🥀NOOR IMAN🥀*Fatima Muhammad Gurin*
•Gureenjo6763 on Wattpad•*'Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)*I am really really sorry wallahi Ina busy ne kwana biyun nan kuka ji ni Shiru and har yanzu ban gama abubuwan dake gabana ba In kun samu gobe to In kuwa baku samu ba kuyi hakuri zuwa jibi, and please ina barar adu'o'inku gobe in Allah ya kaimu zan d'au hanya tafiyar 12hours A yafi juna*
*032*
Hamna ce tsaye rike da kwankwaso tana watso musu kallon rashin mutunci, cikin masifa tace "ka kyauta kenan yaya Abdul? Tunda haka ka za'ba shikenan gobe de kwananta ya kare tunda de bazawara ce" sake Iman yayi yana kallon fuskanta yace "kiyi wanka ki huta zan fita In na dawo zan ganku" tsintar kanta tayi da cewa "Toh Allah ya tsare ya kiyaye se ka dawo" wani kallo ya mata yana sake murmushi kan ya d'an kalli hamna da ta choje bakin kofa kaman d'akinta girgiza kai yayi kan yace "Ameen thanks dear" ya zagayeta ya wuce.
A kafatanin rayuwanshi be ta'ba wai don ze fita ko ze yi tafiya hamna ta mishi adu'a ba, gwara ma farkon Aurensu tana cewa take care amma banda yanzu, hannun hamna ya kama suka fice d'akinshi ya shiga da ita Don ya san d'akinta uwarta na ciki, suna shiga ya saketa ya juyo yana kallonta yace "Kubra! Kubra!! Kubra!! Sau nawa na kiraki?" Tace "uku" tana wani 'bata fuska yace "kin san Allah in baki shiga hankalinki dani ba, ba abinda ze hana In had'a dake da wacce ta kawoki duniya In koraku waje, karki natsu In kin ga dama" ya juya ya fice, what wai ita da uwarta ze had'a ya Kora akan wanchan shashashan yarinyar? A fili tace "duk abinda zaka min akan munafukar matarka zan saukeshi wallahi" ficewa tayi zuwa d'akinta ta fad'awa Ummanta duk abinda ya faru.
Bayan fitanshi ta cire gyalen jikinta da d'an kwali itafa a rayuwarta d'ankwali takura mata yakeyi, d'akin ta bi ko Ina ta karewa kallo tana mamaki, garin ta'be ta'benta ta ta'bo wani abu kaman button fari se gani tayi wani abu ya sauko daga sama ihu tayi tana matsawa, labule ne me kauri sossai cotton fari sol gwanin kyau, ciki ya raba da parlorn, dariya tayi tana kama baki, se taga parlorn ya fita da kyau babba sossai haka ta bud'e labulen ta shiga d'aki nan ma ya fita kato dashi, komawa tayi ta kara danna abun labulen ya koma ta kara dannawa ya sauko cikin nishad'i ta dingayi kaman wata yarinya seda ta gaji ta bari, toilet ta shiga ta dinga bin komai na ciki shima da ta'be ta'be.
Bayan ta gama ta fito ta fice babban parlorn saman, katuwar plasmar parlorn ta gani kunne bayan d'azu da suka shigo ba'a kunne ba, boom tv ke kai se wani rawa akeyi itakam ko kyaun gani be mata ba, hakan ya sa ta nufi gaban tv ta d'auki remote ta fara chanza tasha, daga bayanta taji ance "eyeee ashe su en kauye kuma talakawa an san tv tunda har an iya chanza channel" juyowa tayi se taga Hamna, idanunta ta kawar kan tace "Ina kwana Anty, wai naga abinda ake yi a wanchan tashar ne ba kyaun ga...." tsawa hamna ta daka mata "ke dallah rufewa mutane wannan kazamammen bakin ke har kin san abinda yake maras kyau da me kyau? Ni wuce ki 'bace min da gani kan raina ya 'baci In sa'ba miki kammani yanzun nan".
Umma da yanzu shigowarta ta kalli Iman sama da kasa kan tace "ke kin san ni?" Kai Iman ta girgiza umma tace "Toh bari In fad'amiki wacece ni, ni kanwar mahaifiyar Abdulraheem ne kinga kaman mahaifiya nake a gareshi kuma ni mahaifiyar Hamna ce kin fahimta?" Kai Iman ta d'aga umma ta ci gaba da cewa "so ina da hurumin saki abu kiyi a matsayina na uwar mijinki, ki wuce ki samamin abinda zanci yunwa nake ji".
Kitchen Iman ta nufa ba tare da tace komai ba, kitchen d'in fes dashi kaman ka lashe ba datti ko guda d'aya, komai na bukata akwaishi cikin kitchen d'in store ta bud'e shima akwai kayan abinci jibge se ma suyi shekara suna ci be kare ba, to sede bata san me zata dafa musun ba ganin safe ne yasa ta d'auko doya ta fere dube dube tayi tayi har ta samo inda kwai yake ta fasa, ta koma store inda taga an shanya albasa, garlic, turmeric da ginger d'anye ta d'ibo abinda zata bukata tazo ta had'a nan take tayi musu yam ball ta juye gabad'aya a cooler, tana fitowa da shi Zarah na shigowa.