu albarka gabad'aya ya wuce parlorn shi, nan Hafeez ya fara tsokanarta su Anty rahama suna rama mata gogan nata kam zama yayi ya zaro waya ya fara aikin call idanunshi a kanta wadda hakan ya sa gabad'aya ta takure ta kasa sakewa kunyan su Anty kalthum na kamata musamman da taga Antyn da zarah na kuskus.

Dayake tun shigowar Abba ummu ta bi bayanshi, yana gama wayan ya taso yazo inda take a kasa ya zauna gefenta har cinyansu na gogan juna wayanshi ya dadanna ya fito da wasu hotuna ya d'an duko gefen kafad'anta yace "duba kiga wanne ne yafi kyau anan?" Kar'ba tayi ta fara kallo wasu motoci ne masu asalin kyau colors daban daban daga gani kuma zasuyi tsada akan wata BMW ta tsaya sede colourn Dark blue ne ta san shi kuma baya son colored car kallonshi tayi shima wayan yake kallo yace "ita tafi kyau?" Kai ta gyad'a yayi murmushi tare da kar'ban wayan.

Kashe wayan yayi da sauri ganin Anty rahama na leko kai, hararinsu yayi yana mikewa yace "gulma dae ajali" suka kwashe da dariya gad'aya iman na sakan murmushi, kiran sallah ne ya katse musu hiran da suka d'auko ana gama kiran Abba na fitowa suka had'u da mazan sukayi masallaci basu dawo ba seda sukayi Isha, bama su zauna ba ummu ta nuna hanyar dining tana cewa "bismillahnku dinner is ready" duk dining sukayi ta d'aga wayanta ta kira zarah tana d'agawa tace "me kukeyi ne har yanzu baku sauko ba? Kunga In ku bakwa jin yunwa ku turomin 'yata taci abinci" tana kai nan ta kashe waya.

Zarah ta sauke wayan tana kallonsu Anty cikin muryan shagwa'bewa tace "mu kuma da bola aka tsinto mu se muyi ta zama da yunwa" dariya suka saka Iman na murmushi ta mike sbd su Anty ne kawai bata make zarah ba, dama tunda suka shigo take ta kwaikwayan yadda ummu ke masifa akan Iman se dariya suke, da dariya suka sauko suna hiransu duk suka zauna se suka bar mata seat d'in dake facing d'inshi.

Zarah ce tayi serving kowa tana bawa Abba labarin itama fah ta kusa zama graduate, Hafeez yace "a ina d'in ke da yanzu kike level one" Anty rahama tace "kyaleta shekaru kusan hud'u ke gabanki Don bakiyi komai ba madam" Anty kalthum tace "kila ma harda spill se ki kara mata shekaru biyu kin san itace Anty olodon gidan nan" bubbuga kafa ta fara kasa tana cewa a shagwa'be "Abba ka gansu ko?" Yace "Kunga rahama banaso ku kyale min auta ta sarara, In Shaa Allahu ba spill da zakiyi kinji?" Kai ta gyad'a tana murmushi a lokaci d'aya tana musu gwalo.

Shifa duk abinda sukeyin nan ba sauraransu yake ba tunaninshi da hankalinshi duk ya d'auke akan matarshi murmushin da takeyi ji yake kaman fuskanta ya dawwama a haka har abada, wushiryan tan nan me kyau da one side dimples d'inta da yafi komai d'auke mishi hankali, dayake saitinshi ta zauna ta d'an mike kafa kanta kasa tana juya chokali a lokaci d'aya tana murmushin dramar zahra don har time d'in bata gama ba.

NOOR IMANWhere stories live. Discover now