*RUWAIDAH*
'''Love And Romantinc Story💋'''
*Salon Na Daban Ne.👌🏻*
~*Free Book*~
_*NA*_
_Real Ladingo Oummu Fareesa😘_
*Ƴar Mutan Niger🤙🏻*'''Wattpad@Rahamaummufareesa'''
👹🤡💀😈☠️👺
*_🗣️🗣️🗣️Yekuwa Jama'ar Ruwaidah Kuna Ina???? To Kuce “Innahu min Sulaimanu, Wa'innahu Bismillahir Rahmanir_ Rahim.🤣* '''Wato Abinda Yake Faruwa Aljannun Ruwaida Sun Wuff da Wayata,👺Ina Cikin Typing Suka Bugeta Ta Faɗi, Dan Haka Ku Dage Da Karanta Mata Ayatul kursiyyu.😂 Kuyi Manage Wayar Yau Taƙiya😫.'''*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Chapter 28*
“Meyasa kamana wannan tambayar? Meke faruwane da Ruwaida ɗin?” ya tambaya yanajin faɗuwar gaba mai tsanani!! Mummy tace“Dr ka mana bayani mana..” Dr Junaid yace“Ok muje daga ciki.” Aruɗe sukabi bayansa. Acp kuwa nata ƙiran Mummy taƙi ɗagawa, haka kawai hankalinsa yayi mugun tashi, yaji gabansa na faɗuwa. Miƙewa yay arikice bai tsaya ƙiran ƴan gidan ba yaji ko lfy, kawai ya ɗauki makullan motarsa, ya fito. Cikin girmamawa suke gaishesa suna biye dashi har wajan mota security ɗinsa ya buɗe masa seat ɗin baya, yace“No!! Sauri nake.” haka kawai ya faɗa yana shiga mazaunin direba, yana faɗin“Kujira zan dawo.” ya rufe motar yana fixgarta ya nufi gate aguje. Buɗe masa gate akayi ya sulala motar waje aguje, nufi gidansu, yana sharara gudu ba na wasa ba.
Suna shiga Dr Junaid bayan sun zazzauna ne ya kalli Abbah yace“5
Tambayar da zan sake muku itace, Ruwaida nada miji ne?” Abbah yace“Wai meke faruwane kake mana irin tambayoyin nan? Batada shi faɗamana meke damunta?” Abbah ya ƙarashe mgnr cikin zaƙuwa da son jin meke damun Ruwaida. Dr yace“Bayan duk gwaje² da aka mata kusan kala 3 abun ɗaya yake nunawa tanada shigar ciki na tsawon sati 5...” Bakida ɗayansu suka haɗa baki wajan faɗin.
“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!! Mummy tace“Mun shiga uku ciki sati 5 kenan agidanmu tayi waye acikin yaran nan yaci mana mutunci ya torzatamu haka? Dr ka tabbatar cikine?” Dr Junaid yace“Wlh sau uku ina gwadawa sakammako ɗaya yake bani tanada shigar ciki tsawon sati 5, kuma ai alamu ma gashinan azahiri sun nuna Ruwaida nada ciki.” Hamza yace“Tashin hankali kenan.” Abbah ya koma ya zauna dabas, saman kujera ya dafe kansa, Allah kaɗai yasan me yake ji. Mummy tace“Yanzu ya jikin nata? Kuma nasan kaima kasan Ruwaida tinda ba wannan karon kaɗai aka kawota nan ba, ka dubata so Agsky har yanzu banji na gama gamsuwa ba, da wannan mgnr cikin muje ka kaimu wajanta.” Dr yace“ Wlh ciki gareta, sbd buguwar da tayi ansanya mata drip aciki harda alluran bacci tana buƙatar nutsuwa, tayi bacci.” Abbah ne yace“Ok muje ka kaimu wajanta zamu jira ta tashi, kekuma Bahijjah ki koma gida sbd baƙi har agama kome lfy sai ki dawo zamu zauna da ita.” Mummy tace“Wlh ko naje bazan nutsuba...” Abbah ya tari numfashinta“Dole zaki bayan an kammala sai ki dawo.” “Toh” Mummy ta iya faɗa Dr ya miƙe ya masu jagora har room ɗin da Ruwaida take kwance. Bacci take tana fitar da numfashi cikin nutsuwa an sanya mata drip. Dr ya ƙara dubata ya fice yana mamakin lamarin!! Tabbas yanada yaƙinin zaiyi wuya Acp ne yama yarinyar nan ciki ba ta hanyar aure ba, duba da irin kulawar da yake bata. Bakin gadon su Abbah suka iso suka zauna. Mummy ta kama hannunta tana matsar ƙwalla, ta shafi fuskarta tace“Tabbas idan ɗaya daga cikin yarana suka aikata haka gareki bazan taɓa yafe masu ba...”Abbah ya tari numfashinta ta hanyar faɗin.
