*RUWAIDAH*
'''Love And Romantinc Story💋'''
*Salon Na Daban Ne.👌🏻*
~*Free Book*~
_*NA*_
_Real Ladingo Oummu Fareesa😘_
*Ƴar Mutan Niger🤙🏻*'''Wattpad@Rahamaummufareesa'''
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Chapter 22*
Cike da zallar tsananin tsoro da mamakin irin mugun naunauyan baccin da tayi, Ruwaida ta ƙara waro lumsassun fararan idanunta waje, ta waresu tar ta sake kallon agogon da yake manne ajikin bangon ɗakin. Hannayenta duka 2 ta ɗora saman kanta ta janye dogon gashinta da rabi ya zuɓo ya luluɓe mata fuska. Ta sake tsaida idanunta tar kan agogon, haka dai ya sake nuna mata ƙarfe goma saura minti 4 na safe. Acikin ranta tace“Oh my god! Ya Abbaye har ƙarfe goma na safe tayi, banje hospital na dubo lfyr ka ba? Acikin ranta tayi tambayar, tana ɗan jujjuya manyan idanunta tana turo ɗan ƙaramin bakinta gaba, aranta tana tambayar kanta ya akayi tayi bacci haka? Janye blanket ɗin da yake luluɓe ajikinta tayi ta zuro kyawawan baƙaƙen ƙafafunta waje, ta sauko a hankali tana yamutsa fuska, tasa takalmi tana mai jin haushin su islam da basu tashe ta ba, suka tafiyar su school, dan taso ta bisu su ajiyeta wajan Abbaye'n su sai su wuce. Bathroom ta shiga ta cika bath da ruwan ɗumi ta cire kayanta ta shiga cikin ruwan tayi luf abinta, lumshe shanyayyun idanunta tayi. Banda fuskar Acp ba abinda yake mata gizo, ɗan guntin smile tayi ta saka tafukan hannunta kan fuskarta ta rufe tana murmushi ita ɗaya, jinta take cikin wani irin shauki marar misaltuwa, hannunta ta tura cikin tsakiyar kanta, tana shafa gashinta, ta turo ɗan ƙaramin bakinta gaba, tana musmus da baki. Haka tana shirmanta, ta zage tayi wanka tass, ta ɗaura towel ta fito, ta goge jikinta ta shafa lotion me ƙamshi da laushi, ta gyara gashin kanta ta raba abiyu ta ɗaureshi da ribbon suka sauka gefen kafaɗunta, tayi kyau sosai gashinta sai baza ƙamshi yake. Ƙatuwar wardrobe ɗinsu ta buɗe, ta zaro wata ɗanyar shadda *VIP* milk colour ɗinkin doguwar riga, bayan ta saka pant da bra ta zura rigar, masha Allah cif ta mata ajikinta, tayi mata masifar kyau sosai, hips ɗinta haɗi bom_bom ɗinta, sun fito sosai ɗinki ya zauna ajikinta, manyan boobs ɗinta, da suke cike tsaya cur ƙosassu, sun cika rigar dam masha Allah.
Ruwaida ta ƙarema kanta kallo ta mirror taga yanda ƙirjinta ya matse tayi wani irin kyau, hannunta ta ɗora saman ƙirjin nata, ta ɗan buki ƙirjin nata, aranta tana faɗin“Ni bana son wannan breast sunmin girma.” ta ƙarashe mgnr zucin tana, turo ɗan ƙaramin bakinta gaba. Ɗaurin ɗan kwali ta murza, ta fesa turare, bata ko saka kwali ba, bare powder haka take bata kwaliya, mayafi ta ɗauko babbane milk ta yafa haka takalmi milk, bata ɗauki jaka ba, idan ka kalli Ruwaida se ka sake kallonta sbd kyawun da tayi, tamkar amaryar gwamna, haka ta fito. Wayarta ta ɗauka tana shafa cikinta sbd yunwar da take ji, cikin takunta me cike da nagarta ta nufi hanyar fita falo. Tana fitowa parlon ta fara rarraba idanunta neman Mummy, bata nan ba halamar motsin kowa.
Bedroom ɗin Mummy ta nufa, tana zuwa ta murɗa ƙofar taji a rufe, ta juyo ta nufi kitchen. Larai da Ta'sallah suna ɗan aikace-aikacen su. Ruwaida ta ɗaga masu hannu irin gaisuwa, ta tambayi Larai da hannu ina Mummy? Ta'sallah tace“ Larai nifa bana gane hirata.” Larai tace“Ruwaida kin tashi lfy ya jikin yayan naki? Ai Mummy sun tafi hospital, itada Maman Aneesa, kinyi breakfast ne?” Ruwaida ta girgiza kanta, tana narai² da idanunta, haushin kanta take ji, yanda tayi bacci dayawa haka. Juyawa tayi su Larai na mata mgn taƙi tsayawa ta nufi falo. Musaddiq ta gani atsaye yana waya, ta nufosa ta na mai saita nutsuwarta, tana isowa ta haɗe hannunta, alama ina kwana. Musaddiq ya tsinke ƙiran, yana mata ƙur da idanu yana murmushi yace“Lfy lau Ruwaida ƙanwar Acp, irin wannan kyau haka kamar matar gwamna? Ina Mummy?” Ruwaida ta nuna masa da hannu bata nan.
