BABI NA TAKWAS

2K 152 3
                                    


                 🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
            •Gureenjo6763 on Wattpad•

*'Yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

                       *08*

A d'an tsorace ta mike tana kallonshi ita har ga Allah tana class d'inne kawai amma bata san me ake ba, tunaninta na ga irin wulakancin da ta sha a wurin baba yau da safe, har marinta yayi sbd abunda ya faru a gidan inna jiya, hakan yasa kwata kwata duniyar ya fice mata a kai, har tunanin irin matakin da zata d'aukarwa rayuwanta take.

"Yes!! What did I said it's Fungi in hausa?" Ya kuma jefo mata tambayar a karo na biyu, nan ma Shiru tayi hakan ya sa ya tabbatar da cewa gangar jikinta ne kad'ai a class d'in hankali da ruhinta sam basa jikinta.

Tsallaketa yayi ba tare da ya kuma kallonta ba yayi pointing wani ya bashi amsa, be kara bi ta kanta ba ya ci gaba da abinda ke gabanshi wadda hakan yasa ta zamewa ta zauna kanta a kasa, hannun zarah taji a nata hakan ya sata maida hankali kanta, girgiza mata kai tayi a hankali tace "sorry, karkiyi kuka" murmushi ta sakar mata ita wannan be kai ya sata kuka ba sam.

Aiko cigaba da tunanuka nayi har ya fita ban ma sani ba, hayaniyar da class d'in ya d'auka ne yasa ni dawowa cikin hankalina Ina kallon zarah dake ta kallona ban san dalili ba nace "wai har ya fita?" Hannuna ta kama muka mike muka fita ba tare da ta furta komai ba, har seda muka samu wurin da ba mutane sossai tukuna ta dakata, "wai me ke damunki ne haka besty? Wallahi ko makaho ya shafa fuskan nan naki ya san kina cikin damuwa kar ki kuskura kicemin ba komai, jibeki? Duk a birkice!!".

Hawaye ne ya cika min ido a zuciyata nace "baza ki gane bane" amma a fili se na kwakwulo murmushi nace "ba fa komai besty, kinga muje ki koyamin abinda akayi a class yau, kan 11 muyi Botany" zatayi magana na ja hannunta Ina sakin murmushi, ba yadda ta iya haka ta bi ni, muka koma hall d'in da mukayi lectures yanzu, ba mutane dayawa hakan yasa muka samu wuri muka zauna ta hau min bayani In taga kaman zan tafi tunani se ta san yadda tayi ta hana.

It is really fun zama da zarah tana da wani baiwa da Allah ya bata wadda baza ka ta'ba zama da ita bata saka farin ciki da nishad'i ba, ba ta da girman kai irin na yaran masu kud'in zamanin nan sam, 11 na yi mukayi second lectures d'inmu zuwa 1 tukun muka fito.

Seda nayi sallah kan na fito don gidan hafsy dake low cost zani, tuni zarah ta wuce, cikin natsuwa ta nake tafiya ina yaki da zuciyata wajen hanashi fad'awa tunanin da ze sani yin wani shirmen akan titi don na saba, a kasa na dinga tafiya har bakin gate kan na samu adaidaita na hau tare da fad'a mishi inda ze kaini.

Bamu fita layin BUK road ba wani ya tare me napep d'in dama ba shata na d'auka ba sbd bani da kud'in yin hakan mussaman irin napep na kano, wani fitinennen kamshi ne ya min sallama, wadda har seda ta sani lumshe ido na bud'e a hankali, dukda raina na bani in kalli me wannan kamshin amma ego na ya hana seda naji husky voice d'inshi na cewa "sallamu alaikum" ni da me napep d'in muka amsa, a lokaci d'aya.

Idona na sauka cikin nashi nayi saurin kawarwa na mayar kan titi, "low cost nayi" me napep d'in yace "fad'uwa ta zo daidai da zama muma chan mukayi" be kara magana ba se faskekiyar wayarshi da ya fidda ya fara dannawa, cikin seconds naji yana amsa call "yes plz kazo BUK road gefen wani mini super market zaka ga mota ta a wurin, na shiga na siya abu se kuma ta ki tashi, the key is with the securities just collect it there".

Ban ji me aka ce mishi a d'ayan 'bangaren ba se de naji yana godiya tare da kashe wayan, Shiru shiru ko motsin kirki banayi har muka kusa isa, shi kuwa ta 'bangarenshi kallo d'aya ya mata ya tabbatar ya samu irin macen da yake so, don tayi mishi d'ari bisa d'ari ga natsuwa da ya lura tana da shi.

Don sam ta kasa sakewa ji tayi ya cika mata ido sossai, ganin har ga Allah ba ze iya barin wannan daman ta wuce shi bane yasashi cewa "sunana Muhammad bashir ana ce min hammad and yhu?" Bata tabbatar da ita yakeyi ba seda ta kalleshi taga ba waya yakeyi ba, se ma murmushin da yake ta sake mata har fararen hakwaranshi na bayyana.

Itama murmushin tayi kan tace "Noor Iman" yace "wow nice name amma ba asalin suna bane ko?" Kai ta gyad'a kan tace "asalin Saudah" wani murmushi me sauti ya saki yace "sunan manya, sunan mom d'ina fa gareki" murmushi kawai tayi, a take ya ci gaba da janta da hira duk ta kasa sakewa har suka isa daidai inda zata sauka, ta cewa me napep d'in "zan sauka a nan" da "Toh hajiya" ya amsa tana shirin sauka taji Muhammad yayi saurin cewa "Noor Iman".

