🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
•Gureenjo6763 on Wattpad•
*'Yar mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*01*
Tafiya kawai nakeyi sam ban san inda nake jefa kafafuna ba bare na kula da hanya, hawaye kawai ke kwaranya daga cikin kwarmin idanuna zuwa kan kumatu na.
Tsananin damuwan da nake ciki bai sa na kula da kan hanya na jefa kaina ba sai da naji wani wawan bugu yayinda students na arean suka saki salati wasu na ihu, runtse matsakaitan idanuna nayi cikin jin zafin bugun tun daga ƙafata har tsakiyar kwakwalwata amma ko kad'an zafin bai kai na zuciyata ba.
A hankali na waiga na ƙurawa bakar meserati wadda gabad'ayanshi baki ne har glasses d'in ido don ganin ko zai fito ya ba ni hakuri amma ko motsi kofan motar bai yi ba bare ayi alamun bud'ewa.
Miƙewa nayi na d'ingisa kafana da nasan yayi mugun buguwa na koma gefe na zauna, wasu na min sannu wasu kuma cewa suke Allah ya kara dama yarinyan kullum tana tafiya kaman mahaukaciya sam bata da hankali a kanta mai makon a kaita psychiatric amma an kawo ta nan makaranta ko me zata d'auka oho.
Kuma runtse ido na nayi ba su kad'ai ba duk inda zan gilma sau d'aya sau biyu zasu ce psycho ce ni ba wai dan wai yanayin shigar jikina ba, a'a tsantsar rashin natsuwa da damuwan dake d'auke a yanayina da fuskata ke sa su zaton haka duk da sanyi na a abubuwa dayawa.
Sautin wucewar motar da speed shi ya dawo dani daga duniyar tunani na, kafana na riqe da zarazaran yatsotsin hannuna na dinga matsawa har naji dama dama amma na tabbatar akwai matsala jin irin azabar dake shigata.
Agogon dake d'aure a tsintsiyar hannuna na kalla 7:50 ajiyar zuciya na sauke kan na mike na ci gaba da tafiya a hankali Ina d'ingisa kafan na nufi auditorium sbd achan nake da lectures karfe takwas gashi yanzu 7:50.
Ban isa auditorium ba sai takwas da kusan mintuna takwas, hall d'in tsit kaman anyi ruwa an d'auke a hankali na tura kofan na shiga bakina d'auke da sallaman da iyakarshi lips d'ina a hankali na ci gaba da takawa da nufin karasawa ciki In samu wurin zama.
Sai da nayi tsakiyar hall d'in kan naji an ce "Who the hell did yhu think yhu are?"
Na ɗago na kalleshi idanunmu suka sarƙe, motsa baki nake kokarin yi in ba shi haƙuri amma komai ya kasa fita.
Ya sake daka wata tsawar
"Will you get out of my class jor" sam muryanshi bata da hayaniya dukda tsawa yayi ba don microphone da yake amfani da ita ba ko rabin ajin baza su ji tsawar nashi ba bare lectures d'inshi.
Juyawa nayi na mishi kallo d'aya yayinda shi kuwa idonshi ke kan damin lecture note d'in hannunshi.
'Fa tabarakallahu ahsanul khalki' na furta akan lips dina ban kara gangancin kallonshi ba na juya na fita a sanyaye still cikin d'ingishi kujeru irin na zaman d'alibai dake gaban hall d'in na samu na zauna Ina sauke ajiyar zuciya.
A rayuwana ban ta'ba ganin namiji mai irin kyaunshi a fili ba sai dai a tv, tv d'inma sai tashoshin larabawa ko indiyawa kwata kwata ban san yadda zan fasalta kyaun shi ba illa iyaka abin da zan cewa Allah ya yi halitta na san yana da bala'e'en kyau ga fari mai d'aukan hankali, ga dukkan alamu idan ba bafulatani ba to buzu ne ko ma ba ɗan ƙasar nan ba.
Share tunaninshi nayi saboda damuwana ya fi karfin tunanin kyaun wani halitta, ya zanyi da rayuwata, wai laifin me na aikata da ake hukunta ni da abin da ban san hawanshi ba bare saukarshi? Why always me? A shekaruna na 23 a duniya nayi aure sau hud'u duk ba wadda na mishi kyakyawar wattanni biyar.
Yes inada kyau daidai misali amma kyauna ba mai d'aukan hankali bane sbd fata me duhun haske ce dani wato 'chocolate' color ba kallo d'aya zakamin ka fahimci kyaun da surar da Allah ya bani ba shiyasa tun ina shekaru sha takwas a duniya samari suka min rutututu kowa so yake ya mallakeni.
