🥀NOOR IMAN🥀*Fatima Muhammad Gurin*
•Gureenjo6763 On Wattpad•*'Yar Mutan Adamawa*
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)*Wannan page d'in naku ne masoya wannan littafin, Ina godiya kuma Ina jin daad'in comments d'inku, Allah ya bar kauna*
*031*
A hankali ya d'agota yana kallonta da tsantsar mamaki wai bacci tayi d'an girgizata yayi yaga fa tsakaninta da Allah bacci tayi a fili ya furta "ikon Allah" kan ya mike da ita a hannunshi yaje ya kwantar da ita se kuma ya tuna batayi sallahn azahar ba, fuskanta ya fara shafawa yana kiran sunanta a hankali, da kyar ta bud'e sexy eyes d'inta ta zuba mishi idanunshi ya kawar yace "tashi kiyi sallah kici abinci se kiyi baccin" yana kai nan ya mike ya fice, da kyar ta mike tayo alwala tazo tayi sallah kanta kaman ze tsage haka take jinshi.
Sallama taji anayi wadda hakan yasa ta mike ta fito parlorn ko d'an kwali bata d'aura ba, kuyangu ne rike da trays sunyi hud'u, kan dining dake gefen parlorn ta nuna musu suka ajiye, godiya ta musu kan suka fice ta juya da nufin komawa kenan taji an bud'e kofan dake tsakiya dakatawa tayi se taga shine, juyawa tayi da nufin komawa taji yace "Ina kuma zaki?" Tsayawa tayi be kara kula ta ba ya nufi dinning.
Abinci ya d'iba da d'an yawa Don ko breakfast be yi ba, ba tare da wani damuwa ba ya hau cin kayanshi, gajiya tayi da tsayuwar hakan ya sa ta nufi dinning d'in har ta ja kujera zata zauna yace "koma ki sa d'ankwali" baki ta tura ya d'an kalli lips d'in kan ya kalleta ya kau da kai, d'aki ta koma ta sanyo d'ankwalin ta zauna ta d'ibi abincin kad'an ta fara ci tana dafe kai.
Ya jima da gamawa yana zaune ne kawai yana aikin kallon abinda take yi cin abincin take kaman me cin magani tana 'bata fuska hannunta dafe da kai, mikewa yayi ya shiga d'akinshi chan ya fito da paracetamol ya ajiye mata a gefenta a hankali tace "thanks" kan ya juya yayi komawanshi, bayan ta gama cin abincin kuwa ta sha, a wurin ta bar komai to ko ta tattare bata san inda zata kai sauran abincin ba.
Kwanciya taje tayi bacci ya kuma surarta ba ita ta farka ba se la'asar wasai taji ta ba ciwon kan kuma, sallah tayi ta zauna danna waya, Instagram ta shiga tana ta kallon hutunan bukin mutane, wani wadda ta gani nasu da wasu account suka sa ne ya mata kyau sossai, wadda ya duka a gabanta hannunshi na kan takalminta yana cirewa ita kuma tana d'an lekan abinda yakeyi hoton yayi kyau sossai dukda sides d'in su ne ba full ba.
Saving tayi a wayanta ta koma settings ta d'aura shi a wallpaper d'inta yayi kyau sossai kuwa tunawa tayi da bata mishi godiyan wayan ba, to yanzu ita ta Ina zata mishi godiyan? Ta'be baki tayi ta ci gaba da danne dannenta gabad'aya ranar zarah bata shigo mata ba har dare, ba tare da tayi wanka ba ta chanza zuwa kayan bacci, tayi kwanciyarta bayan ta kira Mama taji jikin da sauki, maman ke fad'a mata gobe zasu wuce.
Da tunanuka fal ranta tayi bacci, wuraren 10 ya shigo duba ta ya samu kuwa ta jima da yin bacci, ya jima tsaye yana kallonta kan ya ja mata blanket ya kashe mata wuta ya fice, kiran sallahn farko ya farka kaman yadda ya saba yayi wanka yayi nafilfilinshi adu'anshi guda kar fushin Ummu yayi tasiri a kanshi yana rokon Allah ya sassauta mata jin haushin matarshi, adu'o'i sossai ya musu kan a kira sallah.
Mikewa yayi ya fito d'akinta ya fara lekawa ya ganta tsaye tana mika dayake tana farkawa ta kunna wuta, da sauri ya kawar da kai yana tsaki ya fice, toilet ta fad'a tayi alwala tazo tayi raka'atanil fajr tayi sallahn asuba kan ta d'auko wayanta qur'an app da tayi downloading jiya ta bud'e ta fara karantawa, seda gari yayi haske kan ta mike ta shiga wanka bayan ta fito ta shafa mai ta d'auko wata atampha A shape gown anyi ado da pattern d'in rigan red ta sanya.