BABI NA ARBA'IN DA SHIDDA

2.1K 158 15
                                    


🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
*Gureenjo6763 on wattpad*

*'Yar Mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

"My Meeroh this is for yhu, I love yhu so much, masoyiyar Stephen, demon da ohooo sorry fah🤣😅😅🤣🤣 Allah sarki Vampire diaries watcher ya zo please ya tayata kuka🤣😅😅😅*

*046*

"Akwai wani rana da babanta yayi tafiya bayan wata uku da aurenshi da mamansu kenan, amma gidanmu ba d'aya ba lokacin ya tafi da safe akan da yamma su hindatu zasu zo su tayani kwana, yayinda kamila zata je gidan mamansu, ban d'aura abinci ba se d'an makulashe da nayi taci se chan yamma likis na d'aura mana farar taliya da miya dama ina da miya na ajiye, bayan na dafa taliyar ta dafu na tsame ta to tafasashen ruwan ba tare da na tsaya ta huce ba na watsashi gabad'aya kuma da karfi magudanar ruwanmu da yake me girma sossai Ina watsawa ana kiran magrib so se na ajiye tukunyar na juya na rufe taliyar na d'au buta na zaga bayi seda na fito nayi noticing ashe duk abin nan da nakeyi ban rufe kaina ba a haka dae nayi alwala na shige d'akina ba wuta a d'akin sannan duhun dare be gama shigowa ba amma d'akin yayi wani irin duhu da ko tafin hannuna bana iya gani.

Lalu'ben inda zan samo torchi nake hannuna ya kai kan keken kwantar da yara da babanta ya saya don tanadin haihuwa a take na rike keken da kyau se jin kukan jinjiri nayi yana kuka da iyakar karfinshi kaman kaina ze rabe tsabar karan tayi yawa, kaman an had'a baki da en nepa suka kawo wuta cikin keken da kukan ke tashi na kalla, wani irin razanannen ihu na sake ina matsawa baya da sauri hannuna dafe da cikina, yaro ne a ciki namiji ne ko mace ban sani ba jikinshi daga kai har kafa kunan wuta ne yayi wani iri ba kyaun gani, idanunshi ba fari se bakin da ya rufe idanun gabad'aya bakinshi baki kirin har wani hucin bakin hayaki ke fita daga ciki, gashin kanshi rabi me tsawo baki har kan fuskanshi rabin kuma a aske tal, har Ina iya ganin karamin kahon dake 'bangare askakken.

Kuka na fara Ina neman kofan fita nan wutan d'akin ya fara d'aukewa da kawowa tuntu'be naci zan fad'i dafe kujera nayi ina dukawa, kuma d'ago kan da zanyi naga wata mace zaune akan plastic chair dake d'akin bayanta ta juyamin kanta kasa tana kuka gashinta a sake dayawa har kugunta faratunta zako zako dogaye bana ganin fuskanta da sauran jikinta abinda na iya gani kenan na sandara wani ihun kawai na fad'i sumammiya.

Ban san ya akayi ba nade ji kaman ana kiran sunana cikin mafarki amma da murya me amo da tsawa a firgice na tashi zaune, se naga wani rabi mutum rabi kwarangwal me girman jiki sossai da tsawo shima gashinshi kaman na matan nan me kuka a kan kujera faratunshi har sunfi nata halitta ne shi me muni da tsoratarwa har yau bana fatan sake ganin wanchan fuskan idanunshi wuta ke ci hancinshi na fitar da hayaki kaman ana kona karamin bola a take hayaki ya turnuke d'akin cikin tsawa yace "ke biladama me ya shigar dake gonata? Kin ko san waye ni?".

Cikin kuka nace "ban sani ba amma ko menene dan Allah kayi hakuri kuyi hakuri ban san me na muku ba" wani irin dariya me rugugi ya sake na minti biyu a take kuma ya had'e rai yace "tashiii!!!!!!" Jiki na rawa na mike na tsaya ya min nuni da gadon yaron "jinjirin d'ana me shekaru d'ari da biyar kika kone min da ruwan zafinki ba tare da kin mana magana mu matsa ko kin ambaci Allah ba da hakan ze hankarar damu!!! Kinga uwarshi nan Zulhaya'i tunda abin ya faru take kuka ko d'ago ido taki tayi!!! tun daga Birnin Sin aka tasoni sbd tashin hankali, Me kike tunanin zamu miki????? Me ya kamata ya zama hukuncinki? Don bazan ta'ba yafemiki ba". Cikin matsanancin tsawa yake maganan.

Zubewa nayi kasa Don bana fatan sake kallon fuskan wanchan yaron na aljani cikin kuka nace "ka taimakeni Don girman Allahn da ya hallicemu ka tausayawa d'an cikina ka yafemin dan Allah, kar ka min komai na tuba" kafewa yayi akan se fa na fad'amishi hukuncin da ze min cikin tsawa da barazana kawai yake magana, matarshi dake ta kuka ne ta d'ago ta kira sunanshi da ba zan iya cewa gashi ba, kallonta nayi da sauri na kawar da kai Ina kuka kawai ba tare da na tuna ambaton Allah ba me makon ruwan hawayen dake zuba a cikin idanunmu ita na jini takeyi zan iya cewa tafi mijin munin gabad'aya rayuwa na ranan da bazan ta'ba iya mantawa ba kenan Don naga tashin hankali iya tashin hankali.

NOOR IMANDonde viven las historias. Descúbrelo ahora