*RUWAIDAH*
'''Love And Romantinc Story💋'''
*Salon Na Daban Ne.👌🏻*
~*Free Book*~
_*NA*_
_Real Ladingo Oummu Fareesa😘_
*Ƴar Mutan Niger🤙🏻*'''Wattpad@Rahamaummufareesa'''
_*DEDICATED TO*_
_Hajiya Jamila Falalu Mai Nasara.😘 Kisani ina ƙaunarki irin wacce babu algus acikinta, ina godiya da tsantsar ƙaunarki da kuma Alkhairinki agareni, Allah bar ƙauna har gaban abadan, Allah ya haɗamu har a aljannatul firdausi.🤝🏼😘_*~Alhamdulillah🤸🏼♀️ Tofa Masoyan Ruwaida Gani~* *~Da Gudu Na Danno Maku Da Ruwaidarku~. ⛹🏻♀️⛹🏻♀️⛹🏻♀️*
*~Wallahi Bakina Yayi Kaɗan Da Faɗin Irin Mugun Daɗi Da Kuma Nishaɗin Da Nakeji Aduk~* *~Lokacin Da Masoyan Ruwaida Kuka Ƙirani, Akan Nayi Haƙuri Naci Gaba Da Muku Typing Ɗin Ruwaida.... Wallahi Ina Jin Shauƙin Abun Duk Da Ba Kowa Nake Samun Damar Maku~ ~Reply Ba, Amman Hakan Yasa Na Ɗauki Damaran Cigaban Maku Da Ruwaida, Amman Idan Kuna Sambaɗo Min Ruwan~ Comments Da Kuma Sharhi, ~To~* *~Alqura'an Sai Kun Gaji Da ~Karatun Ruwaida, Idan Kuwa~ ~Bakwayi, Basss🤗👩🏻🦯~ ~Ƙwaranƙwatsi Ina Gefe Sai~ ~Nayi Kwanciyata, Dan Haka ~Karkuga Laifina.🤪🤪🤪~**Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Chapter 23*
Kusan Mummy Ruwauda ta zauna tana ƙoƙarin saitai nutsuwarta, tinda dai bata san me akayi ba take jin zafin zuciya, tana ji kamar ta shaƙe Rahma. Mummy ta janyota jikinta tana murmushi tace. Ah yayan naki ya tashi ne?” Ruwaida tayi murmushi tana ƙara lafewa jikin Mummy ta ɗaga kanta.
alamar “Eh” Mummy tace“Kin barsu su zanta ko?”Ruwaida tai murmushi ta jinjina kanta. Taslim tace“Masha Allah Ruwaida akwai hankali.”Musaddiq na gefe shida Nadeer suna murmushi, Abbah yace“Ai sai ku tashi ku koma gida har su Bappa.” Mummy murmushi tayi batayi mgn ba. Nazeefa ganin ƴan sanda nata zagaye duk suna ɗauke bindigogi yasa tasha jinin jikinta masu kula da rayuwar Acp ɗinta ne. Kallon Zinat tayi lokacin da take hango dandazon ƴan uwan Acp, yanayin kamarsu yasa ta gane family's ɗinsa ne, tace “Zinat! kalli wa incan mutanna ƴan uwan Safuwan ne, kalli tsabar kama.” ta faɗa tana ƙara sakama kanta nutsuwa. Zinat tace“Eh wlh tab ashe haka suke da zallar kyau?” ta tambayi Nazifa. Nazifa batace uffan ba, suka ƙarasa wajan nasu. Da sallama suka iso. Su Abbah suka amsa, Nazifa suka sunkuya har ƙasa cike da ladabi tace“Dady momy ina yininku ya mai jikin Allah ya ƙara masa afuwa.” Mummy suka amsa cike da fara'a, tace da Taslim“Ki shigar dasu mana. Taslim ta miƙe tace“Bismillarku. Se lkcn Ruwaida ta ɗago da kanta ta kalli su Nazifa, haka kawai taji basu mata ba, ta ɗauke kanta tana ƙara shiga jikin Mummy.
