🥀NOOR IMAN🥀*Fatima Muhammad Gurin*
*Gureenjo6763 on wattpad**'Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)*055*
"Tumors as you can see here" ya mika mishi wani X-ray "tumors are masses of abnormal cells in the brain it can be on spinal cord, that have grown out of control, it can be between benign (non-cancerous) or maligent tumors (cancer) the main concern about it is:- 1- how fast they grow
2- how readily they spread through the rest of the brain
3- where they are located
4- if they can be removed or destroy and not come back"Katseshi Iman tayi da cewa "hope hers is non-cancerous" a rud'e cikin taradaddin amsan da baturen likitan ze bata, murmushi ya mata kan yace "yes hers can be easily destroy, ur mom will gonna be fine soon don't worry" kallon Abdul yayi kan yace "she has small amount of diabetics that's hyperglycemia, the diabetics met with the tumors and all are dangerous diseases that lead to coma that's why it would be difficult to many doctors to figure out the exact problem" ajiyar zuciya ya sauke yana kallon iman da ta dafe kanta kallon doctorn ya kuma yi yace "please do anything that can make her better from those diseases especially the brain tumor" Kai doctorn ya gyad'a cike da gamsuwa yayi en rubuce rubucenshi ya mika musu wasu papers ganin akwai sa hannu ya mikawa baba da yaji dukkan bayanan da akayi hannu ya saka aka ba doctorn ya kuma basu wani abubuwan da zasu bukata daga pharmacy bills d'in na kasa, ba tare da Malabo ya yarda bappa ya gani ba ya mike yana mikawa doctorn hannu suka fice.
Duk yadda baba ya so ya biya ko kad'an daga cikin abubuwan da yake kashewa ne malabo yaki, haka ya biya komai da komai ba 'bata lokaci aka fara treating mama, satinsu biyu a miami seda ya tabbatar an gama komai saura jiran farkawan Mama tukun suka fara shirin wucewa, a sati biyun nan ba wurin shakatawan da basuje ba na cikin garin miami, Florida state of united state, daga kan Miami Beach, Art deco historic district, south beach, vizcaya museum and gardens, Everglades national park.
Yininsu chur a bayside market place in da ya kasance large outdoor style mall dake cikin ruwa with more than 150 shops and restaurants sunyi sayayya har na hauka duk wani shiga na turawa wadda baze bayyana jiki ba seda ya saya mata da mahaukatan nighties a sati biyun nan wani irin mahaukacin soyayya sukayi da ya zauna daram a cikin zukatansu so, shakuwa, kulawa, zallar ruwan kauna shi suka nunawa junansu.
Restaurant yafi kala goma suka je daban daban a areas daban daban wasu a cikin ruwa kai sune har night club a cikin boat sukayi tasha mamaki taga ikon Allah bata ta'ba zaton akwai irin wuraren nan a duniya ba, sune har bay-front park suka ga su light tower da dare, karshen inda suka je shine zoo Miami inda ya ke d'auke da over 3,000 wild animals itade ba dabban ubangiji da bata gani ba, har getto area d'insu da yake d'auke da wynwood walls street art suka zaga inda taga mutane masu ban mamaki mata da maza kowa da zane daga kai har kafa na tattoo.
Anan ta samo wani saffron grills inda suke Gasa duk wani abun ruwa wayyo Ai kullum se sunyi ordern wani abin na ruwa taci, dukda sauran abincinsu ma duk ba laifi taci a heshi and sushi Asian cuisine, santorini, havana vieja, numfashinta seda ya kusa d'aukewa ganinta a freedom tower gashi cikin dare wayyo bazata iya fasalta yadda wurin nan yake ba se wadda yaje, Tabbas ta yarda da inkiyoyin miami da ake ce mishi "magic city", "gateway to the Americans", and "capital of Latin American" Don har d'an yaren Latin d'in ta koya.
Ya jata har cikin university d'insu inda yayi visiting wani friend d'inshi, in takaice muku Noor Iman kam ta zama wata baturiya cikin sati biyun nan tayi fresh ta kara kyau da murjewa wasu wuraren suna d'an zuwa da baba kaman day trip key west with boat sunje dashi wasu wuraren kuwa kud'i kawai yake bayarwa d'an gidanshin nan su fice da baba yaje duk inda yake so.
![](https://img.wattpad.com/cover/243459919-288-k522923.jpg)