Chapter 14

360 21 4
                                    

*💖RUWAIDAH💖*

'''Love And Romantinc Story💋'''

*Salon Na Daban Ne.👌🏻*

~*Free Book*~

'''MALLAKIN'''
          👇🏻
'''Real Ladingo Oummu Fareesa😘'''
 
*Ƴar Mutan  Niger🤙🏻*

'''Wattpad@Rahamaummufareesa'''

*Bismillahir Rahmanir Raheem*



*Chapter 14*

Gyara mata kwanciyar tayi tana faɗin  "Yaranan lallai ma har yanzu babu wanda ya fito, bari na iskesu, Abban Taslim muje na haɗama kayan breakfast."
                 Ta faɗi tana kama hannunsa yana murmushi suka nufi kan dining area ɗin.        Ruwaida ta bude manyan idanunta tar, tana kallonsu Mummy abin gwanin burgewa.               Kyawawan idanunta ta lumshe takai hannunta mai zoben setin hancinta tana sunsunawa, ƙamshin Abbaye ya baibaye mata hanci, tanajin wani irin nishaɗi na ratsata, ta ƙamƙame zoben.          Abbaye jin maganar iyayan nashi, tasa ya ɗago da kansa yana lumshe tsumammun idanunsa, tamkar yana jin bacci haka suka rukiɗe suka canja launi, ya buɗesu tar yana kallon iyayan nasa.
                            Suna isowa wajansa suka saki hannun juna, Abbah yaja kujera ya zauna, dab dashi yace.       Abbaye yace"Good morning Abbah and Mummy!"  Ya faɗi yana ajiye cup ɗin hannunsa.    Abban ya rungumoshi yace.       "Morning my son, ya ka tashi bamu labarin me ya faru jiya da ƴar gidan taka?"   fuska ya yamutsa a hankali ya buɗe bakinsa ya shiga basu labarin abinda ya faru...... Mummy ta shiga haɗama Abbah abinda zaici, tana mai cike da mamakin wannan al'amari.     Tace"Ya Allah ka tseratar da baiwarka daga dukan sharrin abin ƙi!"  Abbaye ya amsa da "Ameen Mummy."  ya miƙe ya manna mata kiss a goshi, ya mannawa Abbah, yace"Zan fita." ya faɗi yana zura hannayensa acikin aljihu, ya zaro wayarsa yay dialing number Rahma.
                                  Ruwaida da take kwance idanunta lumshe, taji amon daddaɗar muryar Acp, yana mgn tamkar bayaso da sautin takunsa, da sauri ta juyo ta buɗe manya idanunta ta kalli gefen da takeji mgnrsa da takunsa.   Karaf idanunsu ya sarƙe cikin na juna, yana tafiya yana faɗi"I miss u too my dear."   Ruwaida ta ɗauke kanta daga kallonsa, ta miƙe da sauri ta nufi beɗroom ɗinsu, yanda jikinta ke motsawa ko ina tamkar tarwaɗa abin gwanin ban sha'awa.   Acp tin kallon farko da Ruwaida ta miƙe da ya mata, yay saurin ɗauke kansa yana taɓe baki ya buɗe ƙofar parlon ya fice.
Ruwaida kuwa da Fu'ad suka haɗu ya fito daga ƴar bedroom ɗinsa, yace"Lah anty kin dawo kin warkene?" Ruwaida ta lumshe manyan idanunta  tana matsar ƙwalla ta jinjina kai ta buɗe idanun nata ta kama hannunsa tana kallonsa.   Fu'ad yace"Anty kina ciwon kaine?"  kai ta girgiza masa, tai masa nuni da Abbaye ne yaci zalinta, kuma ya hanata wayarta. 
                      Fu'ad bai ganeba ya zare hannunsa anata, yace"Anty bari naje nayi breakfast na dawo zanfi gane kwatancan naki." kai ta jinjina masa, ya nufi parlo ita ta shiga bedroom taga wayar Islam a chaji, ta ɗauka, ta haye saman bed ɗin ta shiga tashinsu, suna noƙewa.   Sai ga Mummy tace" Ai ki barsu bari kugani, baccin lafiya har 11 saura?  " Kuda kuka raina mutane."   ta faɗi tana ciro wayar chaji, aikuwa suka diro daga saman gadon suna ihu suka nufi toilet a guje.   Ruwaida me zatayi inba dariya ba.   Mummy tace"Ai kya dara yaran sun raina mutane, kinyi breakfast kuwa?"  Ruwaida ta ɗaga kanta.   Mummy tace"Ok to yanzu ina yake miki ciwo?"  Ruwaida ta girgiza kanta, tai nuni da hannunta, babu.     
                              Widaad ta fito taba islam waje tayi wanka ta bata.      Mummy ta fice tana cewa "Ruwaida ki kwanta ki huta."  Ruwaida ta kalli Widaad tana murmushi.     Widaad tace"Ruwaida yaushe ne kuka zo?" Ruwaida tai mata nuni da hannunta jiya.    Widaad tace"Allah ya ƙaro Afuwa." Ruwaida kuwa kwanciya tayi, tana latsa wayar islam, ta saka number Acp dan ta haddaceta akanta.       Sai taga ma akwaita wajan message ta shiga, har ta fara rubuta masa ta goge ta ajiye mata wayarta ta shige cikin blanket ta ƙudundune, tana ta famar zumburo baki.
                 Islam tana fitowa ta shirya tace"Ruwaida ki tashi muje muyi breakfast."Ruwaida ta buɗe shanyayyun idanunta, ta mata nuni tayi.      Kai ta kaɗa ta fice.      Acp yana fita ma'aikatan gidan na ta kwasar gaisuwa, hannu kawai yake ɗaga masu, ya shiga wata zungureriyar motarsa mai numfashi, yay mata key, yabar gidan, a guje suna waya da Rahma kan yazo ya kaita zataga Ruwaida, ya sanar da ita an sakota, ta shirya idan ya gama abinda yake zai biyu ya ɗauketa suzo taganta, sosai tayi murna sukayi sallama, ya nufi police station ɗinsu.

RUWAIDAHWhere stories live. Discover now