Can wajansu Acp bayan sun gama kallon soyayyar suna sakarwa juna murmushi, abinda Rahma bata taɓa zataba, murmushin Acp kai tsaye, tab yau shiyasa take jinta ta daban. Miƙewa yay ganin lkcn sallah har ya wuce, Rahma na tsokanarsa kamar ba me jinya ba, yayi kyau bai rameba. Murmushi yay mata me tsaɗa ya shiga toilet ya ɗauro alwola ya fito, ta shimfiɗa masa sallaya ya hau ya tayar da sallah.
Taslim ta turo ƙofar bakinta ɗauke da sallama, taga Safuwan na sallah. Rahma ta juyo tana amsawa, suka haɗa idanu da Nazifa. Rahma taji faɗuwar gaba sosai amman ta share ta nuna kamar bata taɓa sanin Nazeefa ba. Fuska ta saki tana faɗin. “Anty tare da baƙi kike sannu. Taslim ta amsa cikin fara tana faɗin“Ashe ya tashi, sallah ma yake? To ga baƙinsa, ku zauna har ya gama sallah.” Taslim ta faɗa tana juyawa. Rahma tace“Sannukun ku zauna mana.
Nazeefa sosai taji kunya haɗi da haushin Rahma amman ganin ta basar yasa itama ta saki fuska, suka isa wajanta suka ajiye ledojin suka zauna bakin gadon, suna gaishe da Rahma ta amsa acikin sakin fuska, tamkar abin bai dameta ba. Acp yana idar da sallah, bayan yayi addu'o'insa ya waigo fuska ba walwala ya kalli gefensu Nazeefa, suna haɗa ido ya kauda kansa, Nazeefa atake ta daburce ta miƙe tsaye ta fara takowa wajan Acp.
Rahma kallon ikon Allah take. Nazeefa nesa dashi ta rusuna tace“Safuwan ina yini ya ƙarfin jiki kuma? Allah ya kiyaye na gaba ya kareka daga sharrin maƙiya da mahassada.” Abbaye yaji daɗin Addu'arta agareshi sosai hakan yasa ya ɗan saki fuska yace“Ameen Ngd.” ya ƙarashe mgnr yana shafa cikinsa. Rahma na ganin haka ta miƙe cike da kissa, ta iso wajan Acp ta beƙa masa hannunta tace“My husband muje ka sakama cikin ka wani abu.” Safuwan ba musu ya miƙe shi ɗaya ba tare da ya kama hannunta ba, yana sakin mata lafiyayyan murmushi. Abakin gadon ya zauna, wayoyinsa sai ringing suke bai ɗauka ba, Rahma ta zuba masa haɗadɗan girkin ta matso da kujerata ta ɗauki spoon ta fara bashi abaki. Nazeefa taji daɗin yanda Acp ya amsa mata gaisuwa, amma wannan abinda Rahma ta masa yasa taji mugun haushi, amman sai ta basar, ta miƙe tsaye cikin farin cikin yanda yau Acp ya amsheta tace.“Mu zamu koma Zinat tashi muje, madam sai anjima.” Abbaye cikin amon daddaɗar muryashi bayan ya haɗiye abincin, yace“Ok Ngd.”Rahma cikin sakin fuska tace“Ok se anjinmanku muna godiya sosai fa. Nazeefa dakyat take cira ƙafafunta, suka fice.
Rahma ta kalli ledar da suka kawo ta ɗauke kanta. Acp ya kalli Rahma ya ɗaga mata gira ya kama hancinta yaja. Murmushi tayi ta tsiyaya masa drink me sanyi ta beƙa masa, tana masa hira.
Nazifa suna fitowa sukama su Mummy sallama, suka tafi, Ruwaida ko kallon arziki bata masu ba. Nazeefa driving take kamar zata tashi sama, Zinat tace“Kinga kibi asannu karki kashemu, waye ya hana ki nuna kishinki wajan da yake da mahimmanci?” Nazeefa tace“Bazaki ganeba ta nunamin ita ƴar barikice, duk da irin yanda talauci ya masu katutu, amman bai fitar da ita daga haiyacinta ba..... So kinga nida naje na sameta banida hanyar nuna mata kishina amman ki zuba ido ki gani zanci ubanta ne.!!! Zinat batace kome ba.
YOU ARE READING
RUWAIDAH
RomanceLabari ne mai cike da soyayya ma rikitarwa da kuma makirci wanda duk yanda kaso ka hana abinda Allah ya tsara to fa babu tsumi babu dabara sai ya faru.