🥀NOOR IMAN🥀*Fatima Muhammad Gurin*
•Gureenjo6763 on Wattpad•*'Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)*023*
"Ummu" ya furta muryanshi na rawa ta daka mishi tsawa "just choose I said!!" Wayanta ne ya d'auki kara hakan ya sa ta maida hankali kai Abbu ta gani da sauri ta d'aga ta d'aura a kan kunnenta se jin muryanshi tayi cikin fushi da fad'a yana cewa "Abinda kike yiwa mijinki da 'ya'yanki kenan dama Rashida?" Cikin kasa da murya tace "Abbu ba fa haka bane ba yarinyar da za..." tsawa ya daka mata "shut up!!! Toh bari kiji da kyau ina me miki rantsuwa da Allah duk kika tilastawa Me suna ya za'beki a kan matar da yakeso na cire ki daga cikin 'ya'yana sede ki nemi wani uban, kuma rashin kunyar da kika d'auka kika yafa wadda ba halinki bane ki ci gaba karki fasa ki bari mijinki ya sake kawo min kararki zanzo har kanon In sa'bamiki a gaban 'ya'yanki In yi dawowa ta don kin haifi samarin 'ya'ya ba shi ze baki lasisin 'bata tarbiyarki da mai da kanki wata kabila ta daban ba".
Me yasa ba wadda ze fahimceta ne? Me yasa take ji kaman In Abdulraheem ya kara aure mutuwa kawai zatayi? bata san sadda ta fashe da kuka ba, se jin muryan Nenne petel tayi tana cewa "Haba rashida ke da kike da tunani da hangen nesa me ze sa kiyi tunanin hana d'anki kara aure bayan ba haramun bane a addini? Ko aka gayamiki don yana auren 'yar uwarshi se baze auro wata ba? Ke fa ba yarinya bace meyasa rashida ba'a ji kanki da mijinki tun kina yarinya ba seda kika girma kika mallaki fiye da hankalin kai? Kar ki 'bata wayonki na gayamiki wannan ba yi bane, and ki sani kaman yadda mahaifinki ya fad'a matukar kika yi sanadiyar da yasa yaron nan fasa aurenshi to ki nemi wasu iyayen ba mu ba". Se ta kashe wayan.
Kuka sossai ummu ke yi wadda yasa Abdul jin hawaye ya cika mishi ido. Yanzu shine sanadiyar hawayen mahaifiyarshi? Takawa ya farayi a hankali ze je gareta se Abba ya mishi hannu da ya fita, fita yayi Abba ya tashi yaje kusa da ita ya zauna tare da sa hannunshi ya kamo nata se kawai ta kwanta jikinshi ta kara fashewa da wani kukan, bayanta ya dinga shafawa a hankali da alamun rarrashi, Mamakinta sossai Abba ke yi, me ya samu rashida haka? Ba haka take ba, ta d'auki abinda ba shine ba ta d'aurawa zuciyarta, tabbas da ze iya da ya hana Abdul aure sbd kwanciyar hankalinta amma kuma Saudah d'in fah?.
Da kyar ya samu tayi shiru jin ba kukan yasa shi zame jikinshi yace "ki shirya akwai tafiyarmu yola goben, bayan d'aurin aure amma mu nan flight zamu bi da amaryar se 'yan uwanta su bi mota" Kai ta gyad'a mishi kan ta mike ta fice.
A inda ya barsu nan ya fito ya samesu zarah na kallonshi ta san ba Lafiya ba don idonshi ya kad'a sossai fuskanshi yayi ja abinka da farin namiji, goshinshi ya fito da wani jijiya babba, Anty rahma ta mike tana cewa "Lafiya kuwa Abdul?" Zarah tace "me ya faru Hamma?" Ko kallonsu be yi ba ya fice daga parlorn, da sauri zarah ta bishi har ya d'aura hannu akan handle na mota ta d'aura hannun ta akan nashi kallonta yayi da alamun gargad'i.
Ta dukar da kanta tace "yhu can't drive in this situation, plz let me drive" sake mata handle d'in yayi ya bud'e baya ya shiga, shiga itama tayi ta danna button d'in key tare da jan motar gate man ya bud'e mata ta fice, har suka isa gidanshi kanshi na jikin kujera yana son mahaifiyarshi fiye da zato ko kad'an baya son abinda ze bakanta mata rai amma gashi yau shi ne yasa iyayenta yi mata fad'a harda barazanar tsinuwa da girmanta.
"Idan ummu ne kayi hakuri Hamma ka kara mata lokaci tabbas Ina matukar zargi da kokonto kaman ba haka kawai ummu ke abinda takeyin nan ba, duk don da takeyiwa hamna ta san daidai ta san akasinshi, kar pressure d'inta ya sa ka fara dana sanin aikata aikin ladan da kayi niyya, haka karka manta komai rubutacce ne ko kana so ko baka so, ko ummu na so ko bata so kai ko duk duniya suka taru suka ce basa so In har Allah ya riga ya rubuta ba yadda aka iya, so dan Allah karka tsani kawata" ta bud'e motan ta fita d'ankwalin kanta ta warware tayi gyale har ta fara tafiya ya fito yace "Auta" ta juyo ya nuna mata motan alamun ta d'auka tare da kakaro murmushi ya sakarmata be kara kallon inda take ba ya shige gidan.