Ashe ni kam maza sune kaddarata, ganin kullum za'ayi sallama ace ana kiran Noor Iman yasa baba na yanke shawaran In fidda miji ya min aure.
Dukda bana so har raina saboda burina shine in yi karatu ba aure ba, amma ban samu wani zaɓi ba kasancewata me tsananin biyayya yasa na fidda wani saurayina da ya nace min tun Ina jss class ba 'bata lokaci a randa na cika sha takwas cib a ranar aka d'aura min aure da bello sai dai takaici da tashin hankali a ranar da aka kaini gidanshi a ranar Bello ya dankara min saki har uku ba tare da na san laifina ba.
Cikin tsananin tashin hankali na dawo gida da safiyar ranan babu wanda ya ba ni listening ear ko ya jira jin ba'asi babana da 'yan uwanshi suka rufu akaina da duka, ba don mama ba 'yaddiko na, wato kishiyar mahaifiyata' da ina ga ban yi rai ba a ranar.
Baƙaƙen maganganun da na sha ko sai da nayi dana sanin zuwa na duniya dayawa suna cewa rashin kai budurcina gidan mijina yasa ya min wannan wulakncin yayinda maganan yayi tasiri akayi ta yad'ata unguwa da 'yan uwa.
Ba nan gizo ke saƙar ba don ko kallo ban ishi umma na ba, bare sannu ko kuma ta ajiye ni taji damuwata hakan yafi komai yimin ciwo a rayuwa ban san daad'in uwa ba, ban san abinda ake cewa uwa ba a kaina kam sai dai Ina ganin yadda take kula da kannena kaman zata maida su ciki.
Abun na min ciwo fiye da tunanin me tunani, mutuwar aurena na farko yayi sanadiyar tashinmu a rijiyar lemu, muka koma gadon kaya da zama sbd ban isa fita ba haka 'yan gidanmu, Babana na matukar sona kan faruwan mutuwar aurena na farko, wani irin so yake min da ban san iyakarshi ba.
Saboda irin tsananin tausayin da nake bashi, komai sai dai kishiyar uwata ta min, tun Ina karama umma ke banzantar da ni wai ita alkunyar 'yar fari a yadda baba ya fad'amin kenan amma har yau ban yarda ba sbd abun yayi yawa.
Ban san kula ba sai a wurin mama, ban san yadda ake shagwa'ba a gaban uwa ba se a gabanta, ban da wanda zan kaiwa kuka na sai mama, da farin cikina da bakin cikina duk tare muke rabawa sai ma ince ta fini shiga damuwa akan mace macen aurena.
Hayaniyar d'alibai masu fitowa daga auditorium hall ya tabbatar min da an gama lectures d'in, d'ago idon da zanyi sai suka sarƙe cikin nashi a karo na biyu a yau, ko second idonshi be yi a kaina ba ya manna baƙin space akan sparkling brown eyes d'inshi tare da nufar motanshi cikin takun isa da kasaita, jarumta da kuma karsashi. Sai a lokacin na gane ashe wadda ya kad'e ni a hanyar shigowata shine lecturer d'inmu na yau.
Kallonshi nake yadda farinshi ke d'aukan ido ga baki wuluk d'in gashin kanshi dake kwance lublub har kasan keyanshi sai sheki yakeyi, irin gashinne cike da girarshi haka su ne gargasan dake kwance a hannunshi zuwa saman kirjinshi da ya fito kad'an sbd V neck black shirt da ya saka.
Ina mamakin wannan bawan Allahn anya d'an ƙasar nan ne? Bakaken kananan kayan dake sanye a jikinshi ya kara fitar da farin fatarshi, kananan maganganun da d'alibai suka fara akanshi ne yasa ni kauda kaina daga kallonshi na mayar kasa Ina me kokarin sake zundumawa duniyar tunani na naji an zauna gefe na.
A hankali na waiga sai naga wata kyakyawar matashiyar yarinyar da tunda na fara zuwa makarantan take yawan ce min sannu bayan ita ban ta'ba magana da wani d'an ajinmu ba, alhalin Ina cikin sati na hud'u kenan da na fara zuwa makarantan ta BUK inda nake karantar B.sc Ed Biology.
"Sunana Zarah Ahmad Malabo and you?" Da kyar na iya yi mata yake don murmushi wahala yake min nace "Saudah Hafeez ana kirana Noor Iman".
*•Assalamu alaikum 'yan uwa ga fah Gureenjoh da sabuwar littafi hope zaku so shi kaman sauran books d'ina, promise yhu will never regret reading my book, in shaa Allah, comments for more pages•*
🖤Gureenjo🖤
