🥀NOOR IMAN🥀
*Fatima Muhammad Gurin*
•Gureenjo6763 on wattpad•
*'yar mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*04*
A Karo na biyu na kuma dunfaro class d'inshi 6mins past eight, dayake ban samu bacci cikin dare sossai ba saboda period pain da nayi fama da shi ban samu salama ba seda jinin yazo gabannin asuba kan nayi bacci.
Bani na farka ba sai karfe bakwai, kan nayi wanka na shirya na taho takwas da mintuna shidda, zuciyata na dukan tara tara saidai banjin zan iya komawa da baya sbd bana son samun matsala da course d'inshi sam gashi yanzu attendance na biyu ke shirin wuce ni.
Nannauyar ajiyar zuciya na sauke kan na tura kofan a hankali na sa kai, muryanshi dake tashi a hankali cikin sanyin da yake naturally ne ya doki dodon kunnena wadda har saida ya haifar min da faduwar gaba da na rasa dalili, ba tare da na kalli inda yake ba na nufi karasawa cikin ajin ko taku biyu ban yi ba na ji shi yana cewa.
"Hey you!!!! Get out of my class" 'Dago eyeballs dina nayi da niyyar bashi hakuri amma me? Bakina kwata kwata yaki bani had'in kai wurin motsashi har muryan ya fito, sarƙewa da idanunmu suka yi cikin na juna.
Wani irin disgusting look yake jifana dashi da ya sa ba shiri na juya na fice jikina na tsananta rawa, Ina jin tsakinshi cikin microphone kan ya ci gaba da bayanin cikin natsatsiyar muryarshi me tafiyar da hankalin me saurare.
Wuri na samu na buga tagumi cike da jimamin sake makara a class d'in bawan Allahn nan Dr. Abdulraheem kaman yadda zarah ta ambaci sunanshi, ina nan zaune har ya gama lecturing ya fito kaman jiya yau ma bakaken kananan kaya ne a jikinshi ko don ya san suna mishi kyau ne yasa yake sakawa? Oho, idanuna suna kanshi har ya bud'e wata Mercedes benz ya shige itama baka yaja da gudu kaman de jiya ya fice.
Ajiyar zuciya na sauke tare da kauda kaina daga hanyar da motar ta bi jin hannu a kafad'ana, kallon me hannun nayi murmushi na saki ganin zarah, fuskantan nan a turbune kaman zatayi kuka cikin dariya nace "lafiya autan ummu?" Kara turo baki tayi tace "You know what you did is not fair right? Me yasa kika zo late plz, wallahi dr. Abdul cewa yayi In baka da 75 percent attendance d'inshi you will not sit for his exams"
Matsa mata nayi ta zauna Ina me sauke ajiyar zuciya nace "In shaa Allahu bazan kara ba, yau ma da dalilin hakan" girgiza kai tayi tare da cewa "and in kin san kinyi late karki dinga shiga wallahi it hurts to see him humiliating you In public ba mutunci ne dashi ba" girgiza kai kawai nayi shiru ya d'an ratsa kan nace "tashi muje mosque mu d'an yi karatu tunda sai 2 muke da wani lectures din".
Mikewa tayi muka fara tafiya muna 'yar hira har muka isa masallaci, daga chan baya muka zauna muka baje handouts na chemistry ta fara koyamin duk abinda ban gane ba, ba mu muka motsa daga nan ba se karfe d'aya ta shiga ta yi sallah ta fito muka wuce zuwa cafeteria abinci muka ci wadda zarah ce ta biya kud'in duk da yadda nayi kokarin hanata.
Multipurpose muka nufa mukayi education 2-4 wadda sossai na fahimta kuma lectures din ya min daad'i har nake jin nan gaba karatun ze iya d'aukemin duk wata damuwana, "mu je ki yi sallah kan azo d'aukanki ko?" Na fad'a Ina kallon zarah dake chatting a wayanta kirar iphone 11pro ba tare da ta kalleni ba tace "yes sure, kin san kanon nan in yamma tayi holdup d'in bala'i ne da ita kan ka isa gida past five".
Murmushi kawai nayi ina mamakin surutun zarah Abu d'aya zaka tambayeta amma ta baka amsa sama da ashirin, a natse muke takawa musamman zarah 'yar gayu da tafiyarta ma kad'ai abun kallo ne, ga shiganta ba wai me nuna tsiraici ba a'a kawai de da ka kalleta zaka san daga gidan arziki ta fito hutu ne ko ta Ina a jikinta.
