Chapter 6

372 20 2
                                    

*💖RUWAIDAH💖*

'''Love And Romantinc Story💋'''

*Salon Na Daban Ne.👌🏻*

~*Free Book*~

'''MALLAKIN'''
          👇🏻
'''Real Ladingo Oummu Fareesa😘'''
 
*Ƴar Mutan  Niger🤙🏻*

'''Wattpad@Rahamaummufareesa'''

*Sadakarwa Wa masoyen Ruwaida, na nesa da na kusa Billahi inaga tsantsar ƙauna, bakina bazai shiru ba dole na gode wa masoyen littafin Ruwaidat, Iove u tafka².*😻

~*DEDICATE TO*~
'''Real Ladingo fan's
Wollah Ruwan comments ɗinku kadai ya isa yasa, nai ta typung ba dare ba rana......ina godiya son so domin Allah🤝🏻😻'''

*Fadar Ummun Fareesa* karfa kuce nayi son kai, yaba kyauta tukuici🤷🏻‍♀️😜🤪


*Bismillahir Rahmanir Raheem*


*Chapter 6*

Dogon gashinta wanda yake baƙi sudik, daya rufe mata fuska ya janye gefe, ya zuba mata fitinannun idanunsa, masu kyawun gaske.
Tuzali yayi da black beauty face ɗinta.  Ruwaida kanta a sadde tana famar kuka, tai ƙasa da kanta sosai. Safuwan kansa ɗauke  sauri, azuciyarsa yana faɗin"A'uzubillahir minal shaiɗaninr rajim."
                  Bakome ya  riki ta Abbaye ba, se manya² brest ɗinta masu matuƙar  kyau da ɗaukan hankali da rabinsu suke baiya ne a waje ashe daman dugwan gashine ya rufesu.

    A riki ce yayi saurin sakinta ta duƙe ƙasa tana famar kuka.     Yayi maza ya cire wata jibgegiyar  rigar sanyin dake jikinsa, wacce ya ɗora kan shaddar jikinsa, tana baza wani irin fitinannan ƙamshinsa, ya rankwafo ya kamo hannunta, ba musu ta miƙe tsaye, tana ta famar kuka, saka mata rigar yay ajikinta, tare da ɓalle bottule ɗin rigar.    A hankali ya shiga tattara mata ɗogon gashinta, waje ɗaya,
Kukan Ruwaida ta rage saboda yanda taji wani irin sanyin daɗi haɗe da wani irin fitinannan ƙamshinsa ya baibayeta, ga yanda taji yana tattara mata gashinta anutse kamar susa yake mata........ƙara ida shige jikinsa tayi ta zagaye hannayenta a bayansa, tana sauke ajiyar zuciya, wata irin nutsuwa na shigar jikinta lungu da sakon jikinta.
Ɗaure mata  gashin yay a tsakiyar kanta, amman saida jelar ta sauka gadon bayanta,  tsaf ɗaurin yay mata kyau.
                              Haɓarta ya ɗago da hannayensa ya ƙura mata mayun idanunsa, cikin wata irin murya sassanya me daɗin gaske,yace.
                           "ke!! Ke! wacece ke?  daga ina kike? kuma meya fito dake a dai² wannan lokacin?"  ya jera mata wannan tambayoyin.
  Wani irin kuka ta sake saki ta fizge haɓarta   da ya riƙe da hannunsa taja baya tare da durƙushewa a wajan tana rusa kuka.
Tsawa ya daka mata yace"Ki amsamin." ɗagowa tayi jikinta yana karkarwa a tsurace ta shiga yi masa kwatance da hannunta.
  Hassala yayi irin ransa ya ɓacin nan saiya barta nan yaja tsaki ya lalubu bindugarsa ya fito da ita ya nufi mota, cikin takunsa na izza.
Yana isa ya buɗe motar yana shirin  shiga, ganin zai  shiga mota ya barta yasa ta miƙe tana rusar kuka da gudu ta nufi gunsa, kafin ya juyo ta rungumesa ta baya gam² ta zagaye hannunta, saman shafaffan cikinsa, tana kuka.
   A hassale ya fincikota ya maidota gabansa, suna fuskantar juna, cikin tsawa yace" Bana son damuwa..." ya faɗi yana ƙureta da idanu, ƙatuwar ajiya zuciya ya sauke, kafin yaci gaba da cewa.
                              " ina maki magana ki faɗamin ke wacece me kike nema a wannan daren?" Nan ma seda yaja burki sbd mgnr tame tsawo.
                  Kafin yace "Kin fito yawon dandine ko ya abun yake....?"  Ya faɗi yana tallafe gefen fuskarta.
                     Cikin rikita ta girgiza kai ta ƙwace fuskarta,  taja baya ta dinga waige²,cikin motarsa ta leƙa taga tsaleliyar phone ɗinsa, *Huawei* da sauri ta miƙa hannu ta ɗauketa,  da take da idanu ya bita cike da makaki yana riƙe da bindiga.
                        Akwai passward a jikinta ta miƙa masa tana kuka tana kwatanta masa ya buɗe mata passward ɗin dake jikin wayar, amsa yayi cike da mugun mamaki ya buɗe mata passward dake jikin wayar ya miƙa mata, a  nan take ta rubuta masa.
 
   *"Ni inaji amma bana magana wani ne ya ɗaukoni,yake neman ya ketamin haddi kuma aure na ya kusa shine na samu na gudu Allah ya haɗani dakai please kamar yadda Allah ya rufa maka asiri nima ka taimake ni ka ɗaukeni daga gurin nan   karya zo.*"

RUWAIDAHWhere stories live. Discover now