“Karkiyi son kai kice kawai Abbaye bazan yafe maka ba, dan keda kanki kinsani Musaddiq baya gari lkcn, kice Abbanmu kaci amanar tarbiyyar da muka baka, haɗi da cin amanar yarinyar da bata san kowaba ayanzu aduniya sai kai, batada uwa da uban da suka fika sai kai, hakan ya baka damar wulaƙanta ƴar mutane... Hummm Bahijjah kije kiji da baƙin ki fa.”Hamza yace“Dan Allah mubi kome asannu zato zunubi ne fa, koda ya zamo gaskiya, duk da mgnr abin dubawace, Dr yace sati 5 itako tayi wata 3 atare daku bare ace, daman chan da abinta tazo...” ya tari numfashinsa. “Hamza watsatsan mutum ya fita daban ka kalli yarinyar nan dakyau wlh ba watsatsiya bace, kome take ina lure da ita gudun karta ɓatamin yara, wlh tsawon wata ɗaya nayi ina kiwonta bari na taƙaita maka kullun sai nabi dare na leƙata sbd tsaro ta window bazaka ga komeba sai ibadar Allah da take tsakiyar dare, dan farko ko rashin mgnrta ban yarda dashiba, har nazo na karanci yarinyar.. Akwai addini da nutsuwa. Tabbas Abbaye ka tozartamu.” ya ƙarashe mgnr yana dafe kasan. Mummy ta saki hannun Ruwaida ranta aɓace tace “To da yaushe hakan ta faru? Wato ranar da ya kaita office ɗinsa, har aljannu suka bigeta, tayi wajan sati uku ko bata jimaba tsautsayi ya faɗa masa.. Tabbas anyi hakan.” ta faɗi tana ficewa daga ɗakin, tana dialing ɗin number Acp.
Lkcn da Acp ya iso gate ɗin gidan nasu kenan, yana zuba uban horn ƙiran Mummy ya shigo wayarsa. Da sauri ya kalli screen ɗin wayar yaga sunan Mummy, da sauri ya ɗauki wayar ya ɗaga ƙiran yana faɗin “Mummy lfy inta ƙiranki baki ɗauka...?” Mummy muryata na rawa alamar kuka tace“Abbanmu mun gode maka da tozarcin da kamana, kazo mahaifinka na jiranka a hospital Ruwaida ma na jiranka ita da ɗan cikinta, ko nace ɗanka suna buƙatarka, suji me zakace sai kuma Rahma matar da,zaka aura sai ka amsa mata duk tambayoyin da zata maka nan gaba kaɗan yanzu kaxo hospital ishaq nason haɗa idanu da maci amanar ɗansa...” tana faɗin haka cikin kuka ta yanke ƙiran, ta kashe wayar baki ɗaya. Ta isa harabar asibitin Sani direba yana hangota ya taso daga gindin bishiyar da yake zaune, ya buɗe mata mota ta shiga, dan ta goge wayenta ta ɓoye damuwarta kar gudun mutane su fahimci halin da take ciki, Sani yaja motar suka bar hospital ɗin.
Tunda Mummy ta farama Acp mgn ta baibai yaji zuciyarsa na bugawa, da ƙarfi.. Jin Mummy na ambaton cikinsa ajikin Ruwaida yasa yaji kamar an buga masa guduma akansa, ya runtse idanunsa yana sauraron uwar tasa har ta gama bayani ta tsinke ƙiran cikin kuka nan ne abin yayi masifar ɗaga masa hankali. Da ƙarfin gaske cikin tashin hankali yace“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!! Ruwaida ce me ciki? Kuma cikina? Mummy sabodani kike kuka? Take jikinsa ya ɗauki wani irin mazari ya juyar da kan motar ya fizgeta amugun guje ya nufi hospital hankalinsa amugun tashe, driving kawai yake, amman sam baya haiyacinsa, danma namijin duniya ne da tuni ya saki hanya. Can gidansu Rahma kuwa masha Allah gidan ya cika da ƴan uwa da abokan arziƙi, anata aikin tarbar baƙi masu kawo kaya. Rahma ko sai baccinta take.
