🥀NOOR IMAN🥀*Fatima Muhammad Gurin*
•Gureenjo6763 on Wattpad•*'Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)*025*
"Umma, baba kun san ko Iman na da laifi a mutuwar aurarrakinta kun fita laifi da zunubi? Umma aure fah aka ce ba wai zaman kwana biyu ba, baba ko min 'batawar Noor gareku be kamata ku ki ta haka ba, umma, baba idan har kuna son wannan auren na Noor ya zama na karshe kuma ya zamana gidanta na har Abada ku taimaka ku dubi girman Allah kusa mata albarka ko da sau d'aya ne, rashin sa albarkanku kaman shine yake zama jagoran 'bata mata sauran aurarrakinta.
Umma ko da Iman ba 'yar ki bace 'yar kishiyarki ce zaki iya bud'e baki kice Allah ya sanya alheri bare kuma noor dake 'yar cikinki" kasa ta duka Noor ma tayi yadda tayi hawaye na aikin kwaranya daga cikin idanunta, baba da jikinshi yayi sanyi ya kurawa Zarah ido yana kallo, umma kam baza ka gane yanayin da take ciki ba, cikin damuwa zarah tace "Don darajar manzon Allah umma da baba ko da wannan shi ze zama magananku na karshe da Noor ku sanya mata albarka kuyi mata fatan Alkhairi a zaman gidan Aurenta" baba ne ya fara bud'e baki yace "Allah ya sanya alkhairi ya bada zaman lafiya" se ya juya ya fice, umma zarah ta kurawa pleasing eyes d'inta tana kallo, kaman bazatayi magana ba har ta juya zata shige d'aki se sukaji tace "Allah yayi albarka" tayi shigewarta ba tare da ta juyo ba, rungume zarah iman tayi tana kuka sossai.
Da wani irin baki zatayiwa Zarah godiya? Yau zarah tayi sanadiyar samun albarkar ummanta a gabad'aya rayuwanta abinda ta jima sossai tana murd'in samu, 'yan sauran en uwan da suka saura ne d'aya daga ciki ta duka ta d'agota sukayi waje sauran suka rufa mata baya, zarah ma ta mike Anty kalthum ta rike mata hannu tare da bubbuga kafad'anta da d'ayan hannun cikin kasa da murya tace "proud of you lil" murmushi kawai zarah tayi suka fito.
A motar Abba da Anty kalthum ta taho a ciki aka sakata a baya dayake driver ne ya kawo ta yana zaune a mazauninshi, zagayawa Anty kalthum tayi ta shiga, zarah taje ta shiga nata motar suka ja suka fice, direct GRA sukayi a harabar gidan driver yayi parking Anty kalthum ta taimaka mata ta fito kanta kasa suka shige ciki, a parlorn ummu suka dakata.
Zarah ta kalli kalthum, kalthum ta kalleta basu san ya zasuyi ba, sam be dace ta shigo gidan bata je ta gaida ummu ba sede kawai su had'u a jirgi gashi suna tsoron su kaita ummu tayi mata wulakanci, kalthum ce ta yanke shurun da "Iman muje ki gaida Ummu ko" Kai ta gyad'a kan ta d'aga kafa ta fara tafiya gabanta na tsananta fad'uwa, da sallama suka haura parlorn saman, zaune suka hangi ummu ta ci ado na fitar hankali ba wai kwalliya a fuska ba a'a wata arniyar milk da pink less ta saka ta kafa d'auri da d'ankwalin daga abinda yayi wuyanta, kunnenta da hannunta duk gwala gwalai ne In ka ganta zaka d'auka wata matar shugaban kasa ce, farin babban gyalenta na ajiye gefenta da farin handbag se farin flat shoe d'inta.
Trolley d'inta na zaune gefe, idanunta sanye da medicated glass hannunta waya ne tana dannawa, a kasa Iman ta zube ba tare da ta d'ago kai ba tace "Ina kwana ummu?" Shiru ummu tayi kaman bata ji ba, ta sake nanatawa nan ma Shiru, Zarah tace "ummu ana gaisheki" wani banzan harara ta sakarwa zarah kan ta ja tsuki ta mike ta shige d'akinta.
Ajiyar zuciya kalthum ta sauke kan tace "zauna da kyau Iman kiyi hakuri kuma da abinda ummu ta miki sam ba haka halinta yake ba" zarah ma ajiyar zuciya ta sauke kan ta mike "Anty kalthum zanje nayi wanka na fiddo akwatina kan su Abba su shigo, Besty Bari inje In zo ko muje tare kiga room d'ina?" Kai Iman ta girgiza murmushi Zarah tayi kan ta fara tafiya tana cewa "zaki shiga ne ma wata rana".
Shiru Anty kalthum tayi tana tunanin sabon halin da ummu ta fara wadda basu ta'ba gani tanayi ba ko su Mama da yaranta batayiwa wannan hali su da suka nuna basa sonsu karara, Iman ma tunanin Abinda ummun ta mata take Allah sarki mata me mutumci zata 'bata mata rayuwa da tsanarta Ai da ba haka take ba, sau nawa suna gaisawa ta wayar zarah amma yanzu gashi ta shiga tsakanin d'a da uwa.
![](https://img.wattpad.com/cover/243459919-288-k522923.jpg)