🥀NOOR IMAN🥀*Fatima Muhammad Gurin*
*Gureenjoh6763 on wattpad**'Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)*Am so sorry for keeping you guys waiting🙏*
*048*
Layi ne a wurin na bala'i abin mamakin kuma matane karankatakap ba namiji ko d'aya a galabaice Mama ta dubi jawahir tace "ke dama haka ake cin uban wuya kan a samu ganinshi? Yanzu kina nufin se mun jira duka wannan layin kan mu ganshi?" Murmushi jawahir tayi tace "no inde da kud'ad'e wannan layin ba komai bane yanzu zamu iya ganinshi" umma tace "ko nawa ne dan Allah muyi mu hanzarta" Hamna dake ta nyamutsa fuska tana kallon wurin tace "yanzu anan mutum yake rayuwa? Tabb" ba wadda ya amsata se d'an waya da jawahir tayi nan da nan wani yazo ya bi dasu ta baya har bukkan boka.
Wani mummunan bakin kafiri mushriki ne zube a wurin kato irin giant d'innan shirgege da uban tumbi zaune idanunshi a rufe hannayenshi a bud'e kaman dae yana wani bautansu dae na shirka, duk zama sukayi cikin dakakkiyar muryanshi yace "me ke tafe daku?" Umma ce tayi gyaran murya tace "ni dae 'ya'yan 'yar uwata ne nake so duk su wulakanta su zama abin Allah sarki sbd komai da suka fini, mijinta kuma a nakastashi, tunda har ya kasa aurena ya aureta se 'yata gatanan tana auren d'aya daga cikin yaran ne Abdulraheem muna so ya zama a tafin hannunta se yadda ta juyashi kawai, sannan munafukar d'ayar matarshi a haukata ta haukan da za'a rasa warakanshi har abada"
Shiru yayi na mintuna akallah talatin har sun kosa duk se kara gyara zama suke kan ya fad'i wata kalma se ga kwarya a gabansu da wani jan abu ciki wani abin ya kuma fad'a se ga Iman nan kwance a jikin ummanta tana mata surutu ita umman murmushi kawai take sakewa, had'e rai Hamna tayi In da itace tayi magana ma wallahi da cewa zatayi a kasheta har lahira kawai dae tana tsoron wannan gabjejen mutum ne.
Yace "ita?" Umma tayi saurin cewa "kwarai kuwa boka" kai ya gyad'a ya sake fad'an wata kalma da wani yare da bama su sani ba se ga wani kulli gaban hamna fari da baki da wasu garin magani gasunan dai kore kore yellow yellow, yace "ba'kin shi zakiyi wanka dashi a tsakiyar d'akinta ki kirayi sunanta sau ukku a duk inda take zata haukace tabi duniya, Farin kuma ki sawa shi mijin naki a abinci ko abin sha an wuce wurin In dae har ya sha ko yaci komai kankartar abin".
Tace "Boka an gode" yace "ki godewa Aljannu" Ai ko ta gode musu ta hanyar cire makudan kud'i Don har d'akin Abdul ta shiga ta lalu'bo kud'ad'e dayake ta san ma'ajiyarshi ta zubewa wannan mushriki, kan umma ya koma ya fad'i wasu kalmomi se ga layu sun bayyana manya guda uku, yace "d'auka" ta d'auka ba ko tsoro yace "ki binne d'aya bayan d'akin ita 'yar uwartaki, d'aya bayan d'akin shi mijin nata d'ayan kuma shine ze kasance na yaran ki samu kan bola tsakiyar dare ki binne shikenan Aljannu zasu karasa aikin ki tabbatar ba wadda ya ganki in sun binnu kuma ki tabbatar ba wadda ze iya tonowa".
Jawahir ma ta nemi karin shiri akan alhazawanta suka sallameshi da makudan kud'i suka fito cikin jin daad'i gani suke kaman har sun aikata komai ya faru suna fantamawa cikin arziki, machine suka samu bayan sunyi tafiyan kafa sossai suka d'ane ya fito dasu suka hau motansu se Nigeria cikin zakuwa.
*******
"Wannan surutu ya isa hakannan ga abinci sauko kici kan wannan yaron ya dawo miki da magani kisha ki kwanta ki huta" tray d'in ta ajiye mata umma tace "wai sannu da kokari" murmushi kawai ummu tayi Iman tace "na gode ummu Allah ya saka da alkhairi" hancinta kawai ummu ta ja zatayi magana wayanta ya d'au kara dubawa tayi taga zahra murmushi tayi kan ta d'aga tace "Autana" kawai se zahra ta sa mata kuka ta manta when last taji ummun ta kirata da haka murmushi ummu tayi tace "ke kam bazaki girma ba ko? Yanzu me abun kukan?" Tace "ummuna nayi missing d'inki dan Allah yaushe zaki dawo? Ko In zo?" Ummu Tace "makarantan kuma wa ze je miki zamu dawo ne da daughter ta samu sauki" zahra tace "ummu zan iya yi mata magana yanzu?" A sanyaye ummu tace "ga ta".