Taslim ta fito da akwatina na Abbaye gwada 12 cif wanda suke shaƙe da kaya, na kece raini, tsaya faɗar irin manyan lace dasu atamfa material Abaya kayan bacci ƙananun kaya, ɓangaran takalmai hijabbai, duk ɓata lkcne faɗarsu, dan akwatinan kawai abin kallone pink colour ne, me karatu ka kisima irin kayan da Acp yayima Rahma. Haka na Musaddiq shima haka akwati 12 shaƙe da kaya babu abinda bai saka ba. Bayan sun jera kome Taslim suka zauna suna santi mutane sunata shigowa ganin kaya anata sanya alkhairi, har ƴan gidansu Mummy suka iso, nan aka baje ana sabbatun kayan ƴan mazan Mummy sunyi ɓarin kuɗi. Mummy ce ta shigo da sallama ta ɓoye damuwarta. Taslim tace“Mummy ya me jikin?” Ta ƙaraso tana murmushin ƙarfin hali tace“Da sauƙi shiyasa nazo har mu gama da baƙi.” ta zauna suna gaisawa da jama'a, sunata sanya alkhairi. Ƙiran sallar azuhur da sukaji yasa suka miƙe, domin sallah, Mummy tace“Taslim kawai da anyi sallah arabu abiyu ku Taslim keda su Aunty hajiya Salma Khadija da sauranku ku tafi Nasarawo gidansu Rahma akai kayan.
“Kukuma su Zuwaira kuma ku goma ku shiga nan gidan namu ɗaya sai ku kai na Aneesa yayi ko?” ta tambayesu. Suka amsa da“Wallahi rabon yayi sosai. Salma tace“Mu ƴan Nasarawo ne inason innar Rahma ba ruwanta.” Murmushi Mummy tayi tace“Eh” ta nufi bedroom ɗinta tana riƙe da hannun ihsan ɗiyar Taslim.
Abbaye ikon Allah ya kawoshi hospital ɗin, lkcn ana ƙiran sallah, yana gama parking ya fito ya rufe motar ya nufi masallacin sbd yanada alwala ya nufi masallacin domin sallah, dosai ya ɓoye zallar tashin hankalin da yake ciki, jin Ruwaida nada ciki kuma wai iyayansa na iƙirarin cikinsa ne... Shi sam bama cewar cikinsa bane ya dameshi ya girgiza masa rayuwa da ɗaga masa hankali A'a abu 2 biyu yake masifar wujijjiga masa zuciya wanda sam ayanzu baisan me zaice ba ma, bai kuma san me zai iske aciki ba. Abbah ma jin ƙiran sallar yasa yace da Hamza“ Tinda bacci take muje muyi sallah.” Hamza ya amsa da “Toh” ya miƙe ya shiga toilet ɗin ɗakin ya ɗauro alwalla shima Abbah ya ɗauro, har xasu fita yaga Ruwaida ta ɗan motsa hannunta ya karkace mai drip. Da sauri ya ƙarasa ya gyara mata suka fice.
Ana daidaita sahu su Abbah suka shigo, karaf idanunsa suka sauka kan Abbaye, yay saurin ɗauke kansa suka shiga sahu aka tayar da sallah.
Ana salamacewa, Acp ya kai goshinsa ƙasa yana Sujada, yanama Allah ƙirari da sunayensa tsarkaka guda 99 akan ya warware masa wannan mugun ƙullin ya kuma sassauta zuciyar iyayansu, akansa su fahimceshi cikin sauƙi, dan kukan Mummy yafi kome firgitashi da ɗaga masa hankali. Abbah bai kalli sharan da Safwan yake ba, ya miƙe ya fice daga masallacin. Hamza ya zauna har Safuwan ya gama Addu'oinsa yana ɗagowa suka haɗa idanu da Hamza. Acp cikin dakiya yace“Kawuna meke faruwane don girman Allah...?” Hamza ya matso ya rufe masa baki yace“Tashi maza muje ciki sai muyi mgn amman inaso ka dubi girman Allah ka faɗamin gsky aduk tambayar da zan maka akan Ruwaidah.” Ya faɗa yana kama Acp ya miƙar dashi, da kansa ya miƙe idanunsa sun kaɗa sunyi jajur ya tsare kawun nasa dasu yana masa kallon tambaayoyi dayawa, amman sam Kawunsa bai basa fuska ba. Yana riƙe da hannunsa suka fito.daga masallacin asibitin suka nufi ciki. Abbah na zaune bakin gadon riƙe da hannun Ruwaida wacce take motsa hannun nata. Ƙaran buɗe ƙofar yasa Abbah ɗago da kansa, karaf suka haɗa idanu da Abbaye. Kallon da Abbah ya masa yasa ya ƙara tsorata da lamarin. Amman cikin dauriyasa da jarumtarsa ya janye hannunsa daga na Kawunsa ya fara takowa wajan Abbah yana mai ƙurama Ruwaida fitinannun idanunsa wanda sukayi mugun Ja, cike da mugun tausayinta da tausayin kansa ganin kallon da mahaifinsa ke watsa masa. Yana dab da isa bakin gadon, Abbah ya ɗaga masa hannunsa cikin tsawa yace“Karka kuskura ka iso nan..!!
YOU ARE READING
RUWAIDAH
RomanceLabari ne mai cike da soyayya ma rikitarwa da kuma makirci wanda duk yanda kaso ka hana abinda Allah ya tsara to fa babu tsumi babu dabara sai ya faru.