Waigowa tayi se taga waya yake miko mata at the same time yana murmushi yace "samun number d'inki plz ma dinga gaisawa" d'an Shiru tayi tana kallon wayan seda ya kuma cewa "dan Allah" kan ta kar'ba ta saka mishi, "thanks" yace bayan ya kira yaji ringing d'inshi a jikinta, umarnin tafiya ya ba me napep d'in don yaji tana shirin bud'e jaka don d'auko kud'i.

Girgiza kai tayi bayan wucewarsu kan ta nufi karamin kofan gidan hafsyn da sallama ta shiga a tsakar gida ta ga maman mijinta zaune tana cin goro, dukawa tayi ta gaisheta, amsawa tayi tana me kare mata kallo har Noor ta dunfari parlorn hasfy taji matar nan tace "tsaya wannan ba yayar hafsatu sarauniyar zaurawa ba? Me aure aure da ta kasa zama sbd bin maza ya bi jikinta?".

Wani irin bugu zuciyata tayi a lokaci d'aya naji Ina shirin dena gani da kyar na iya juyawa na kalleta nace "itace de, sede kar masu fad'in hakan su manta kaddara ce tana kan kowa kuma bata fi karfin kowa ba, an haihu de" salati matar ta saka, ko karasa sauraron salatin nata banyi ba na fad'a parlorn hafsa kujerar da ya fi kusa dani kawai na samu na zauna a kai Ina dafe kirji.

Abubuwa sun min yawa har ga Allah sede In na tuna Allah baya d'aurawa bawa abinda yafi karfinshi se ince "Astagfirullah wa atubu ilaih" amma Ina tunanin zuwa yanzu akwai abinda ka iya samun zuciyata don kiris ya saura ta tarwatse gabad'ayanta, "Yaya Noor ce, sannu da zuwa" muryan hafsy ya katse min bakin cikin da nake ciki murmushi na kwakulo ganin yadda take fara'a nace.

"Nice Hafsy fatan bakiyi fushi dani ba, wallahi tunda kikayi 'barin nan nake ta sa ranan zuwa dubiya Allah be yi ba se yau, Allah de ya kiyaye na gaba ya baki me anfani" tana murmushi tace "ba komai wallahi yaya noor, na gode Ai yanzu da lokacin ma duk d'aya ne tunda de kinzo. Bari na kawo miki ruwa" ta mike ta fice chan ta shigo ranta ba daad'i hannunta d'auke da katon faranti me d'auke da plate d'in jollof da ruwan pure water guda biyu.

Da mamaki nace "Lafiya kuwa hafsy?" Murmushi tayi wadda daga gani na san na yake ne tace "ba komai, ya su mama da umma? Ya school?" Kan na bata amsa se ga uwar mijinta nan da mijin shi kanshi, "au wato da nace kizo kice mata ta fice min daga gidan d'a shine kikayi biris da maganata ga shashasha nan ko? Asararriya irin wannan ballagazan yar taki".

Cewar uwar mijinta, da sauri hafsy tace "a'a hajiya wai dama nace ko ruwa ne tasha kan ta wuce, daga makaranta take kuma dubiya da jajen 'ba...." da tsawa mijin ya katseta "Hafsah da uwata kike ja In ja? Lallai ashe hajiya gaskiyanki ne wannan yar tata munafuka annamimiya itace ke shirin fara hure mata kunne amma ba haka take ba".

Kuka hafsa ta fara da sauri na mike na d'au jakata Ina danne hawayena nace "kuyi hakuri In shaa Allahu bazan sake zuwa ba bare har na hure mata kunne, hafsy dan Allah kiyi hakuri" a sama sama nake jin muryan habu yana cewa "gwara kam, kuma wallahi hafsat kika bari wanchan tsohuwar guzumar ta kara shigomin gida ba tare da izinina ba a bakin auren ki, zan kira baban don ki tabbatar uwata tafi ta kowa ta bada tarbiyya me kyau ga duka 'ya'yanta ba'ayi watsatsiyar da zata shigo ta zageta ba".

Innalillahi wainna ilaihi rajiun, Allah Astagfirullah, Allah ka dubeni, shine abinda nake ta nanatawa Ina tafiya ban san ya baba ze yi dani In yaji maganan nan ba, da ma ban zo ba, horn d'in mota da na dinga ji a bayana ne yasa ni dakatawa na kuma yi saurin goge fuskana da yayi cha'ba cha'ba da hawaye, "Noor har kin gama ziyarar?" Juyawa nayi ina kallon shi, hammad ne zaune cikin wata white Mercedes murmushi na kakalo nace "Eh" yace "Ohk shigo plz na kaiki gida" Kai na girgiza "a'a zan hau napep na gode".

Kafewa yayi, a yanayin da nake cikin nan bani da wani karfin yin musu da shi hakan yasa na bud'e gefen me zaman banza na zauna yaja yana tambayata "wace unguwa?" Nace cikin sanyin murya "gandun albasa" tafiya mukeyi Shiru shiru kan yayi breaking silence d'in da cewa "Damuwa da tunani be dace da kyakyawar fuskar nan ba sam".



                        🖤Gureenjo🖤

NOOR IMANOù les histoires vivent. Découvrez maintenant