🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
*Gureenjo6763 on wattpad*
*'Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*this page is dedicated to you my deedi just want you to know that I love you and I will always be with you, take your side no matter what the situation is, you are such a wonderful and strong woman, you should stick in that love🥰🥰, you are the best sister ever and will always be*
*054*
Bayan kwana uku
A cikin kwanaki ukun nan masarautar modibbo Adama ya shiga wani irin yanayi da zasu ce sun manta rabon da abu makamancin haka ya faru, yau akayi sadakar ukun baba galadima da umma dukda dae dayawa har an fara mantawa da rasuwan biyu ne ba d'aya ba, duk wadda ze yi gaisuwa sede yace "Allah yaji kan galadima ya mishi rahama" Tun dawowan Abdul ya sa aka chanzawa nenne petel d'aki ya kuma janye ummu daga kan Hamna ta koma kan mahaifiyarta shima kuma anan yake yini yana bata baki Don ya lura tana cikin damuwa tun bayan da nenne petel ta farka sau d'aya mistakenly wata baiwa ta kawo musu abinci ta mata gaisuwan baba jikin ya kuma rud'ewa tun jiya da safe har yanzu bata farka ba.
Abdul yayi masifa kaman ze ari baki, me martaba da modibbo suna zuwa ko wani dare su dubata yayinda su iman sede suzo fisha su fice, dukda yana bukatan lokaci da matarshi amma ba yadda ya iya yanzu ummu tafi bukatarshi fiye da kowa se dare ya tsala yake komawa part d'insu a hakan ya kuwa taimakawa ummun sossai.
Kaman yau bayan sun dawo daga asibitin bayan tayi magrib tana azkar taga kiran ummanta na shigowa bata d'aga ba seda ta jira ya tsinke tukun ta kirata back tana d'agawa tace "ummanah Ina kewarku" umma daga 'bangarenta tace "khaih mamana yanzu sallaman taki kenan?" Baki ta tura gaba tace "ummah Assalamu alaikum" murmushi umma tayi kan tace "wa'alaikissalam ya kuke? Ya ummunku da hakurin rashi?" Tace "Alhamdulillah umma d'azu naji kunyi waya ko?" Umma tace "Ina ruwanki" kuma turo baki gaba tayi cikin shagwa'ba tace "shikenan ummah babu, Ina su ikhram Ina missing d'insu wallahi, d'azu hafsy take ce min ta shiga satin haihuwanta ko? Ni kam umma kuna waya da maman Abulkhairi kuwa ya jima ina son tambaya se in sha'afa kullum In na kira wayanta baya shiga".
Ajiyar zuciya umma ta sauke Tace "yanzu fisabilillahi wanne kike so in amsa miki? Ni kiran da na miki daban kin wani cika ni da surutu" dariya tayi tace "Toh Ina ji ummanah me ya faru?" Umma tace "ni kam ko kun ta'ba waya da babanku tunda suka tafi? In na kira layinshi baya shiga" da mamaki tace "Ina suka tafi?" Umma tace "ee bakuyi maganan da maigidanki bane? Na zata ya fad'amiki yasa bamuyi maganan ba ai tun randa akayi rasuwan nan suka wuce da safe zuwa ganin likita da mamanku".
Shiru tayi tana mamaki a hankali tace "bamuyi maganan ba, In ya dawo In Shaa Allahu zan mishi magana watakila suna waya" Umma tace "Toh shikenan, maman Abulkhairi sun tafi kauyen su mijinta daga baucin ya d'an kwana biyu sbd rashin lafiyar surukarta, su ikhram suna gaida ke" Tace "Ina amsawa ummahna itakuma surukarta Allah ya bata lafiya, se da safe ummah" sukayi sallama ta kashe wayan.
Ta jima zaune tana tunani Allah sarki duk wani ups tackles na rayuwanshi baya mantawa da ita da family d'inta wani irin sonshi take ji wadda ya wuce misali se yanzu take gane ashe tun kallon farko da ta mishi ne sonshi ya mata mummunan kamu, wani irin bukatan mijinta take abinda yayi mugun bata mamaki, a haka ta lalla'ba tayi isha kan ta kwanta nan kan sallayan ta takure, ita ba bacci ba ita ba ido biyu ba gashi ta kashe wuta, ta jima sossai kwance d'akin har bata san iya adadin lokutan da ta d'auka ba se jin motsin kofa tayi alamun za'a shigo bata damu ba sanin ba me shigowa se shi tana nan kwance bata motsa ba har aka shigo cikin d'akin tana de kallon inuwan mutum tsaye yana dube dube, murmushi tayi taki magana kaman kuwa ya san itace nan yayi wurin sallayan sede tun daga tafiyan ta fara kokonton anya wannan shine? Don tafiyanshi ba haka yake ba, bata gama tunani ba taji ana shafata kamshin ba namijinta bane da hanzari ta mike tana buge hannun tace "wayene?" Muryanta na rawa.
