🥀NOOR IMAN🥀*Fatima Muhammad Gurin*
•Gureenjo6763 on wattpad•*'Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)*027*
Walima akeyi me class wadda ya ratsa duk wani me sauran imani kan a tashi kuyangi suka fara shigowa da abinci kala kala suna rabawa da souvenirs da ban san sadda akayi ba, a cikin paper bag me d'auke da hotunansu su biyu rike da hannun juna ita kanta bata san sadda akayi ba, cikin jakan kuma dardumar sallah ce babba me tsadar da azkar wadda ya had'a na safe dana yamma se na bacci da bayan sallah a jikin ba hotonsu sede sunayensu, se memo me d'auke da hotonsu kala kala masu kyau.
Dukwadda ya taka kafanshi wurin seda ya san eh fah wannan walimar ta had'u, 'yan Annur hausa novels harda fad'a wurin karbar souvenirs bayan nenne ta fad'a musu kowa ze samu😜, ana tashi zarah ta kama hannun Iman suka fice bata bari sunyi magana da en uwanta ba sbd kar su 'bata mata rai ranar farin cikinta, mota suka shiga aka wuce dasu, cikin sanyin murya iman tace "Zarah Ina son ki kaini wurin nenne".
Kallon drivern zarah tayi tace "Part d'in Fulani" yace "An gama ranki shi dad'e" murmushi Iman tayi tace kasa kasa "er air se kace gaske na lura kema jinin sarautar nan na yawo kanki kaman d'an hayakin yayanki" ta karasa kasa kasa kaman batayi niyyar fad'a ba, dariya zarah tayi tana cewa itama kasa kasa "Eyyeh Lallai ma matarnan yayan nawa ne kanshi ke hayaki?" Dariya Iman tayi zatayi magana zarah ta d'aura da "ba dole ba kin san aka ce In kazo inda aka san waye kai ka kama ajinka da girman ka sbd bama son raini ya shigo ciki, sannan abinda kika fad'a kaman a kunnen yayana kuwa don wannan sako ne".
Girgiza kai Iman tayi tana waro ido zatayi magana kenan motar ta tsaya, se kuma wasu dogarai suka bud'e musu, fita sukayi zuwa kofan part d'in nennen, Shiru kaman ba me rai a ciki dukda en bukin da suka cika gidan amma ba kowa part d'inta sbd ita bata son hayaniya da yawan mutane a wuri, iso suka nema kuyangarta ta shiga ta nemo izini aka ce su shiga.
Babban parlor ne da ya amsa sunansa kafatanin rayuwar iman zata iya cewa bata ta'ba shiga parlor irin wannan ba, dukda a part d'in ta sauka amma 'bangare daban daga chan baya me karamin parlor da bedroom d'in da suke da zarah, bata karaso nan ba balle ta san ya yake kuma ta chan be cika yawan dogarai da kuyangi kaman nan ba, room d'in dake facing d'insu zarah ta mata jagora zuwa ciki, kamilalliyar tsohuwar na kishingid'e akan tuntu d'akin karan kanshi duniya ne komai na ciki na asalin gidan sarauta ne.
Wasu kuyangi ke mata tausa, murmushi ta sakarwa Iman wadda ya bayyanar da hakorin makkanta me kyau da yalki, hannu ta ma kuyangin suka fice, da sassarfa Iman ta karaso gabanta ta duka se kuma ta fashe da kuka, ita da zarah duk ido suka zubata kan Nenne ta mike ta iso gabanta batayi zato ba taji tsohuwar tayi hugging d'inta wani sihirtaccen kamshi me sanyi da zata ce bata ta'ba jin turare me kwantar da hankali ba irin wannan ke tashi a jikinta.
"Gimbiyarmu meke faruwa ne? Ko wani ne ya 'bata miki?" Kai Iman ta girgiza tace "Kin min abinda duk duniya ba wadda ya isa ya min, kin farantamin kin kankaro darajata a idon en uwana da masarautar nan, ni kuwa nenne me zanyi in biyaki wannan alkhairan naki gareni?" Murmushi nenne tayi kan ta saketa tayi baya kad'an zuwa kan tattausan carpet irin na sarauta ta kishingid'a kan tace "Ba abinda zakimin da ya wuce adu'a tun dana ji labarinki daga bakin Zarah naji wani irin tausayi da soyayyarki ya shigeni, rashin kulawar uwa ba karamin illa bane ga 'ya musamman mace, Ina so ki d'aukeni a matsayin uwa wacce zaki dinga fad'awa damuwarki a ko yaushe kinji?".
Kai Iman ta gyad'a kan Tace "In shaa Allahu Nenne zan ci gaba da yi miki adu'a har karshen rayuwana Allah ya biyaki ya saka miki da gidan Aljannah" da Amin ta amsa, kan ta harari zarah, baki zarah ta zum'buro tare da cewa "aaa ya da harara ni kuma me nayi?" Tace "wayace ki kawota nan, bayan kin san kuna da shirin dinner a gabanku? Oya tashi kuje tayi sallah ku fara shiri sannan ki tabbatar taci abinci".
![](https://img.wattpad.com/cover/243459919-288-k522923.jpg)