🥀NOOR IMAN🥀*Fatima Muhammad Gurin*
•Gureenjo6763 on Wattpad•*'yar mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)*09*
"Noor magana nayi baki ce komai ba, ko zan iya sanin damuwanki? In da hali In magance miki?" Nan ma Shiru tayi, kaman bazata ce komai ba se kuma tace "damuwana yafi karfin tunaninka, ba me iya magance min ita se wadda ya busan numfashi" Shiru ya ratsa na mintuna kan yace "hkne but komai Ai yana da sila, I understand sbd baki sanni bane yasa bazaki iya fad'amin damuwanki yanzu ba.
But with time zan san me ya dameki nima zaki san me damuwana, sbd alaka ta har abada nake son kullawa dake, kallo d'aya na miki na tabbatar na samu irin macen da nake so kab duniya, Ina sonki" wani irin bugu da zuciyarta yayi seda tayi tunanin ze iya ji, inaaa bata shirya ba, bata shirya wani tozarcin ba, ba ta yadda za'ayi tayi aure yanzu wallahi.
Cikin rawar murya tace "a'a kayi hakuri dan Allah ka nemi wata" hankalinshi kwance yace "ni ke nake so ba wata ba, bazan rabu dake ba se kin ban kwakwaran dalilin yin hakan" Kai tsaye tace "ni bazawara ce" d'an Jim yayi kan yace "hakan ba dalili bane" dukda he was not expecting that, "aurena har hud'u ba d'aya ba" waro ido yayi yana kallonta har be san sadda yayi losing control ba tare da bumping wata bakar mota dake gabanshi.
Birki ya taka tare da sakin ajiyar zuciya, ba 'bata lokaci ya bud'e motar ya fita don yayiwa na gabanshi 'barna kad'an, tana nan zaune taga de yana knocking glass d'in motar ta gabansu, kuma taga an bud'e bata ji me suka tattauna ba, ta de san maganan da sukayi bata wuce na minti biyu ba, taga wanchan d'in yaja motarshi yayi gaba, bud'e kofan da hammad yayi ne yasata kallonshi har seda ya zauna kan ta d'auke kanta.
"Dan Allah ban son wasa Noor kinga abinda kika ja sbd kawai kina so in rabu dake se kicemin aurenki hud'u da kananan shekarunki?" Shiru tayi don baze fahimta ba, amma tana fatan yana ajiyeta a unguwansu a tare shi a bashi labari, nuna mishi hanya ta d'ingayi har kofan gidansu, "na gode" shine kawai abinda ta furta kan ta sa Kai ta fice, Ai ko de kaman yadda tayi tunani be fita a unguwan ba aka tareshi aka bashi labarinta na karya da gaskiya wadda yasa shi fita cikin natsuwarshi, gashi Allah ya sa mishi sonta farat d'aya a ranshi.
Ze 'boyewa mom don ya san In har ta sani bazata ta'ba yarda ya aureta ba, gashi shi kuwa baze iya rabuwa da ita ba, gida ya nufa da nufin yayi tunani ta yadda ze shawo kan mom kan tayi bincike, don haka take In har d'anta ze yi aure da kanta take bincikar halin surukarta da yanayin gidansu, sede kash yana parking mom na fitowa.
"A'a hammad ya na ganka haka? Me ke damunka?" Shiru yayi na mintuna kan yace "mom ba ko..." katseshi tayi "kul karka kuskura yaushe muka fara wasan haka da kai, zaka fad'amin ko se ranka ya 'baci?" Dayake Allah ya halliceta da son nata gata da zafi bata yarda komai ya samu d'anta bata d'au mataki ba, ba yadda ya iya hakan yasa yace "na samu matar aure".
In disbelief take kallonshi kan ta sake murmushi tana cewa "Toh shine abun tada hankali? Kode tsoron gayamata kake In shige gaba don na sanka da tsoron mata" murmushi yayi yana gyad'a kai, tace "toh ya sunanta? Kuma wani unguwa take?" Ko yayi karya se ta gane don ba halinshi bane "sunanku d'aya amma ana kiranta 'Noor iman' unguwansu kuma gandun albasa.
Tana murmushi tace "masha Allah, ka san tsari na, kar naji maganan nan a bakin mahaifinka ni da kaina zan gayamishi" sawa ranshi kawai yayi ya rasa Noor don In har mom taji abinda yaji Toh kuwa baze ta'ba aurenta ba ko mutuwa yake yana farkowa, amma kuma ance Ai ba abinda yafi karfin Allah, da wannan tunanin ya wuce part d'inshi.
*********
Tassss Tass taji saukan mari akan kuncinta hagu da dama a razane take kallonta, Umma!!! Bata ta'ba shiga harkata ba se yau, bata ta'ba d'aga hannu da sunan dukana ba se yau, "ana cewa baki da hankali da natsuwa ban ta'ba yarda ba se yau, Toh bari kiji bazata ta'ba sa'buwa ba yadda kike kashe aurenki sbd iskanci irin naki ki kashewa 'ya'yana ba, wallahi ki kiyayeni ba abinda bazan iya miki ba In har kika kuskura auren 'ya'yana yayi rawa ta dalilinki, su ba gur'batattu bane sun san me sukeyi" kan baba dake zaune gefe ta maida kanta.