Murmushi yay Lyace“Ta tafi hospital ko? Kai Ruwaida ta ɗaga tana masa nuni da ya kaita, yace“Ok kin yi breakfast ne?” Kai ta girgiza. Yace“Ok muje muyi sai mutafi... Kafaɗa ta maƙale alamun baza tayi ba. Musaddiq yace“Ok shikenan bazaki ba.” ya faɗa yana kallon kyakyawar fuskarta, shi kam yarinyar yanayinta ya burgeshi. Ruwaida ta shagwaɓe fuska ta masa nuni zataci. Dariya yayi yace“Ok muje kan dining area ɗin.
Yana gaba tana binsa abaya. Da kansa ya haɗa mata tea ya zuba mata soyayen dankalin turawa da kwai, tako ci sosai tasha tea ɗin. Shima yaci sosai, suna kammalawa, suka bar parlon. A dab da part ɗinsu Bappa suka haɗu da Bappa da ummani Sani zai kaisu hospital.
Ruwaida ta nufi wajansu fuskarta ɗauke da murmushi, Musaddiq yana biye da ita. Ummani ta rungume, tana sakin murmushi. Bappah yace“Ah Ruwaida kina bacci Baban naku yazo ya koma baki bishi wajan uban gidan naki ba?” Ummani tace“ Aa yafa kwanta sai anjima zasu koma.” Musaddiq ya ƙaraso ya rungume Bappa yana murmushi yace“Nayi kewarku sosai fatan na sameku lfy?” Bappa yace“Uhmmm ango shigar dare akayi sannu da zuwa.” Ummani tace“Ina tsarabata?”Musaddiq
Yce“Tana nan, wai ina sani zai kaiku ne?” Bappa yace“asibiti mana. Musaddiq yace“Ok muje ai can zamu da Ruwaida! Sani yay zamansa se muje tare. Compound ɗin gidan suka nufa, Ruwaida na riƙe da hannun ummani. Rumfar ajiyar motoci suka nufa, wata baƙar mota ya cirema riga me numfashi sai sheƙi take wacce take mallakinsa, ya buɗema ummani da Bappa baya, suka shiga ya bauɗema Ruwaida gaba ta zauna, ya zagaya ya shiga mazaunin direba, ya murza ma motar key, ya nufi gate ɗin gidan.
Megadi ya buɗe masa babban gate ɗin bayan sun gaisa da sauran ma'aikatan ya sulala motar waje. Ruwaida sai rarraba idanu take, ta matsu ta isa wajan yayanta. Musaddiq anuntse yake dirving ɗinsa.
Rahma yau tin 7 tabar gida zuwa school, tama riga Zainab tafiya, taso ta samu taje wajan Acp ta gansa kafin take tafiya amman ina dole sai idan sun taso zata biya.
Su Abbah kuwa tin bayan sallar asubah suna zaune, gari na waye suke ta famar amsar jama'a ƴan ya me jiki, sai kusan zauwa su Mammy suka kora mazajan nasu suje suyi wanka su ɗan huta da rana sai su dawo su kuma su tafi, bayan sunyi brekafast suka tafi gida bayan sunyi wanka suka kowa ya kwanta agidansa ya huta.
Musaddiq suna shigowa hospital ɗin bayan an buɗe masa, gate ya shige da motar cikin asibitin. Yana gama parking ya fito ya buɗe masu ƙifa suka fito, ya rufe suka nufi cikin asibitin. Ruwaida takunta take me cike da nagarta, idan ka kalleta sai ka sake kallonta, sbd tsabar kyawun da tayi, tamkar amaryar gwamna. Acp ne kwance bacci yake, acikin nutsuwa yayi kyau sosai singleti ce ajinsa baƙa, sai wando 3quarter gashin ƙirjinsa luf akwance, sajan fuskarshi yayi luwai luf fayau fuskarshi. Su Mummy na gefe zaune saman ɗayan gadon suna hira Mom Aneesa, suka ji knocking. Mummy ta miƙe tana faɗin“Ai fa bazamu huta ba...” tana buɗe ƙofar tayi tozali da Musaddiq. Zatayi mgn ya rungumeta yana murmushi yace“I miss u my mummy.”Mummy ta bugi bayansa tace“Wai yaushe ka shigo garin ne? Ni sakeni to. Ta kalli ummani tana faɗin“Ummani kuda nace ku zauna jikin nasa da sauƙi fa. Bappa yace“A'a abarni naga jikana.”Mummy ta janye Mudaddiq ajikinta, ta kalli Ruwaida wacce ta raɓu da jikinta tana kallonta tana zumburo baki irin an ɓata mata rai. Mummy ta rungumeta, tace“Barka da safiya ƙanwar Abbaye.”Ruwaida gaishe da Mummy tayi ta nufi wajan Acp.