"Ka jawa 'yar ka kunne Hafeez Wallahi tallahi ta kara taka kafanta zuwa gidan 'ya'yana zan yi mugun bata mamaki" bata jira cewarshi ba ta juya ta fad'a d'akinta, da kallo baba ya bi ta kan ya maida idonshi kaina, ina tsaye ne kawai amma wallahi zan iya rantsewa jini be tafiya a jijiyar jikina, i am more than shock da kalaman umma, nafi mintuna biyar kan naji zuciyata ta fara bugawa da karfi tana wani irin zafi, wasu zafafan hawaye suka fara rolling a idonanuna da kyar na taka zuwa d'akin mama, baba de be ce min komai ba se kallona da yakeyi har na kule.
Mama bata nan hakan ya bani daman fad'awa kan gadonta na fashe da wani irin kuka me ban tausayi, me tayi ne a duniyanta da take fuskantan irin wannan bakin rayuwan? Wani laifi ta aikata haka me girma da yake hunting d'inta like this? Innalillahi wainna ilaihi rajiun uwa de da ta haifeta a cikinta, ta raine ta na wata tara tasha wahalan nakuda amma shine take mata haka?.
Me babancin dake tsakanina da 'yan uwana da har za'a fifita su sama dani? A kuma raba tsakaninmu, me nayiwa umma ne?? Da irin wannan tunanukan take kuka tambayoyi ne fal a raina akan rayuwata sede banda wacce zan iya tambaya, sede tayi kuka me isanta kan ta mike ta fad'a toilet tayi wanka, seda ta fito daga wanka kan taga mama murmushi ta kakalo tace "sannu da dawowa mama".
"Yauwa Iman lafiya kuwa na ganki wata iri" ba tare da ta kalli maman ba tace "Lafiya bacci na d'anyi" girgiza kai kawai mama tayi don ta san ba haka bane, kallo ta dinga binta dashi har ta shirya cikin normal English gown tare da zura hijab, seda ta tada sallah kan maman ta d'auke kanta daga kallonta, tana nan zaune har ta idar da sallah, ta juyo tace "me za'a d'aura mama?" Mama tace "babanku ya kawo aleyaho se kiyi miyan da tuwon shinkafa" da Toh ta amsa tana mikewa da hula a hannu ta fice.
***********
"Ai rayuwar gidan Abdul ba karamin gyara bane a cikinshi, da wannan matar tashi da da ita da babu duk d'aya" cewar Anty Rumah kanta na kan bama d'anta Arfat nono, Kallon Abdul d'in dake kwance kan doguwar kujera Kalthum tayi tana son yin magana tana tsoron kar ya zageta amma ganin idanunshi a lumshe kaman ba magananshi ake yi ba yasa ta cewa.
"Wallahi kau Anty Rumah baki ga da na shiga gidanta da safe ba, ko wurin zama na kirki babu tsabar tarkace da datti, wai da na mata magana shine take neman yi min rashin kunya kaman ba shekara na bata ba" Hamma Hafeez yana dariya yace "Toh sarauniyar son girma, amma Ina suna da namiji cleaner?".
Zarah da ta fito daga kitchen hannunta d'auke da tray da cups na smoothie akai flavor kala kala dayake kowa da irin flavorn da yake so, tana ajiyewa tace "hmm ina ko ze iya zama da masifan Anty hamna" Anty Rumah tace "Da gwara macece ma amma Ina shegen kishinta na tsiya ze iya bari ta nemi me aiki mace", Hamma Hafeez kai tsaye yace "Da nine Abba wallahi aure zan karamishi" Anty Rumah na dariya tace "Se kace baka san halin gayen ba? Ai ko Abban ne se yaga dama ya amshi matan, balle kuma kai da kace da kai ne, Ai magana ta 'baci".
Zarah tace "Da kuwa na za'ba mishi nitsatsiyar matar da babu irinta" kaman daga sama sukaji muryan ummu tana cewa "Lallai yaran nan kun cika, Yanzu fisabilillahi akan 'yar uwarku kuke irin wannan mugun fatan? Kar fah ku manta da ni da uwarta uwarmu d'aya ubanmu d'aya, to bari kuji in fad'a muku hamna ita kad'ai zata zauna a gidan Abdulraheem In har na isa dashi, kuma kuyi ku tattara ku fice min a gida tunda kune masu hure mishi kunne.
Shima In ba shashasha ba taya za'ayi ya zauna kuna zagin matarshi yana ji be kare ta ba, to Abdulraheem kajini da kyau In har Ina numfashi matarka d'aya hamnah" daga bakin kofa sukaji Abba yace "A'a Rashida Ina miki rantsuwa da Allah a yau Babana ya kawo wata macen yace yana so in aura mishi, Toh fah se inda karfina ya kare, Allah ne fah ya bashi daman zama da mace fin d'aya In har baya jin daad'in na farkon, karki zata ban san duk halin da yake ciki da matar tashi ba Ina sane, sannan 'yan uwanshi nada gaskiya dole su zauna su nema ma d'an uwansu mafita In har da gaske suna sonshi, ban ga dalilin d'aukan zafi akan abinda ba shine ba" kallo kawai ummu ke bin Abba dashi kan ta juya ta haura a zuciye a ganinta 'ya'yanta Da mijinta sun tsani 'yar 'yar uwarta tunda har zasu iya cewa a yi mata kishiya su kuma suna zaune gidajensu su kad'ai, Toh kuwa zata ga uban da ya isa yi ma Abdulraheem aure tunda d'anta ne, tana da hakki a kanshi kaman yadda shi Abban ke dashi a kanshi, sannan se ta jaa wa su rahma shati akan shiga harkar da ba nasu ba, duk zasu gamu da ita.
🖤Gureenjo🖤