Su Mummy na biye da ita. Gaishe da mom Aneesa tayi, ta zauna bakin gadon tana kallon Acp ya mata kyau sosai. Mom Aneesa tace“Ƴar gidan Acp anzo jinya mu tafi gida ko?”Ruwaida tayi murmushi ta sadda kanta. Musaddiq ya iso ya zauna kusan Ruwaida yana gaishe da surukarsa. Tace“Musaddiq shigowar tsakiyar dare ko?” yace“Ai anan na kwana fa.” Bappa ya iso yana faɗin“Masha “Allah Safuwan jiki yayi sauƙi. Addu'a yay masa ya zauna yana riƙe da hannunsa. Mom Aneesa ta gaishesu, ummani tace“ Alhmdllh jiki fa yana sauƙi. Hira suke sosai Ruwaida dai ba mgn take ba, dan haka ta shiga whatsapp ta kunna data ta turama Acp imojin 😿 ta fara rubuta masa sako kamar haka.
_“Aslm Yayana ina kwana ya ƙarfin jikin? gani nazo kanata bacci,😥 to Allah yasa ba inda yake maka ciwo ina maka fatan akhairi nice ƙanwarka me son taga ka samu lfy akoda yaushe ina maka fatan nasara akan aikinka, da samun galaba akan maƙiyanka, insha Allahu wannan harbin shine na ƙarshe da za'a kuma maka har ka kammala aikinka na ɗan sanda.😰_ Ta tura masa ta shiga wajan game, tana game, Musaddiq sunata hirasu da iyayansa da kakaninsa.
Ƙarfe 12 su Abbah suka dawo lokacin da suka zo, ƴan gidansu Mummy masha Allah duk suna hospital ɗin, Taslim ma tazo. Suna waje dukansu a zaune sbd yawan mutanan Dr yace su zauna awaje, Ruwaida ce take wajan Acp kawai a zaune, ta rafka tagumi ta sashi gaba tana kallo, har yanzu bai farka ba, sbd alluran da Dr ya masa bayan yayi breakfast. Ɓangaran Rahma suna tashi daga makaranta, ƙarfe ɗaya da rabi, gida ta wuce. Agaggauce take shirinta ta sanya Abaya red mai fararan duwatsu ta yane kanta da mayafin abayar, tayi kyau sosai sai ƙamshi take bazawa, masha Allah tayi kyau duk da batayi kwaliya ba, wayarta ta ɗauka ta fito. Innah na zaune aƙofar ɗaki cikin rumfa Rahma ta fito tana faɗin“Toh innta zanje hospita, Zainab basu taso ba da ta rakani, pls innah bani rancan dubu ɗaya, wlh zan biyaki.” innah tana buɗe hanci tace“Rahma ina rabaki fa, sbd Allah kenan yanzu duk kuɗin da nake kashewa akan ki na gyaraki, kuma shikenan a yawo hanyar zuwa asibiti kyan zai zoge, shida ƴan uwansa su ƙare miki kallo wlh ko an kaiki bazasu ga wani sauyi ba, abd kin watsar da gyran a hanyar hospital, ni ba rancan da zan baki se kije aƙafa, wai yau kinyi ma kuwa duk abinda ya dace?” Rahma tace“Haba innah yanzu sbd Allah Safuwan na gadon asibiti se na nemi waje na zauna ai baiyi ba kema kin sani, shikenan tinda bazaki aramin ba bari zan ramta wajan maman Sabrin idan naje na roƙi Acp yaban sai nazo na bata har kyautar 1k zan ƙara mata asama...” Rahma ta faɗa kamar gaske dan tasan innah bazata bari akaiwa makota kyautar dubu ɗaya ba haka siddan.
Innah tace“ Jeki waye sakare da bansan halinki ba shine, kece zaki roƙi kuɗi, jeki bazan bayar ba, ki bata dubu goma dan Allah.”Rahma dariya tayi ta tafirta. Tana fita ta sami malam Ɗahiru rumfarsa ta almajirci, ta isa ta sunkuya ta gaishesa, tace“Baba zanje asibiti kuma banida ko sisi.”Malam ya zaro ƴar dubu ɗayar da take aljihunsa itama ɗazu aka bashi yana murmushi yace“ Uwa taki ta hanaki ko? Ayita haƙuri, ki gaidasu, ni tin bayan sallar asuba naje na duboshi, naga jikin masha Allah.”Rahma ta amsa tana godiya ta masa sallama ta nufi bakin titi.
YOU ARE READING
RUWAIDAH
RomanceLabari ne mai cike da soyayya ma rikitarwa da kuma makirci wanda duk yanda kaso ka hana abinda Allah ya tsara to fa babu tsumi babu dabara sai ya faru.